WAEC Ta Rike Sakamakon Jarabawar Mutum 1,021

Daga Umar A Hunkuyi

Hukumar shirya jarabawar kammala manyan makarantun Sakandare ta Yammacin Afrika, (WAEC) ta bayar da sanarwar sakamakon jarabawar da ta shirya a tsakanin watannin Janairu da na Fabrairu 2018, a ranar Talata.

Shugaban hukumar a wannan kasar, Olu Adenipekun, shi ne ya bayyana sakamakon a Legas, inda ya ce, hukumar ta rike sakamakon jarabawar na mutane 1,021.

An dai amince da shirya karin yin jarabawar ce ga daliban na bayan fage a wannan kasa tamu da ma sauran kasashe biyar da ke yankin, a taro na 65 da hukumar ta yi a watan Maris na shekarar 2017, wanda hakan ya mayar da jarabawar da hukumar ke shirya wa suka zama uku a duk shekara.

A cewar Olu Adenipekun, hukumar ta rike sakamakon jarabawar mutanan ne sabili da sun aikata laifukan magudi daban-daban a lokacin jarabawar.

Ya ce, ana bincikar laifukan na su, da an gama binkcika kuma za a hannata matsalolin na su ga kwamiti na musamman domin ya duba ya yi hukunci. Bayan nan ne za a sanar da mutanan da abin ya shafa hukuncin da kwamitin ya yi a kansu.

A cewar sa, mutane 11,721, ne suka yi rajistan daukar jarabawar, amma mutane 11,307, ne suka zauna daukan jarabawar.

Da yake bayyana sakamakon jarabawar dalla-dalla, Shugaban ya ce, mutane 8,113 ne suka sami cinye jarabawar da makin Kiredit zuwa sama a darussa biyu.

Sannan ya ce, mutane 6,375 sun ci jarabawar da makin Kiredit zuwa sama a darussa uku, sa’ilin da mutane 4,762 suka sami cin jarabawar da makin Kiredit zuwa sama a darussa hudu.

Olu Adenipekun, ya ce, mutane 3,263 sun ci jarabawar da makin Kiredit zuwa sama a darussa biyar, inda kuma mutane 2,010 suka ci jarabawar da makin Kiredit zuwa sama a darussa shida.

“Jimillan mutane 1,937, kimanin kashi 17.13, sun sami cin jarabawar da mikidarin Kiredit a darussa biyar zuwa sama, da suka hada da darussan Turanci da Lissafi.

Kwatankwacin su da suka sami wannan matsayin a jarabawar ta shekarar 2017, shi ne kashi 26.01.

“Daga abin da muka bayyana na wannan sakamakon, za mu iya cewa, an fadi a jarabawar, in an kwatanta da abin da aka samu a shekarar 2016 da ta 2017.

“Don haka muna kira ga dalibai da su dauki wannan jarabawar da mahimmanci,” in ji shi.

Shugaban ya nu na jin dadinsa da yadda ‘yan Nijeriya suka rungumi wannan karin shirya jarabawar da aka yi.

Olu Adenipekun, ya ce, bullo da karin shirya wannan jarabawar zai magance, matsalar cuwa-cuwar jarabawar da wasu mutane sukan so yi.

Ya kuma ce, Hukumar shirya jarabawar ta yammacin Afrika, ta bullo da wannan karin ne domin ta tallafawa kokarin gwamnatoci a dukkanin matakai na fadada sha’anin ilimin su a nahiyar ta Yammacin Afrika.

Olu Adenipekun, ya bukaci dukkanin mutanan da suka san sun zana jarabawar da su binciki sakamakon jarabawar na su a shafin hukumar na yanar gizo

Exit mobile version