Connect with us

SHARHI

Wace Irin Hasara Amurka Ta Yi, Wadda A Hakika Ke Samun ‘Moriyar Rarar Kudi’?

Published

on

A yayin takaddamar cinikayya da take tsananta a tsakanin kasashen Sin da Amurka a rabin shekara da ta wuce, wani dalili da kasar Amuka ke zargi a kai shi ne, akwai babban gibin kudi a fannin gudanar da cinikayya a tsakaninta da Sin, don haka wai Amurka ta yi hasara. Wannan ne kuma daya daga cikin dalilan da suka sanya Amurka ta kara sanya haraji kan kayayyakin dake shigowa kasar daga wasu manyan abokan cinikayyarta, ciki har da Canada, Mexico, EU, Japan da dai sauransu. To, ko gaskiya ne Amurka ta yi hasara yayin cinikayya a tsakaninta da kasar Sin?

Wakilin ma’aikatar kasuwancin Sin mai kula da shawarwari kan cinikayya a tsakanin kasa da kasa, kuma mataimakin ministan kasuwancin kasar Fu Ziying ya bayyana a ranar Talata a nan birnin Beijing cewa, bambancin yawan cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka ya shafi yawan cinikin da suka gudanar, kuma ba ya nufin samun riba ko akasin haka. Ko kasar Amurka ta yi hasara ko a’a wajen gudanar da cinikayya da Sin, masana’antu da masu sayen kayayyaki na kasar sun fi kowa sanin abin da ke faruwa.

Jami’in ya nuna cewa, a yayin hadin gwiwa a tsakanin bangarorin biyu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, yawan ribar da masana’antun Amurka suka samu ya fi na kasar Sin sosai, ko da yake ana ganin kamar bangaren kasar Sin ya fi samun rarar kudin cinikayya, amma a hakika kasar Amurka ta fi samun “moriyar rarar kudi”.

Kasar Amurka ce ta fi samum “moriyar rarar kudi” wajen gudanar da cinikayya tare da Sin, wannan shi ne gaskiyar magana. A cikin shekaru kusan 40 da suka gabata, kasashen Sin da Amurka na hada kai sosai da dogaro da juna a fannin tattalin arziki. Yawan cinikayyar dake tsakanin kasashen biyu ya kai dalar Amurka biliyan 700, yawan kudin shiga da kamfanonin kasar Amurka suke samu a ko wace shekara wajen sayar da kayayyaki ya kai dalar Amurka biliyan 700, yawan riban da suka samu ya wuce dala biliyan 50.

Bayanai na nuna cewa, Sin da Amurka, sun sha bamban a fannin samar da kayayyaki a duniya, yayin da Amurka take a matsayi na gaba, Sin tana matsayin baya. Sai dai kamfanonin Sin suna samun kudi ne daga kere-kere, yayin da Amurka ke samun kudi masu yawa a fannonin tsara salon kayyayaki, da samar da sassan injuna, da kuma aikin saye da sayarwa. Kamar wayar salular Iphone ce, wadda ake tsara ta Amurka, a kuma kera da harhada ta a kasar Sin, sannan a sayar da ita a duk duniya. Hukumar Goldman Sachs ta ba da rahoton nazari na shekarar 2018, idan kamfanin Apple Inc. ya gudanar da ayyukan kerawa da harhadawa a kasar Amurka, to yawan kudin da zai kashe wajen fitar da kayayyakinsa zai karu da kashi 37 cikin dari.

A fannin sayen kayayyaki kuma, wasu kayayyakin cinikayya masu inganci kuma masu araha kirar kasar Sin sun shiga iyalan Amurka, wadanda suka baiwa masu sayen kayayyaki na Amurka hanyoyi da dama wajen zaben kayayyakin da suke so, kana da rage yawan kudin da suke kashewa a rayuwarsu ta yau da kullum, hakan ya taimaka wajen kara karfin Amurkawa, musamman ma wadanda ke rukuni na kasa da matsakaici a cikin al’umma wajen sayen kayayyaki. Bisa sakamakon nazarin da majalisar kula da harkokin cinikayya tsakanin Amurka da Sin wato USCBC a takaice ya yi, ta nuna cewa, a shekarar 2015, sakamakon cinikayyar dake tsakanin Sin da Amurka, ya sa ko wane iyalin kasar Amurka yana iya adana abin da bai gaza dala 850 ba.

A matsayinta na babbar kasuwa mai samun saurin ci gaba, hadin gwiwa a tsakanin kasashen Sin da Amurka a fannonin tattalin arziki da cinikayya ya samar da damar cinikayya mai tarin yawa ga masana’antun kasar Amurka. Bisa rahoton da USCBC ta bayar game da yadda jihohi daban daban na kasar Amurka ke fitar da kayayyaki zuwa kasar Sin a shekarar 2017, ya nuna cewa, a wannan shekara matsakaicin kayayyakin da ko wane manomi ke fitarwa zuwa kasar Sin ya wuce dala dubu goma. Kana bisa kididdigar da ma’aikatar cinikayyar kasar Sin ta fitar, ta nuna cewa, kamfanin kera motoci na General Motors (GM) na kasar Amurka yana da kamfanoni masu jarin hadin gwiwar da na Sin a kasar Sin, yawan motocin da suka kera ya kai kashi 40 cikin dari bisa wadanda ya kera a duk duniya.

