Aminu Muktar Dan Alhaji">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Wadata Manoma Da Kayan Aiki Ne Kadai Zai Rage Tsadar Abinci A Nijeriya – Kamilu Sugau

by Aminu Muktar Dan Alhaji
January 29, 2021
in LABARAI
2 min read
Wadata Manoma Da Kayan Aiki Ne Kadai Zai Rage Tsadar Abinci A Nijeriya – Kamilu Sugau
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Wani hamshakin manomi a yankin karamar hukumar Lere ta jihar Kaduna, Alhaji Kamilu Sa’idu Sugau, ya ce kayayyakin abinci za su yi sauki ne kawai idan gwamnatin tarayya ta samar wa manoma dukkan abubuwan da ke bukata domin habaka sana’arsu ta noma.Alhaji Kamilu Sugau wanda ke zantawa da wakilinmu a garin na Sugau, ya koka cewa karancin takin zamani musamman samfurin kamfa na daga cikin matsalolin da ke ci wa manoman kasar nan tuwo a kwarya.

Ya lura tare da bayyana damuwa cewa duk da ikirarin da gwamnatin tarayya mai ci yanzu ke yi na bunkasa noma a kasar nan, har yanzu manoma na fuskantar matsala wajen sayan takin zamani samfurin kamfa N P K 15-15-15.Ya yi bayanin cewa samun wadataccen takin zamani zai taimaka ba kadan ba wajen habaka noma a fadin Nijeriya.
Duk da yake ya ce gwamnatin tarayya ta yi kokari wajen samar da takin zamani samfurin yuriya amma ko kusa hakan bai wadatar ba, domin kuwa kamfa din na da matukar mahimmanci wajen bunkasa amfanin gona.Ya kuma lura cewa wadansu yan baya ga dangi na suna gurbata takin zamani dan Buhari, domin haka ya ce samar da takin zamani samfurin kamfa zai tallafa wa manoman ba kadan ba.
Ya nuna bukatar da ke akwai ga gwamnatin tarayya da na johohi su taimaka wa manoma ta hanyar samar musu da taraktocin noma, domin saukake musu wahalhalun da suke sha a harkarsu ta noma.Ya lura cewa duk da yake gwamnatin tarayya ta yanzu tana nuna ta himmatu sosai wajen mai do da martabar noma, amma manoma sun sami tallafi a fannin noma a lokacin gwamnatocin da suka gabata fiye da gwamnati mai ci yanzu.
Alhaji Kamilu Sugau, ya yi zargin cewa ko da gwamnatin na fitar da tallafin noma ba ya zuwa hannun manoma na gaskiya, sannan ya jaddada bukatar da ke akwai ga gwamnatin ta rika tallafa wa manoma na gaskiya domin kwalliya ta biya kudin sabulu.
Ya bukaci gwamnatin tarayya ta rika sayan kayayyakin amfanin gona daga hannun manoma da daraja a lokacin kaka.Ya nunar da cewa hakan zai taimaka wa manoma wajen habaka sana’arsu ta noma.To sai dai ya ce ko idan gwamnatin za ta sayi amfanin gona ya kamata ta tabbatar ta bai wa mutanen kirki ne wannan aikin domin ganin sun sayi amfanin gona daga manoma na gaskiya, ba yan ba-ni-na-iya ba.
Ya yi bayanin cewa akwai wuraren adana kayan amfanin gona na gwamnati a sassa daban-daban na kasar nan wanda idan gwamnatin ta so za ta sayi amfanin gona mai tarin yawa kuma da daraja, domin karfafa wa manoma gwiwar noma abinci mai yalwa.

SendShareTweetShare
Previous Post

‘Yan Abbatuwa Ikobo Sun Yaba Da Ziyarar Sarkin Hausawan Legas

Next Post

A Zuciya Ake Tsoron Allah Ba Yaudara Ba – Nasiru Gulma

RelatedPosts

Garkuwa

An Kama Sojan Da Ke Kai Wa ‘Yan Ta’adda Kayan Sojoji A Zamfara

by Aminu Muktar Dan Alhaji
2 hours ago
0

Daga Sulaiman Ibrahim "An kama wani jami’in soja da budurwarsa...

Aikin Wutar Mambilla  A Takardu Kawai Yake, Inji Gwamnonin Arewa Maso Gabas

Aikin Wutar Mambilla A Takardu Kawai Yake, Inji Gwamnonin Arewa Maso Gabas

by Aminu Muktar Dan Alhaji
5 hours ago
0

Kungiyar gwamnonin arewa maso gabas sun nuna rashin jin dadin...

Bindiga

Gwamna Ortom Ya Yabawa Umarnin Buhari Na Hana Mallakar  AK47 Ba Bisa Ka’ida Ba

by Aminu Muktar Dan Alhaji
6 hours ago
0

Daga Rabiu Ali Indabawa, Gwamnan Jihar Benue Samuel Ortom a ranar...

Next Post
A Zuciya Ake Tsoron Allah Ba Yaudara Ba – Nasiru Gulma

A Zuciya Ake Tsoron Allah Ba Yaudara Ba - Nasiru Gulma

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version