Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home NAZARI

Wa’azin Kirista: Zamantakewar Kirista Na Nan A Cikin Littafi Mai Tsarki (Bible) II

by Tayo Adelaja
September 24, 2017
in NAZARI
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Tare Da Fasto Yohanna Y.D. Buru  0806 871 8181  yyohanna@gmail.com

Cikin Sunan Allah Ubangijimu, Kristoci na Mika Godiyarsu LEADERSHIP A YAU da dukan Ma’aikatansu.

Daga nan za mu ci gaba da maganarmu, wato “zamantakewa a cikin Addinin Krista.” Za mu ci gaba daga Romawa 13:10-11

  1. “Ku yi zaman dadin soyayya da junanku cikin kamnar ‘yan uwa; kuna gabatar da juna cikin ban-girma; 11. Cikin kwazo kada ku yi ragonci; kuna huruwa a cikin ruhu; kuna bauta ma Ubangiji.”

Kamar yadda muka yi bayani a aya ta 9 game da kauna ko kamna, ta haka ne za mu gane da bambancin kauna da soyayya. Kamar yadda muka fada a makon da ya gabata cewa kauna ita ce tushen Zamantakewan a cikin Addinin Krista. In babu kauna a zuciyar Krista ba zai iya kaunar wani ba. In kuma akwai kauna a zuciyar Krista, to ita ce tushen soyayya.

Marubucin Littafin Romawa yana kokarin ya bayana wa Kristoci da cewa, ba a zamantakewa in ba tare da kauna ba. In da kauna, to tabbataccen tushen soyayya ta kafu. Ta wurin kauna ne kadai akan sami dalilin soyayya.

Zamantakewar Krista ita ce ma’aunin halayyar cikakken Krista. Kauna a matsayi tushen Zamantakewa, ita soyayya kuma ita ce mahadin da ke bayyana ko akwai kauna ko babu.

A cikin aya 10, wanda ya ruwaito ya tabbatar mana da cewa a cikin zamantakewar Krista; ya zama wa Kristoci dole su yi zaman dadin soyayya da junansu cikin kamnar ‘yan-uwa. Wannan babbar magana ce mai muhimmanci ga kowanne Krista. Domin duk wanda ya fahimci maganar nan, to zai gane cewa umurni ne ba shawara ba. Shi Marubucin Littafin Romawa na biye da umurnin da Ubangiji Yesu Almasihu ya umurci Almajiransa, kamar yadda wannan umurnin na samuwa a Littafin Bishara ta hannun Yohanna kamar haka:

“Sabuwar doka ni ke ba ku, ku yi kamnar juna; kamar yadda ni na kamnarce ku, ku ma ku yi kamnar juna” (Yohanna 13:34).

Sirrin zamantakewa a cikin Addinin Krista na samuwa tawurin kauna ne. Tabbacin wannan maganar na samuwa a 1Korinthiyawa 13:4-8a. Matuka Yesu Almasihu ya umurci Almajiransa da Kiristoci da su kaunaci juna, to ba ta nan kadai gizo ke saka ba, domin Yesu Almasihu bai ce kaunar Kirista ta tsaya daga tsakani Kristoci ba, a’a.

Yesu ya kuma umurci Almajiransa da Kiristoci su kaunaci Magabtanku, a kuma yi wa mai tsananta maku addu’a. Amma ga abin da Yesu Almasihu ya umurci Almajiransa da Kiristoci su yi ga ire-iren mutane nan kamar haka:

“Kun ji aka fadi, Ka yi kamnar makwabcinka, ka ki magabcinka: amma ni ina ce maku, ku yi kamnar magabtanku, kuma wadanda su kan tsananta maku, ku yi masu addu’a” (Matta 5:43-44).

Kowa yana sane da cewa, kana iya kaunar makwabcinka da abokinka, amma ba da sauki ba ne a ce mutum ya kaunaci makiyinsa, ko kuma mai tsananta masa. Gaskiyar magana, yana da wuya wannan ta faru matuka muna cikin mutuntakarmu.

Amma domin Yesu Almasihu ya san muhimancin zamantakewa ga kowanne irin bil Adama, shi ya sa Yesu Almasihu ya umurci Almajiransa da Kiristoci su kaunaci juna, magabtansu da masu tsananta masu. Yesu Almasihu ya ci gaba da koyarwa akan muhimmanci zamantakewa da cewa:

“Gama idan kuna kamnar wadanda ke kamnarmu, wace lada ke gareku? Ko masu karbar haraji ba haka su ke yi ba? Idan kuwa kuna gaida ‘yan uwanku kadai, ina kun fi wadansu? Ko Al’umma ba haka suke yi bayani,” ( Matta 5:46-47). Maganar zamantakewa a cikin Littafin Mai tsarki na fadi fiye da yadda ake tunani. Wadannan ayoyin guda biyu sun kara fadada da kuma jaddada maganar zamantakewar Kirista da wadanda ba Kiristoci ba ne.

Matta 5:46-47, tana kara bayyana mana muhimmanci zamantakewa tsakanin Kirista da kowanne irin mutum, wato ko da makwabcinsa ne, ko makiyinsa ne ko da dan uwansa Kirista. Wato matuka Kirista ya bi dukan umurnin da Ubangiji Yesu Almasihu ya umurce shi ya yi game kyauta zamantakewa tsakanin Kiristoci da mabambantan addidinai, to duk duniya za ta samu cikakken zaman lafiya da fahimtar juna.

A nan umurnin da Ubangiji Yesu Almasihu ya umurci Almajiransa da Kiristoci su kaunaci makiyinsa ko kuma masu tsananta masu, ita ce kadai za ta karya logon makiyin Kristoci da kuma masu tsananta masu a ko’ina a duniya. Baicin haka, zamantakewar da ta ginu akan kauna ko kamna zai inganta kyakyawar mu’amula tsakanin Kirista da kowanne irin mutum ko mabambantan addidinai ako’ina a duniya.

Matta 546-47, na nuna mana cewa zamantakewan Kirista ko Kiristoci daban take. Zamantakewan da ta kafu akan kauna ko kamna ta kan kawo zaman dadin soyayya da juna cikin kamnar ‘yan uwa a mastsayin su Kiristoci da kuma kowanne irin mutum ko mabambantan addidinai. Romawa 12:10b na cewa: “…kuna gabatar da juna cikin bangirma.”

Wato bayanin shi ne matukar zamantakewar Kirista ta kafu ko tushenta daga cikin kamna ko kauna ne, to tabatace zamantakewan na kunshe da kauna tare da soyayyar juna da kuma kyakkyawar mu’amula da Zamantakewa da kowanne irin mutum ba tare da nuna bambancin addini ko kabilanci ko bangaranci ko nuna bambancin launin fata ko jinsi ba.

Kyakyawar zamantakewa cikin kaunar juna tare da soyayya shi ne ke kawo girmawar juna, addininmu daya ne ko ba daya ba. Ku tuna fa a cikin 1Korinthiyawa 13:4-8a za mu tarar a cikin Littafin Allah, wato Littafin Maitsarki Allah ya nuna mana da cewa kauna tana da yawan hakuri, nasiha, kishi, fahariya, kumbura, ba ta rashin hankali, bida ma kanta, jin cakuna, yin nukura, ba ta yin murna cikin rashin adalci…..

To in kamna ko kauna haka take a cikin koyarwar addinin Kirista, to babu wani mutum ko mutane da ke da kyakkyawar zamantakewa irinta Kirista. Kauna na cikin zuciyar Kirista sai soyayya na bayyana kaunar Kirista ga kowa ba sai dai Kirista dan uwansa ba kawai ba a’a.

In mun dauki lokaci mu yi nazari akan ayyukan kamna ko kauna ko mene ne kauna ko kamna take bisa ga 1Korinthiyawa 13:4-5, abubuwan da ke kunshe a chikin ayoyin nan biyu, to in akwai kauna ko kamna, to ba za a taba samun rashin zaman lafiya ba. Domin abubuwan da ke kawo zaman lafiya su ne ke tattare a cikin kauna, kuma da su ne za a sami zaman lafiya tare da kyakkyawar mu’amula da Zamantakewa tsakanin mabambantan addidinai.

Kafin mu karkare a yau, dole mu koma baya, domin tuna baya shi ne roko. Wadanan ayoyin da muke mora, wato Romawa 12:10-11 zan so mu dubi wadanan ayoyin kuma, amma a takaice. “Ku yi zaman dadin soyayya da junanku cikin kamnar yan uwa…” wato zama lafiya na samuwa ta wurin soyayya da juna ne. Zaman lafiya ba ta yiwuwa sai da kyakyawar zamantakewa, kuma zamantakewa na kafuwa akan kauna ko kamna kawai.

Ta wurin kauna ko kamna ne kowanne irin mutum kan iya girmawa dan uwansa, addinin mu daya ko ba daya ba ne. Zamantakewa na tunatar mana da mu’amula da ke tsakanin Kirista da kowanne irin mutum ko a mastsayin bil Adama ko kuwa ta addini. Ko Zamantakewan irin ta addini ne ko irin ta bil Adama ne ba za a ce babu zamantakewa ba. Ta wurin kyakkyawar zamantakewa da ke tsakaninmu da juna za mu iya girmama juna, soyayya da juna zai inganta, kyautatawar mu’amula, kaunar juna za ta karu da kuma mututa juna.

Ta wurin kyakkyawar zamantakewa za a rege ragonci ko zaman kashe wando, domin wasu masu ragonci za a iya karfafasu har su daina zaman ragonci. In akwai kyakkyawar zamantakewa da mu’amula tsakaninmu da juna za mu koya daga juna her mu ga karshen ragonci tsakaninmu.

Kyakkyawar zamantakewa da mu’amula da juna na kawo ci gaba ta wurin tattaunawa, musayan ra’ayoyi da juna, mu kuma koya wasu abubuwa daga juna. Zamantakewa na kara wa juna ilmi, na kawo ci gaban tattalin arziki. Zamantakewa na kawo zaman lafiya, na iya kawo kowanne irin albarkatu masu yawa.

Ku zauna cikin dadin soyayya da junanku cikin kamnar ’yan uwa, wato wannan wata babbar umurni ce a takaice ga kowanne Kirista zuwa ga ‘yan uwansu Kiristoci da kuma kowanne irin mutum ko makwabci ne ko makiyi ne.

In Allah ya kai mu mako mai zuwa , za mu ci gaba daga nan. Ku kasance cikin kaunar Allah da kuma Alherinsa daga yanzun har ab:ada. Amin.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kaucin Kaba Sha Nema: Rana Zafi Inuwa Kuna

Next Post

MADUBIN IMANI

RelatedPosts

Tarbiyyar ‘Ya Mace A Zamanance

Tarbiyyar ‘Ya Mace A Zamanance

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

Daga A'isha Muhammad A wanna Mukalar zan yi duba ne...

Lokaci

Muhimmiyar Tsaraba Ga Ma’auratan Jiya Da Na Yau

by Sulaiman Ibrahim
4 days ago
0

Daga Yusuf Kabir Aure yana daya daga cikin abin da...

Maleriya

Yaushe Za A Samar Da Riga-kafin Maleriya A Nijeriya?

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Najeeb Maigatari, A rubutun da ya gabata na dan...

Next Post

MADUBIN IMANI

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version