Tambaya:
Don Allah Malam wata tambaya aka yi min, shi ne na ke son a taimaka min wajan ba da amsa, tambayar ita ce : me ya kamata mai yaron ciki ta kula da shi?
Amsa:
To malama akwai abubuwan da ya kamata mace ta kula da su, lokacin da take da ciki, ga wasu daga ciki:
1. Ki yi kokari, ki dinga cin halal, saboda lokacin da yaro yake ciki, na daga cikin lokutan da yaro yake ginuwa, don haka, idan kina cin haramun, yaron zai ginu da ita, sai Allah ya fara cirewa gabobinsa son alkhairi, tun yana yaro, domin duk jikin da ya ginu da haramun zai zama mai kasala wajan aikata abin da Allah yake so, kamar yadda malamai suka yi bayani.
2. Wasu malaman suna cewa : yawan saduwa yana karfafa yaro a ciki, saboda Annabi s.a.w ya kamanta ciki da shuka, kamar yadda ya zo a hadisin Abu dawud, mai lamba ta: 1847, kuma shuka tana kara karfi duk lokacin da aka bata ruwa.
3. Neman masa tsari daga shaidan, kamar yadda mahaifiyar nana Maryam ta nemarwa ‘yarta tsari, lokacin da ta haife ta.
4. Nisantar duk wani abu da zai cutar da shi, saboda musulunci ya yi umarni da kula da rai, don haka zai yi kyau a matsayinki na sabon aure, ki nemi shawarar magabata da kuma likitoci, saboda ki gujewa abin da zai cutar da yaronki.
5. Zuwa asibiti, lokaci-lokaci don tabbatar da lafiyar yaron.
Allah ne mafi Sani.
Fatawar Rabon Gado (105)
Tamabaya:
Assalamu alaikum Malam Ina da tambaya Allah ua karawa Malam daraja, mace ce ta mutu tabar ya mace da uwa da uba da kuma kanne da yayu uwa daya uba daya yaya za’a raba gadon ta?
Amsa:
Wa alaikum assalam. Za’a raba abin da ta bari kashi shida 6, a bawa ‘yarta kashi uku, mahaifiyarta kashi daya, mahaifinsa ya dau kashi biyu, kashi daya daga ciki sudusinsa ne, kashi na biyun kuma saboda shi ne asibi.
Allah ne mafi sani.
Nasiha A Cikin Mutane, Tozartawa Ne!
Tambaya:
Asslamu Alaikum. Don Allah Mallam mene ne hukuncin wanda idan ya ga anyi kuskure yake tozarta mutum a cikin jama’a?! Shugaba ne na makaranta yake jan jam’i rana daya dalibi yaja da aka idar da sallah sai aka fara yiwa dalibin tozarta a gaban dalibai maza da mata kan cewa bai kamata ba, ni ina ganin da an kira shi gefe an masa nasiha da karin haske ko a hadasu iya maza ayi musu zai fi. Meye hukuncin haka?
Amsa:
Wa’alaikum assalam, Yi wa mutum nasiha a cikin mutane bai dace ba, kuma hanya ce da za ta hana shi amsar nasihar, in ba wanda aka yiwa nasihar yana da tsananin ikhlasi ba, Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda ya suturta Musulmi Allah zai suturta shi”. Kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 2074.
Allah ne mafi sani.
Shin Musulmi Zai Iya Aiki A Coci, Don Samun Na Kalaci ?
Tambaya:
Assalam/ ya malam ina da tambaya; misali ni brikilane kuma na kasance musulmine sai aka ban contrc din gini na church, ogana ya ce mu za muyi; yaya matsayin mu yake idan munyi wannan aikin?
Amsa:
To dan’uwa malamai sun yi bayani cewa : bai halatta musulmi ya zama Birkila a Coci ba, saboda hakan yana daga cikin taimakawa aikata zunubi, kuma zai iya jawowa mutum ya ga yadda ake shirka da Allah, wanda hakan zai iya masa tasiri.,
Allah madaukaki yana cewa “ kada ku yi taimakekeniya wajan aikata sabo”, “ suratul Al-maidah aya ta : 2, sannan duk abin da yake kaiwa zuwa barna, to zai zama haramun ko makaruhi.
Don neman kari bayani duba : Al’umm ta Shafi’i 4/213.
Allah ne mafi sani.
Zan Iya Sallar Nafila A Lokacin Tafiya?
Tambaya:
Assalamu alaikum, malam tambaya ta ita ce yaya hukuncin yin nafila yayin da mutum a halin tafiya wato yanayin kasaru, naji wasu malaman suna cewa ba’ayin nafila a yanayin kasaru don Allah malam ina bukatar amsa da gaggawa, nagode.
Amsa:
To dan’uwa abin da aka rawaito idan Annabi (SAW) ya yi tafiya, yana barin nafiloli, in ba wutiri da raka’atanil fijr ba, kamar yadda Ibnul-kayyim ya ambata a littafinsa na Zadul-ma’ad 1\456.
