Connect with us

WASANNI

Wacce Kungiya Ce Za Ta Lashe Kofin Zakarun Turai Na Bana?

Published

on

A ranar Alhamis din data gabata hukumar kula da kwallon kafar nahiyar turai ta fitar da jadawalin yadda kungiyoyi zasu fafata a gasar cin kofin zakarun turai na nahiyar wanda hukumar take shiryawa duk shekara.
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce dai ta lashe gasar a kakar wasan data gabata inda ta doke kungiyar kwallon kafa ta Liberpool a wasan karshen da kungiyoyin suka buga a birnin Kieb dake kasar Ukraine.
Sai dai ba kamar shekarar data gabatab ba, domin a wannan kakar manyan kungiyoyin da basa samun damar zuwa gasar sunzo irinsu kungiyar kwallon kafa ta Inter Millan da Balencia da Lokomotib Moscow da PSB da kuma kungiyar kwallon kafa ta Club Brugge.
Shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta nahiyar turai, Aledandra Ceferin ya bayyana cewa gasar da za’a buga a wannan kakar za tafi ta kowacce shekara kayatarwa ganin yadda kungiyoyin da suka samu cancantar shiga gasar.
“Tabbas a wannan kakar za’a buga gasa mai ban mamaki kuma kungiyoyi za su fafata sannan kuma wasannin zasu kayatar yadda yakamata saboda naga manyan kungiyoyi masu tarihi a wannan gasar zasu buga a wannan shekarar” in ji shugaban hukumar ta turai.

Ga Yadda Jadawalin Kungiyoyin Ya Ke
Rukunin A
Atlético Madrid
Borussia Dortmund
Monaco
Club Brugge

Rukunin B:
Barcelona
Tottenham Hotspur
PSB Eindhoben
Internazionale Milano

Rukunin C:
Paris Saint-Germain,
Napoli
Liberpool
Crbena zbezda

Rukunin D:
Lokomotib Moskba
Porto
Schalke
Galatasaray

Rukunin E:
Bayern München
Benfica
Ajad
AEK Athens

Rukunin F:
Manchester City
Shakhtar Donetsk
Lyon
Hoffenheim

Rukunin G:
Real Madrid
Roma
CSKA Moskba
Biktoria Plzeň

Rukunin H:
Jubentus
Manchester United
Balencia
Young Boys

Sai Dai Ko Wacce Kungiya Ce Za Ta Samu Nasara A Wannan Kakar?
Real Madrid
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce dai take rike da kambun wannan shekarar bayan ta doke kungiyar Liberpool a wasan karshen da suka fafata a kasar Ukraine wasan da suka tashi Real Madrid tasamu nasara daci 3-1.
A kowacce shekara dai idan za’a fara buga gasar ana saka Real Madrid acikin kungiyoyin da za su iya lashe gasar biyo bayan tarihin da kungiyar take dashi a gasar kuma ga yawan kwararrun ‘yan wasan da suke dade suna buga gasar.
A cikin shekaru biyar Real Madrid ta lashe gasar sau hudu sannan kuma guda uku a jere hakan yasa kusan kawo yanzu babu wata kungiya data kai Real Madrid damar lashe gasar ganin yadda tayi a shekarun baya ga kuma tarihi da take dashi a gasar.
Sai dai damar lashe gasar da Real Madrid take dashi na lashe gasar ya ragu sosai sakamakon ta rabu da dan wasanta Cristiano Ronaldo wanda yakoma Jubentus a kwanakin baya kuma ya kasance wani jigo acikin nasarorin da kungiyar tasamu a baya.
Kungiyar dai kawo yanzu bata siyi wani babban dan wasa ba wanda zai maye mata gurbin Ronaldo kuma hakan wasu masana kwallon kafa suna ganin kamar matsala ce ga kungiyar domin Ronaldo yana daya daga cikin kashin bayan kungiyar da har tasamu wadancan nasarori a baya.
Sai dai bisa dukkanin alamu kungiyar zata iya buga gasar wannan shekarar ba tare da rashin Ronaldo yazama matsala ba ganin yadda kungiyar tasamu nasara a wasanni biyun data buga na laliga sannan kuma tana zuwa kwallaye a raga.
Har ila yau ‘yan wasa irinsu Luca Modric da Toni Kroos da Casemiro da Marcelo da kuma kyaftin din kungiyar Sergio Ramos har yanzu suna kungiyar ga kuma wanda aka dora ragamar kungiyar a kansa a yanzu wato Gareth Bale.
Hakan yana nufin kungiyar har yanzu itace akan gaba acikin kungiyoyin da zasu iya lashe gasar ta wannan shekarar duk da cewa babu dan wasa Ronaldo.