Ko wadannan abubuwa suna iya shaida cewa, kamfanoni da masu sayayya na Amurka sun yi hasara?

Hakika, gudanar da cinikayya cikin ‘yanci na nufin cewa, wani yana son sayen wani abu, yayin da wani na daban ke son sayar wa. Kasar Amurka tana kara sayo kayayyaki daga kasar Sin, al’amarin da babu shakka zai haifar da gibin cinikayya dake tsakaninsu, amma ba wanda ya tilastawa wani ya saya ko ya sayar.

Karfin yin takara ta fannin cinikayya ya samo asali ne daga karfin yin takara ta fannin masana’antu, kuma a kan fitar da kayayyakin masana’antun dake da karfin yin takara zuwa kasashen waje. Kasar Amurka ta fi kasar Sin samun rarar kudin cinikayya a wasu sana’o’in da take da karfi, ciki har da kera motoci, da jiragen sama, da kayan noma, da sana’ar bada hidima da sauransu. Alal misali, a shekara ta 2017, darajar motocin da kasar Sin ta shigo da su daga Amurka ta kai dala biliyan 13.1, amma darajar motocin da kasar Sin ta fitar da su zuwa Amurka dala biliyan 1.4 ne kawai, wato darajar kudin motocin da kasar Sin ta shigo da su daga Amurka ya ninka kusan sau goma idan aka kwatanta da na motocin da Amurka ta shigo da su daga kasar Sin. Bisa takardar bayanin da gwamnatin kasar Sin ta fitar game da shaidu da matsayinta kan takaddamar cinikayya dake tsakaninta da kasar Amurka a ranar 24 ga wata, an ce, daga cikin wasu abubuwan da kasar Amurka ta fitar zuwa kasashen waje, ciki har da kashi 57 bisa dari na wake, da kashi 25 bisa dari na jiragen sama kirar Boeing, da kashi 20 bisa dari na motoci, da kashi 17 bisa dari na auduga, wadanda aka shigo da su cikin kasar ta Sin.

A fannin dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka, wani batun da ‘yan kasar Amurka ba su so su yi tsokaci a kai shi ne, rarar kudin cinikayya da yawanta ya zarce dala biliyan 54 da Amurka ta samu a kan kasar Sin ta fannin sana’ar bada hidima. Bisa alkaluman da ma’aikatar harkokin kasuwancin Amurka ta fitar, an ce, zuwa shekara ta 2016, adadin yawan Sinawan da suke zuwa yawon bude ido Amurka ya ci gaba da karuwa har tsawon shekaru 13, ciki har da akwai shekaru 12 wadanda yawan karuwar ya wuce kashi 10 bisa dari. Sa’annan bisa kididdigar da gwamnatin kasar Sin ta fitar, ta nuna cewa, kasar Amurka shi ne waje na farko da ya fi karbar daliban kasar Sin wadanda suke dalibta a can, kuma a shekara ta 2017, adadin yawan daliban kasar Sin da suka yi karatu a kasar Amurka ya kai kimanin dubu 420, wadanda suka bayar da gudummawar kudin shiga da yawansa ya kai kimanin dala biliyan 18 ga kasar ta Amurka. Bugu da kari, adadin yawan kudin da kasar Sin ta biya kasar Amurka a fannin ‘yancin mallakar fasaha ya karu daga dala biliyan 3.46 a shekarar 2011 zuwa dala biliyan 7.2 a shekara ta 2017, wanda ya ninka sau daya a cikin shekaru shida.

Hakikanin gaskiya, rashin samun daidaiton cinikayya dake tsakanin Sin da Amurka na da alaka da matakan da gwamnatin kasar Amurka ta dauka, wato Amurka ta kayyade fitar da wasu kayayyakinta zuwa kasar Sin. Bisa binciken da wasu hukumomin Amurka suka yi, ya nuna cewa, idan Amurka ta sassauto har ta kara fitar da kayayyakin amfanin jama’a da suka kunshi fasahohin zamani zuwa kasar Sin, yawan gibin cinikayyar dake tsakanin Amurka da Sin zai ragu da kashi 35 bisa dari.

Shaidu na nuna cewa, Sin da Amurka sun samu moriya kusan iri daya a yayin da suke gudanar da harkokin tattalin arziki da cinikayya tsakaninsu, har ma Amurka ta fi kasar Sin samun moriya, abun da ya nuna cewa, maganar da Amurka ke yi cewa wai ba ta samu moriya ba har ta yi hasara, sam ba shi da tushe balle makama. (Masu Fassarawa: Bilkisu Xin, Murtala Zhang, ma’aikatan sashin Hausa na CRI)

 

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: