Wadanda Za Su Taimakawa Xavi A Barcelona

Ranar Talata Xavi Hernandez ya fara jan ragamar atisayen Barcelon a matakin sabon kocinta kuma Xavi tsohon dan wasan Barcelona ya amince da kunshin yarjejeniyar kammala kakar bana da kara guda biyu bayan nan. Ga jerin wadanda zai gabatar da aikin tare da su a Barcelona.

Babban koci: Xavi Hernandez. Mataimaki na daya: Òscar Hernández. Mataimaki na biyu: Sergio Alegre. Mai kula da kuzarin ‘yan wasa: Ibán Torres. Kocin masu tsaron raga: José Ramon De la Fuente.

Masu kula da nagarta da kwazo: Sergio Garcia da Toni Lobo da kuma Xavid Prats Xavi zai fara jan ragamar Baracelona wasan hamayya da za ta buga da Espanyol ranar 20 ga watan Nuwamba a gasar La Liga kuma Barcelona mai kwantan wasa tana ta tara a kan teburin gasar La Liga da maki 17, bayan kammala karawar mako na 13.

Barcelona ta gabatar da Xavi a gaban magoya bayanta da kuma ‘yan jarida a filin wasanta ranar Litinin, wanda ya maye gurbin Ronald Koeman da ta sallama, kuma tuni Xavi ya saka hannu kan yarjejeniyar da za ta kare a karshen kakar wasa ta 2024.

Dan kasar ta Sifaniya mai shekara 41 ya fara horar da Al Sadd tun daga shekara ta 2019, wanda ya amince ya karbi aikin jan ragamar Barcelona ranar Juma’a kuma a baya ya yi wa Barcelona wasanni 767 a kungiyar ya lashe kofi 25 a shekara 17 da ya yi sannan daga nan ya koma Al Sadd a matakin dan wasa a 2015, sannan ya zama kocinta

Wasannin mako na 14 da a kara a gasar La Liga:

Ranar Juuma’a 19 ga watan Nuwamba- Lebante da Athletic Bilbao

Ranar Asabar 20 ga wwatan Nuwamba- Celta Bigo da Billarreal

Sebilla da Deportibo Alabes- Atletico Madrid da Osasuna. FC Barcelona da Espanyol- Ranar Lahadi 21 ga watan Nuwamba. Getafe da Cadiz- Granada da Real Madrid Elche da Real Betis. Real Sociedad da Balencia- Ranar Litinin 22 ga watan Nuwamba Rayo Ballecano da Real Mallorca

 

Exit mobile version