Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home WASANNI

Wacce Kungiya Messi Zai Koma?

by Muhammad
January 10, 2021
in WASANNI
4 min read
Kungiya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wasu bayanai da jaridun Brazil suka wallafa sun ce tauraro kuma kyaftin din Barcelona ta Spain Lionel Messi na shirin komawa PSG da taka leda sabanin Manchester City da kuma Inter Miami da ke zawarcinsa.

Messi mai shekaru 33 wanda ya mikawa Barcelona bukatar sauya sheka cikin watan Agustan da ya gabata, wani dan jaridan Brazil Thiago Asmar ya ce dan wasan ya fifita PSG kan sauran kungiyoyin biyu don sake haduwa da tsohon abokin wasansa Neymar Junior.

samndaads

Cikin watan Yuni mai zuwa ne kwantiragin Messi zai kare da Barcelona ya yinda tsohon kocinsa Pep Guardiola ke son hadewa da shi a Manchester City a bangare guda kuma Dabid Becham ke son kai shi Inter Miami a kasar Amurka, sai dai dan jarida Asmar ya ce Messi yayin wata hirarsa da Neymar ta shafin sada zmunta na Whatsapps wadda ya gani da idonsa, kyaftin din na Barcelona ya ce a shirye ya ke ya zabi PSG akan sauran kungiyoyin biyu.

Messi da Neymar a tsawon lokacin da suka shafe suna buga wasa karkashin Barcelona sun kafa gagarumin tarihi tare da kayarta da magoya baya ta yadda suka dage kofin lig har sau biyu gabanin Neymar ya sauya sheka zuwa PSG a shekarar 2017.

Yayin zantawa da manema labarai Neymar ya ce ya zama dole a wannan karon burinsa na sake zama kungiya daya da Messi ya cika a kakar wasa mai zuwa bayan yabar Barcelona a shekarar 2017.

Neymar ya sauya sheka daga Barcelona zuwa PSG kan kudi mafi tsada a duniyar kwallon kafa a wancan lokacin na Euro miliyan 222 sai dai kafin sauyin shekar Neymar da Messi da kuma Luis Suarez sun baiwa Barcelona gagarumar gudunmawa a nasarorin da suka samu na shekarun baya bayan nan, sakamakon kakkarfar hadin gwiwar masu zura kwallon da suka hada, baya ga nasibin iya sarrafa kwallon dalla-dalla.

Sai dai a kwanakin baya Messi, ya ce yana da burin wata rana ya buga wasa a kasar Amurka, amma ya ce bashi da tabbacin abin da zai faru nan gaba idan kwantiraginsa ya kare a watan Yunin shekara mai zuwa a Barcelona.

Messi dai zai iya fara ciniki da kungiyoyin da suke bibiyarsa na kasashen ketare a watan Janairu banda wadanda suke a kasar Sipaniya kamar yadda dokar hukumar kwallon kafa ta duniya ta tsara.

Ce-ce-ku-ce kan makomar Messi a nan gaba ya karu matuka tun bayan da Messi din ya nemi barin kungiyar a watan Agustan shekarar data wuce sai dai daga baya tsohon shugaban kungiyar ya hana dan wasan tafiya inda yace dole sai an biya Barcelona yuro miliyan 700 idan anaso a dauki shahararren dan wasan duniyar.

Barcelona, wadda ba ta ci kofi a kakar da ta gabata ba, ita ce ta hudu a La Liga bayan sun yi wasa mafi muni a farkon gasar cikin shekara 33 kuma a kwanakin baya Messi da kansa ya bayyana cewa dalilin da yasa baya kokari a wannan kakar ya samo asaline da rashin bashi dama yabar Barcelona.

Tun bayan da Messi ya shiga Barcelona lokacin yana da shekara 13 a duniya, dan wasan ya zama wanda ya fi zama zakara a tarihin kungiyar ta bangaren cin kwallaye, inda ya ci gasar La Liga 10, da kuma gasar cin kofin zakarun turai na Champions League sau hudu da kuma lambar yabo ta Ballon d’Or sau shida – wadda lambar yabo ce da ake bawa dan wasan kwallon kafa da ya fi shahara a duniya duk shekara.

“Wannan wani yanayi ne mai wuya ga Barcelona, amma wadanda ke cikin kungiyar sun san yana cikin mawuyacin hali, abubuwa sun lalace kuma yana da wahala Barcelona ta koma yadda take a baya,” a cewar Messi a kwanakin baya.

Tuni dai aka fara alakanta Messi da komawa wasu daga cikin manyan kungiyoyi a duniya ciki kuwa har da Manchester City ta Ingila wadda mai koyarwa Pep Guardiola yake koyarwa kuma Messi sunyi aiki da Guardiola a lokacin zamansu a Barcelona na tsawon sehkara hudu.

Itama kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint German tana daya daga cikin kungiyoyin da suke bibiyar dan wasan inda ko a kwanakin baya dan wasa Neymar na kungiyar sai da ya bayyana cewa zai iya barin PSG din idan basu sayo masa Messi ba a karshen kakar wasa ta bana.

Bugu da kari shugabannin kungiyar kwallon kafa ta PSG suna ganin idan suka dauki Messi ya koma kungiyar zasu samu damar ci gaba da rike Neymar sannan shima matashin dan wasa Mbappe zai iya zama idan har yaga Messi ya koma kungiyar.

A kwanakin baya ne Mbappe ya sanar da shugabannin kungiyar cewa zai iya barin kungiyar a karshen kakar wasa inda tuni kungiyoyin Jubentus da Real Madrid da Liberpool suka fara nuna sha’awarsu ta ganin sun dauki Mbappe, dan Faransa.

Tuni dai aka bayyana cewa shugaban gudanarwar kungiyar PSG ya fara shirye-shiryen tattaunawa da wakilan dan wasa Messi a cikin watan Janairu domin ganin ko zasu iya shawo kan dan wasan ya amince ya koma kasar Faransa da buga wasa.

SendShareTweetShare
Previous Post

Ozil Yana Dab Da Komawa Fenerbahce

Next Post

Messi Yafi Pele Komai A Duniya -Aguiro

RelatedPosts

Diego Costa

Wace Kungiya Ce  Zata Dauki Diego Costa

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Tun bayan da kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, ta...

Zaben Shugaban Barcelona

An Dage Babban Zaben Shugaban Barcelona

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta bayar da...

ozil

Rikita-Rikitar Da Ta Baibaye Dangantakar Ozil Da Arsenal

by Sulaiman Ibrahim
9 hours ago
0

Kusan yanzu zamu iya cewa ta faru ta kare domin...

Next Post
Aguiro

Messi Yafi Pele Komai A Duniya -Aguiro

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version