Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home SIYASA

Wadanda Ke Zagaye Da Shugaba Buhari Ne Matsalarsa -Alhaji Mustafa

by Tayo Adelaja
September 18, 2017
in SIYASA
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Alhaji  Mustafa Usman, shi ne mataimakin shugaban kwamitin amintattu na kasa na Kungiyar Hada Kan Matasan  Arewa, a wannan tattaunawar da yayi da wakilinmu, YUSUF SHU’AIBU ya yi korafi kan irin tsarin Ministocin da ke wakiltar Arewa a wannan gwamnati ta Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Shekara biyu kenan da kafa wannan gwamnati, shin  ina aka kwana?

samndaads

Fisabilillahi akwai waje da daman gaske da wannan gwamnatin ta yi kokari, musamman ta bangaren tsaro, a kullum ina fadin cewa ko da makiyin Buhari in aka zo kan maganar tsaro, dole a yaba masa. Akwai ‘yan wuraren da aka samu nukusani, mutane na cikin wahala na yanayin rayuwar  da suka tsinci kansu a ciki, wanda wasu mutane  ‘yan kalilan suka sanya mu a ciki, shi yasa  a kodayaushe muke ta kiran ‘yan Nijeriya da su ci gaba da hakuri da addu’a domin hakuri ne zai janyo mana nasara, har abubuwa su dawo dai-dai.

Shin mene ne kake ganin ya jawo hakan?

Lokacin da Shugaba Buhari ya hau mulki ya ce duk  wanda aka kama shi da satar dukiyar kasa, a kama shi a daure shi?

Toh! Wa ka ga an tsare a wadanda aka kama din? Sai ka ji an ce an kama domin har yanzu, shari’a ake yi a kotu da wadanda aka kama wa ka ji an ce kudin nan sun sata? Kuma shekaru tafiya suke yi, ba dole ba ne a ce APC sai ta ci zabe a 2019 ba, wata gwamnatin na iya zuwa su ce sun rushe maganar gaba daya.

In na fahimce ka, dokar hawan kawara ake yi mata kenan?

Hawan kawara suke yi mata, ministan shari’a Malami ba wai abokina ba ne kawai, dan uwana ne, amma akwai masu kawo masa matsala bai sani ba, ya dauka masu ba shi shawara nagari ne, amma a zancen gaskiya su ne masu lalata masa aiki.

A yanzu haka akwai maganar  masu kwarmato nan gaba kadan za ka ji cewar an fara kama wasu da kudi, Buhari kuma saboda ba azzalumi ba ne da ya ji haka sai zuciyarsa ta buga hawan jininsa ya tashi a kara maida shi inda ya fito, wato  asibiti, saboda da ma ba sonsa suke yi ba, so suke su hallaka shi.

Wace shawara za ka bada a bangaren shari’a a kan hakan?

Ai ya danganta ne a kan shi kansa Malami, ka ga kamar tsofoffin ministocin shari’a irin  na da, za ka samu ba su taba gazawa ba a kan duk wata shari’ar da suka dauko. Misali, lokacin tsohon ministan shari’a Andoka, ai ka ga duk babu irin wannan kwamacalar, amma yanzu lokacin Malami, sai in Malami ya rusa wancan kwamitin ne kawai amma in ba haka ba, babu inda zai je.

Amma  a bangare daya kuma wani babban jami’in  sojan kasar nan ya zargi Gwamnan Jihar da laifin ruruta wutar fitinar, shin me za ka ce a kan hakan?

Mu a bangarenmu da abin ya zo mana sai da muka yi bincike a kan maganar da sojan ya yi, kuma  akwai rubuce-rubucen da muka yi. Ka ga inda wata kasa ce, za a yi wani abu a kan wannan lamarin,  amma mu nan sai a ce akwai kariya,  ni a tawa fahimtar da kuma  ra’ayina, akwai addini da kabilanci a cikin lamarin. Yanzu misali, maganar da T.Y Danjuma ya yi kwanan baya dangane da addini a nan kasar, in ka kawo maganar Taraba tun da dan Taraba ne, kenan akwai maganar addini da na kabilanci a ciki, ka duba irin kisan kiyashin da aka yi wa Fulani, sannan ka dubi yadda aka salwantar musu da dabbobi masu yawan gaske. Shin  me Gwamnatin Taraba ta yi a kan lamarin? Kuma ka dubi irin maganganun da suka yi wadanda za su iya tada rikici, kuma da ma tun farko mutane suna zargin su T.Y da irin su Zamani Lekwot da kawo rikicin addini a kasar nan, saboda haka ba abin mamaki ba ne idan  an ce rikicin Taraba na addini ne ko na kabilanci, ai Fulani aka kashe me ya sa ba su kashe wasu ba? Fulani kuma Musulmai ne gwamnan jihar  bai yi komai ba saboda ana zarginsa da hannu dumu-dumu  a cikin rikicin, tun da har babban jami’in soja  ya fito ya bayyana cewa gwamna ya sa aka yi wannan, kuma sojan nan ba Musulmi ba ne Kirista ne, shin me shugabannin Musulmi da sarakuna suke yi a kan lamarin? Ai cewa ma suka yi wai ai ba na addini ko  kabilanci ba ne.

Wace shawara za ka bada a kan hakan?

Idan an kawo wa mutum bayani sai ya yi kokari ya duba a koyaushe,  saboda mu nemi zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista, domin Allah Ya halicce mu kuma ya sanya mu a kasa daya. ‘yan siyasa ne ke kokarin hada mu fada sannan a karshe idan ka lura da kyau, za ka tarar babu ‘ya’yansu a cikin wadanda aka kashe, gaba daya  ‘ya’yan talakawa  ne lamarin ya shafa. Mu burinmu a kullum shi ne Allah ya kara  bai wa Shugaba Muhammadu Buhari lafiya domin ya cika wa al’ummar kasar nan  alkawuran da ya dauka. Amma maganar gaskiya ministocinmu na Arewa ba su tsinana wa ‘yan Arewa da Arewar komai, ka duba sauran ministocin da ke Kudancin kasar nan irin su Fashola da na Yammacin kasar nan irin su Rotimi  Amechi,  yadda suke yi wa yan kunansu aiki tukuru.

Amma mu namu, sai dai su fito su yi ta ihun Arewa, Arewa, amma ba wani abin cigaba da suka kawo yankin Arewar da ‘yan Arewa. Ina so ka fada min fisabilillahi, a duk cikin ministocinmu na  Arewa, wane ne ya  yi wa matasan Arewa wani abu, su wa ke mulki a kasar nan, me muka samu a wurinsu? Sai in zabe ya zo su rinka amfani da mu, ina mai tabbatar musu cewa daga yanzu  ba za mu sake yarda da irin  wannan ba. A baya mun tafka  babban kuskure,  mun  zabi mutane saboda Buhari, aka zo aka zabi wasu mutanen banza wadanda ba su san abin da suke yi ba. In Allah Ya kai mu shekara 2019 rai da lafiya, ba za a sake irin wannan ba. Ba wani sauran ‘Sak’, yanzu ba ga shi an yi Sak din amma an tsaya Cak ba! Shugaba  Buhari ne fa kadai na kirki a cikinsu, ka fada min, misali a cikin gwamnoni kamar El-rufai, yadda yasa aka haka wa mutane kwalbatoci sannan aka zo aka  dakatar,  ga shi ana damina ruwa ya zo yana shiga gidajen mutane.

An zo an haka min rami a gidana, ruwa yana shiga mini gida , ka zo ka yi shiru. A kullum ina fadin El-Rufai da na sani yana minista, ba shi ba ne wanda na sani a yau yana gwamna a Kaduna ba.  Domin lokacin da ya yi minista a Abuja ya yi aiki sosai, amma yanzu ka shigo Kaduna ka gani,  ko lokacin da muka je kamfen na sha fada don Buhari na da kirki, kar a zabi kowa, a tsaya a zadi wanda ya fi cancanta.

Amma yanzu mutane ma saboda rashin hankali so suke su sake jawo Buhari ba su ma maganar lafiyarsa. Kuma ni a nawa  tunanin da kuma ra’ayina, ya kamata Shugaban Kasa  Buhari ya kori duk ministocinmu na Arewa su je su huta, saboda babu abin da suka tsinana wa Arewar.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kungiyar NURTW Ta Kaddamar Da Sabbin Shugabanni A Galma

Next Post

Na Gamsu Da Kulawar Da Ganduje Ke Bai Wa Mata A Kano – Sa’adiya Isma’il

RelatedPosts

Har Yanzu Sakkwatawa Ba Su Fara Morar Dimukradiyya Karkashin Mulkin Tambuwal Ba – Umar Lili

Har Yanzu Sakkwatawa Ba Su Fara Morar Dimukradiyya Karkashin Mulkin Tambuwal Ba – Umar Lili

by Nasir Gwangwazo
4 months ago
0

Shugaban kungiyar matasan jihar Sokoto kuma dan gwagwarmayar ganin an...

Wane Ne Hon. Mal Samaila Suleiman (Dujiman Zazzau)?

Wane Ne Hon. Mal Samaila Suleiman (Dujiman Zazzau)?

by Daurawa Daurawa
7 months ago
0

Hon. Malam Sama'ila Sulaiman (Dujiman Zazzau) an haifeshi ranar 03/02/1981,...

Bala Abu Ga Sanata Mandiya: Babu Taimakon Da Ka Yi Wa ‘Yan Gudun Hijirar Faskari

Bala Abu Ga Sanata Mandiya: Babu Taimakon Da Ka Yi Wa ‘Yan Gudun Hijirar Faskari

by Daurawa Daurawa
7 months ago
0

Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC yankin Funtua a jihar Katsina, Alhaji...

Next Post

Na Gamsu Da Kulawar Da Ganduje Ke Bai Wa Mata A Kano – Sa’adiya Isma’il

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version