Barcelona
Kungiyar kwallon kafa ta shafe shekaru uku ana fitar da ita a zagayen kusa dana kusa dana karshe na gasar cin kofin zakarun turai wanda hakan yasa kungiyar a wannan kakar take ganin zatayi iya yinta don ganin tasamu nasarar lashe kofin.
Kungiyar kwallon kafa ta Roma ce dai ta shammaci Barcelona a kakar wasan data gabata inda ta doke ta da wani sakamako na ban mamaki kuma hakan yasa kungiyar ta fita daga gasar nan take.
Kungiyar Barcelona dai ta siyi ‘yan wasa a wannan kakar domin kara karfi a kokarin da takeyi na lashe kofin zakarun turai bayan da rabon ta da kofin tun a kakar wasa ta 2013 zuwa 2014 data doke Jubentus a wasan karshe.
Sai dai ba kamar Real Madrid ba, Barcelona har yanzu babban dan wasanta Messi yana kungiyar yana cigaba da buga wasa sannan kuma akwai ‘yan wasa irinsu Luis Suares da Coutinho da manyan ‘yan wasa irinsu Gerard Pikue a baya da kuma sabon dan wasa Arturo Bidal da kungiyar ta siya.
A kwankin baya kociyan kungiyar ya bayyana cewa baza su sake su sake irin rashin nasarar da sukayi ba a hannun Roma a gasar zakarun turai kuma suna nan suna gyara domin ganin sun lashe gasar.
Barcelona ce dai ta lashe gasar laligar data gabata inda wasa daya kawai tayi rashin nasara a kakar wasan data gabata sannan kuma sun lashe kofin kalubale na Copa Del Rey bayan sun doke kungiyar Sebilla daci biyar babu ko daya a wasan karshe.
A na ganin Barcelona a wannan kakar tana daya daga cikin kungiyoyin da zasu iya lashe gasar idan akayi la’akari da kwararrun ‘yan wasan da suke kungiyar yanzu kuma Real Madrid karfinta yaragu tun bayan tashin Ronaldo.

Bayern Munchen
Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ma dai a kowacce shekara ana sakata acikin kungiyoyin da ake saran za su iya lashe gasar duba da irin tarihin da kungiyar take dashi sannan kuma akwai manyan ‘yan wasa a kungiyar da zasu iya kai kungiyar kowanne mataki.
Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen ma kamar kowacce kungiya tanada manyan ‘yan wasa wadanda sunada kwarewa ta buga gasar cin kofin zakarun turai sannan kuma har ila yau kungiyar tana yawan zuwa gasar.
Duk da cewa kungiyar bata siyi wasu manyan ‘yan wasa ba domin tunkarar wannan kakar amma kuma itama bata saki ‘yan wasanta ba wadanda suke taimaka mata wajen lashe kofuna da kuma manyan wasanni sai dan wasa Arturo Bidal wanda yakoma Barcelona.
Munich dai tayi sabon mai koyarwa Kobac, dan kasar Crotia kuma yayi alkawarin ganin kungiyar ta lashe kofin zakarun turai da za’a fara a wannan shekarar duba da yadda kungiyar tayi gyara na daukar matasan ‘yan wasa kuma bata rabu da tsofaffin ‘yan wasanta ba.
Har yanzu ‘yan wasa irinsu Arjen Robben da Frank Ribery suna bugawa kungiyar wasa sannan kuma dan wasa Robert Lewandowski wanda yafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a kungiyar har yanzu yana nan ga kuma irinsu Muller da sauran ‘yan wasa irinsu Thiago Alcantara.
Ko a kakar wasan data gabata ma said a kungiyar taje wasan kusa dana karshe kafin tayi rashin nasara a hannun wadda ta lashe gasar wato Real Madrid.

