Duk da cewa burin dan wasa Messi na barin Barcelona a farkon wannan kakar bai cika ba amma ana ganin lokaci yayi da dan wasan zai fara tattaunawa da wasu daga cikin kungiyoyin da suke bibiyarsa.
Sai dai a kwanakin baya kungiyar kwallon kafa ta Manchester City dake Ingila tace ta hakura da zawarcin da take yiwa dan wasan bayan da kungiyar tayi lissafin irin kudin da zata kashe a lokacin yin cinikin.
A cikin watan Agustan daya gabata kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta so daukar dan wasa Lionel Messi daga kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, bayan da dan kwallon ya bukaci barin kungiyar sakamakon rashin jituwa da tsohon shugaban gudanarwar ta Barcelona.
Barcelona ta ci karo da cikas a kakar bara, bayan da ta kasa lashe kofi ko guda daya, bayan dukan kawo wuka da Bayern Munich ta yi mata a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League daci 8-2.
Kyaftin din tawagar na Argentina ya samu rashin jituwa da Josep Bartomeu – wanda ya ajiye aikin shugabantar Barcelona a cikin watan Oktoban daya gabata wanda hakan yasa dan wasan ya bukaci raba gari da kungiyar wadda ya fara bugawa wasa tun yana matashi.
Kwantiragin Messi zai kare a kungiyar Barcelona a karshen watan Yunin shekarar 2021, wanda hakan na nufi wata kungiyar za ta iya tattaunawa da shi da nufin daukar shi ranar 1 ga watan Janairun shekara mai zuwa.
Wannan dama ce idan Manchester City za ta yi amfani da ita wajen sake zawarcin kyaftin din Argentina sai dai wasu bayanai na cewa Manchester City ba za ta iya biyan Barcelona Yuro miliyan 50 ba, kudin da kungiyar za ta amince saboda halin matsi da cutar korona ta haddasa.
Ana ganin Manchester City za ta iya jira zuwa karshen kakar bana, lokacin da kwantiraginsa zai kare a Camp Nou kuma zai tafi ba tare da kungiyar ta Barcelona ta samu ko sisin kwabo ba sai dai kuma yawan albashin da yake dauka zai hana wannan ciniki.
Tuni dai Manchester City ta haura da zawarcin dan wasan saboda yana daukar yuro miliyan 100 wanda ba karamin kudi bane a halin yanzu da kungiyoyi suka talauce sakamakon annobar cutar Korona hakan yasa dole zasu hakura da daukar dan wasan.
Sai dai a cikin satin daya gabata dan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta PSG, Neymar, ya bayyana cewa zai iya barin kungiyar a kakar wasa mai zuwa idan har shugabannin kungiyar basu sayo musu dan wasa Messi ba inda ya ce ba zai sake sabon kwantiragi ba.
“Bani da burin da ya wuce sake buga wasa a kungiya daya da Messi saboda babban abokina ne kuma shima har yanzu yana da burin sake buga wasa dani saboda haka zanyi kokarin ganin ta kasance a kakar wasa mai zuwa” in ji Neymar
Ya ci gaba da cewa “Messi zai iya barin Barcelona a kakar wasa mai zuwa kuma kungiyar PSG tana daya daga cikin kungiyoyin da suke bibiyar dan wasan hakan ne ya bani kwarin guiwar cewa nan gaba zamu hadu a kungiya daya”
Tuni dai aka bayyana cewa shugaban gudanarwar kungiyar PSG ya fara shirye-shiryen tattaunawa da wakilan dan wasa Messi a cikin watan Janairu domin ganin ko zasu iya shawo kan dan wasan ya amince ya koma kasar Faransa da buga wasa.
Sai dai banda Manchester City, kungiyoyin Chelsea da Inter Milan da kungiyar Bayern Munchen duka sun nemi Messi sai dai a halin yanzu ana ganin PSG ce akan gaba wajen neman kaftin din na Barcelona da Argentina.
Shin Messi Zai Yi Abin Kirki A Faransa Ko Ingila?
Tuni aka fara nuna shakku akan ko tauraruwar dan wasan zata ci gaba da haskawa a daya daga cikin kasashen Ingila ko Faransa inda ake tunanin zai koma daya daga cikinsu amma kuma wasu suna ganin Messi gwarzon duniya ne saboda haka duk inda yaje zai nuna kansa.
A kowanne wasa a fadin duniya akwai matakin da ake zuwa dan wasa yayi ritaya daga buga wannan wasan ko kuma wasan yayi ritaya daga jikin dan wasan idan ya kasa ganewa cewa lokaci yayi da zai koma gefe ya huta domin ya bawa wasu dama.
Hakane ne yasa ‘yan wasa da dama suke ajiye takalmansu da zarar sunga kwallon ta fara tafiya daga kafarsu ko kuma da zarar sunga shekaru sun fara yi musu yawa kuma an fara samun matasa masu tasowa.
A kwanakin baya Messi ya bukaci barin Barcelona sakamakon rashin jituwar daya samu tsakaninsa da shugaban gudanarwar kungiyar Josep maria Bartemeu wanda a karshe ya ajiye mukamin nasa a farkon watan daya gabata.
Sai dai shugaban kula da gasar La Liga ta kasar Sipaniya, Jabier Tebas ya bayyana cewa a shirye yake idan har Messi ya bar kasar Spaniya da buga wasanninsa saboda manyan ‘yan wasa a baya sun buga gasar kuma sun tafi ba tare da sun samu nakasu ba
Messi ya bukaci izinin barin Barcelona a cikin watan Agustan daya gabata kungiyar da ya je tun yana da shekara 13 daga baya batun ya lafa, bayan da aka tsawaita yarjejeniyar zamansa a Camp Noun a tsawon shekara daya.
Shi dai Tebas na son Messi ya ci gaba da buga wasa a kasar Spaniya, amma ya ce ko babu Messi za’a ci gaba da gudanar da wasannin sannan shugaban na La Liga ya ce Neymar ya bar Spaniya a shekarar 2017 daga Barcelona zuwa Paris St Germain, kuma a shekarar 2018 Cristiano Ronaldo ya bar Real Madrid zuwa Juventus an kuma ci gaba da buga gasar.
Tebas ya yi nuni da cewar watakila Messi ya koma buga gasar Premier League a filin wasa na Etihad – koda yake wata majiya ta ce babu wani daga mahukuntan Manchester City da ya yi magana kan sayo Messi.
Sai dai salon buga wasa a Ingila ba irin na Ingila bane hakan yasa ake ganin dan wasan zai iya shan wahala amma kuma idan aka duba a baya za’a ga yadda ya buga wasa da kungiyoyin Firimiyar Ingila kuma ya samu nasara.