Wasu malaman suna ganin nafilolin da suke da alaka da sallolin farilla su ake bari, amma wadanda ba su da alaka da sallolin farilla kamar tsayuwar dare an iya yinta, an samu halaccin hakan daga Imamu Ahmad. Zadul-ma’ad 1\457.
Allah ne mafi sani.
Fatawar Rabon Gado (106)
Tambaya:
Assalamu alaikum: Da fatan an yini lafiya, Ina da tambaya da nakeso a taimaka mini da answer
Tambayar akan rabon gado ne
Mace ce ta mutu ta bar kudi 109,000 naira cash .
: 1 – Bata da Uwa babu Uba ,
2 – babu miji
3 -bata taba haihuwa ba ,
4 – kuma bata da dan uwa ko ‘yar uwa wanda suke uwa daya uba daya .
: 5 – Bata da kakanni both side
To yaya za a raba gadan wannan kudin ? Dangi da ta bari kawai ‘yan uwa ne uwa daya da kuma ‘yan uba daya .Da fatan za a amsa min
Amsa:
Wa alaikum assalam, za’a raba abin da ta bari gida uku, kashi daya a bawa ‘yan’uwan da suke uwa daya, in maza da mata ne su raba daidai babu bambanci tsakanin namiji da mace, ragowar kashi biyun sai a bawa ‘yan uba su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.
Allah ne mafi Sani
Ina So Na Yi Tsayuwar Dare, Ammma Na Gaza, Me Ya Kamata Na Yi?
Tambaya:
Assalamu Alaikum. Malam ina sha’awar yin tsayuwar dare saboda dimbin falalar da ta kunsa, saidai a lokuta da yawa, na kan so na tashi, amma sai na kasa, ko malam zai taimaka min da shawarwari akan abin da zai taimake ni wajan yin wannan babban aikin, Allah ya karawa malam daukaka, amin.
Amsa:
Wa’alaikum assalam, To dan’uwa ina fatan Allah ya datar da mu gaba daya zuwa wannan ibada mai girma, akwai abubuwa da malamai suka yi bayanin cewa, suna taimakawa wajan samun damar tsayuwar dare, ga wasu daga ciki :
1. Baccin rana: Hasanul Basary ya wuce wasu mutane a kasuwa da rana, sai ya ce wadannan ba za su yi bacci ba, sai aka ce masa E, sai ya ce ina ganin darensu ba zai yi kyau ba”.
2. Yin bacci da wuri, Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya karhanta bacci kafin sallar isha da kuma yin hira bayanta, kamar yadda ya zo a hadisin Muslim mai lamba ta: 647, kuma dalilin da ya sa ya karhanta hin hira bayanta saboda hakan zai iya hana mutum tsayuwar dare.
3. Aikata ladubban bacci yayin kwanciya, ta yadda zai karanta abin da ya zo a cikin sunna na ladubban bacci.
4. Umartar wani ya tashe shi kamar matarsa ko wanda suke tare.
5. Rashin cika ciki da abinci.
6. Nisantar yin aiki mai wahala da rana.
7. Nisantar abin da zai kawo maka fargaba a cikin zuciya, ta hanyar rage burirrika da tunanin abin da ya wuce
8. Nisantar zunubai, Fudhail bn Iyadh yana cewa: “idan ka ga ba ka iya tsayuwar dare, to ka tabbatar zunubai ne suka dabaibaye ka.
Allah ne mafi Sani.
Fatawar Rabon Gabo (107)
Tambaya
Assalamu’alaikum. Mal mutum ne ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya biyu maza da kaka (mahaifiyar Uwa) da ‘yan Uwa shakikai da li’bbai. Wa zai gaje shi cikin wadannan? Kuma ya rabon zai kasance?
Amsa
Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari gida: 24, a bawa matarsa : 3, kakarsa : 4, ragowar sai a bawa ‘ya’yansa su raba.
Allah ne mafi sani.
Na Ga Wandona A Jike Da Maniyyi Bayan Na Kammala Sallar La’asar, Ya Zan Yi?
Tambaya:
Aslamualaikum MALAM na tashi da janaba nayi salar asuba da azahar da kuma laasar, duk nayi sallah sai bayen naje wanka da yemma naga wando na da alamun manniyi shin ya ingancin sallolina na baya? nagode
Amsa:
Wa’alaikum assalam, mutukar ka tabbatar a baccin asuba maniyyin ya fito, to ya wajaba ka sake asuba da azahar da la’asar din.
In har ka yi wani baccin bayan azahar to za ka danganta janabar ne zuwa ga baccin karshe da ka yi, ta yadda sallar da ka yi bayan baccin karshe ita za ka sake, kamar yadda Imamu Malik ya rawaito a Muwadda daga Sayyady Umar.
Allah ne mafi sani