PSG
Kungiyar kwallon kafa ta PSG ta dade tana son ganin ta lashe gasar zakarun turai tun bayan da mai kungiyar Almansur Alkhilafi ya siyi kungiyar, hakan yasa take kashe makudan kudade wajen siyan manyan ‘yan wasa a duniya sannan kuma tana kokarin lashe wasu daga cikin manyan wasanninta.
A shekarar data gabata kungiyar ta siyi dan wasa Neymar daga kungiyar kwallon kafa ta Barcelona akan kudi fam miliyan 200 sannan kuma ta dauki dan wasa Kylian Mbappe dan kasar Faransa wanda ya lashe kofin duniya daga kungiyar Monaco.
A kakar wasan data gabata kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ce tayi waje da ita a gasar ta zakarun turai inda ta doke ta gida da waje bayan anfito daga cikin rukuni sai dai a wannan kakar kungiyar tana ganin zata iya lashe gasar sakamakon ta sake sabon mai koyarwa, Thomas Tuchel, dan kasar Jamus, kuma tsohon kociayn kungiyar Borussia Dortmund.
’Yan wasa irinsu Cabani da Neymar da Mbappe sune ‘yan wasan da kungiyar take ji dasu kuma za su iya taimakawa kungiyar wajen ganin ta lashe gasar ta wannan shekarar duk da cewa akwai manyan kungiyoyi a gasar wadanda zasu iya doketa.
PSG bata taba lashe kofin zakarun turai ba sannan a kasar Faransa gaba daya kungiyar kwallon kafa ta Marseille ceta taba lashe gasar a shekara ta 1993 lokacin shahararren dan wasan Africa George Weah, dan kasar Liberia, wanda a yanzu shine shugaban kasar ta Liberia yana kungiyar.

Manchester City
Ganin mai koyarwa Pep Guardiola a kungiyar yasa kungiyar ta shiga cikin kungiyoyin da zasu iya lashe kofin kuma a kakar wasan data gabata kungiyar taje wasan kusa dana kusa dana karshe kafin Liberpool tayi waje da ita.
Shekaru biyu da suka gabata kungiyar taje wasan kusa dana karshe hakan yasa kungiyar yanzu ake ganin zata iya zuwa kowanne mataki a gasar sannan kuma ga manyan ‘yan wasa irinsu De Bruyne da Dabid Silba da kuma Sergio Aguiro.
A kakar wasan data gabata dai kungiyar ce ta lashe kofin firimiyar gasar data gabata bayan ta kafa tarihin lashe gasar da maki 100 sannan kuma a wannan kakar har yanzu batayi rashin nasara ba bayan an buga wasanni uku.
A zamansa a kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Guardiola ya lashe kofin zakarun turai sau biyu cikin shekaru hudu sai dai zamansa a kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen bai lashe gasar ba sai dai yaje wasan kusa dana karshe sau biyu.
Manyan ‘yan wasan da suke Manchester City a yanzu yasa an saka kungiyar acikin manyan kungiyoyin da zasu iya lashe gasar sai dai har yanzu kungiyar bata da kwarewa irinta Real Madrid da Barcelona da kuma Bayern Munchen.

Manchester United
Abu ne mai wahala kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta iya lashe gasar ta zakarun turai ganin halin da kungiyar ta shiga a yanzu na rashin nasara a wasanni biyu cikin wasanni uku na gasar firimiyar Ingila.
Kuma ana ganin cewa abune mai wahala kociyan kungiyar, Jose Mourinho ya dade a kungiyar idan akayi la’akari da yadda ake ta rade radin cewa zai iya barin kungiyar kowanne lokaci daga yanzu ganin yadda sakamako baya kyau.
Mourinho ya lashe kofin zakarun turai sau biyu a tarihi daya a kungiyar kwallon kafa ta FC Porto daya kuma a Inter Millan ta kasar Italiya sannan a shekararsa ta farko a Manchester United ya lashe kofin Europa.
Manchester United bata da karfin ragowar kungiyoyin da zasu iya lashe gasar duba da yadda babu manyan ‘yan wasa a kungiyar kamar na ragowar kungiyoyi sannan kuma akwai rashin jituwa tsakanin shugabannin kungiyar dashi kansa kociyan kungiyar.
A kakar wasan data gabata kungiyar kwallon kafa ta Sebilla ce tayi waje da Manchester United a gasar inda ta doke ta har gida daci 2-1 bayan anyi canjaras babu kungiyar data zura kwallo a kasar Sipaniya a wasan farko.
Hakan yasa ake ganin abune mai wahala Mourinho da ‘yan wasansa su iya abin azo agani a gasar wannan shekarar sai dai komai yana iya faruwa a kwallo amma kuma idan aka duba girman ‘yan wasa abune mai wahala.

Liberpool
A kakar wasan data gabata kungiyar kwallon kafa ta Liberpool taje wasan karshe na gasar inda tayi rashin nasara a hannun zakara wato Real Madrid a wasan karshen da aka buga a birnin Kieb na kasar Ukraine.
Tun bayan da kungiyar ta Liberpool ta dauki mai koyarwa Jurgen Klopp kungiyar tafra canjawa duk shekara kuma a yanzu kungiyar tanada matasan ‘yan wasa kwararru wadanda zasu kai kungiyar kowanne mataki.
Muhammad Salah shine wanda tauraruwarsa ta haska a shekarar data gabata inda ya zura kwallaye 43 cikin wasannin daya buga gaba daya kuma shine ya lashe kyautar dan wasan dayafi kowanne dan wasa zura kwallo a raga a gasar firimiya.
Akwai masu taimakawa kungiyar irinsu Sadio Mane dan kasar Senegal da kuma Robertp Firmino wadanda duk ‘yan wasan gaba ne sannan kuma akwai sabon dan wasan kungiyar Nerby Keita wanda ake ganin ba karamin karin karfi kungiyar tasamu ba zuwan dan wasan.
A kakar wasan data gabata kungiyar tasha wahala musamman rashin kwararren mai tsaron raga hakan yasa kungiyar ta siyo mai tsaron raga Allison Becker daga kungiyar kwallon kafa ta Roma dan kasar Brazil akan kudi fam miliyan 62.
Hakan yasa ake ganin kungiyar ta rage kashi hamsin na daga cikin matsalolin data fuskanta kuma kawo yanzu kungiyar tasamu nasara a wasanni uku data buga a gasar firimiya kuma tana matsayi na daya a yanzu haka.

Jubentus
Cristiano Ronaldo yana daya daga cikin dalilan da suka sanya ake ganin yanzu Jubentus zata iya lashe kofin na zakarun turai bayan daya koma kungiyar a watan daya gabata kuma daman kungiyar duk shekara tana yin kokari a gasar.
A cikin shekaru biyar Jubentus tazo wasan karshe sau biyu sai dai duk tayi rashin nasara a hannun Barcelona Real Madrid sannan kuma a kakar wasan data gabata taje wasan kusa dana kusa dana karshe.
Tuni dai aka bayyana cewa yanzu Jubentus tanada duk wata dama ta lashe kofin ganin yanzu Ronaldo yana kungiyar kuma akwai manyan ‘yan wasa a kungiyar da suka hada da Paolo Dybala da Mario Mandzukic da kuma irinsu Chiellini da sauran ‘yan wasan kungiyar.
Sai dai wannan shekarar babu Buffon, tsohon mai tsaron ragar kungiyar bayan da a kakar wasan data gabata yakawo karshen zamansa a kungiyar bayan ya shafe shekaru 17 inda a yanzu yana kungiyar kwallon kafa ta PSG ta kasar Faransa.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: