Wai Shin ‘Karin Magana’ Mace CE Ko Namiji NE?

Magana

Gabatarwa:

Akwai takaddama a game da jinsin Karin Magana. Wasu su ce ITA Karin Magana, wasu kuma su ce SHI Karin Magana. Ko su ce Karin Magana NE, wasu kuwa su ce Karin Magana CE. To wai shin wanne ne daidai? Wannan makala za ta dilmiya cikin bincike don gano ainihin takamemen jinsin Karin Magana.

Karin Magana

Farfesa Adbdukadir Dangambo a littafinsa na Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari) wallafar Amana publishers, shekarar 2008, shafi na 67, sakin layi na farko, da yake bayanin hikima da sarrafa harshe, ya ce:

Karin magana, dabara ce ta dunkule magana mai yawa a cikin zance ko ‘yan kalmomi kadan, cikin hikima. Karin magana, yawanci, YAna da bari biyu: bari na farko yana yin jimlataccen bayani ko furuci na wata manufa, bari na biyu kuwa, yana yin sharhi ko karin bayani, kan abin da bari na farko ya fada. misali

Bari na farko : Garin dadi na nesa,

Bari na biyu :  Ungulu ta leka masai

Shi kuwa Yakubu Musa Muhammad a nasa littafin mai suna ‘Adabin Hausa’ dab’in kamfani buga littattafai na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a shafi na 59 babi na uku cewa ya yi kowanne harshe na duniya yana da salon maganarsa. Wadansu harsuna suna da karin magana, wadansu ba su da SHI. Hausa tana daga cikin harshen da Allah Ya yi mata baiwa da karin magana.

Ya kara da cewa:

SHI karin magana wata ‘yar gajeriyar jimla ce ta hikima; wadda ta kunshi ma’ana mai yawa in za a tsaya a yi bayaninta. Kuma YAkan kara wa salon magana dadi da armashi, YAkan nuna gwanintar iya maganar mai magana, kuma YA sa mai sauraron maganar rashin kosawa da zancen da aka gaya masa.

Muhammad Baban Zara Hassan a kasidar da ya gabatar a wajen bikin makon Hausa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ranar 27 ga watan Maris na shekarar 1985, mai taken ‘Matsayin Hausa A Kafofin Watsa Labarai (Jaridu)’ ya yi bayanin cewa:

Da yake Allah ya yi wa Hausa baiwa da karin magana mai tarin yawa, jaridu kan yi kokarin yin amfani da SHI domin fito da al’adun Hausawa tare da bunkasa Harshen.

Haka nan a littafin Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa na aji daya don Kananan Makarantun Sakandare da kamfani dab’i na Jami’ar Ibadan ya wallafa a shekarar 2011, a shafi na 45, Malam Rabiu Zarruk da Malam Abubakar Kafin Hausa da Dokta Bello Alhassan sun yi bayanin cewa:

Karin Magana gajeren zance ne wanda yake kunshe da hikima. A cikin karin magana za a samu hikima iri biyu. Ta farko ita ce yadda jama’a ke lura da al’amura.

Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya a littafinsa na Labarun Gargajiya na 2 dab’in kamfanin buga littattafai na Jami’ar Ibadan, shekarar 2009 shafi na 62 da ya yi bayani karkashin ‘Wasu Darussa Cikin Karin Magana’

Karin maganaR Hausa suna cike da koyar da halayen zaman duniya, a shirye cikin azancin magana.

Shi kuwa Yusufu Yunusa a littafinsa na Hausa A Dunkule da Triump ta soma bugawa a shekarar 1989, magana ya yi a kan karin magana da misalai da dama. Sai dai in ban da a shafi na bi bai fito fili ya nuna Hausa a dunkule din nan fa Karin Magana yake nufi ba. A shafin ne ya yi bayani a game da tsare-tsaren karin maganar Hausa.

Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, da Farfesa Mu’azu Sani Zariya, da Farfesa Said Muhammad Gusau da Malam Tanimu ‘Yar Aduwa a littafinsu na Darussan Hausa don Manyan Makarantun Sakandare littafi na daya, da kamfanin dab’i na Jami’ar Ibadan ya wallafa a shekarar 2007, shafi na 30 sun yi bayanin cewa Karin magana tsararren zance ne wanda yake zuwa a gajarce na hikima da zalaka tare da bayar da ma’ana gamsasshiya, mai fadi, mai yalwa, musamman idan aka tsaya aka yi bayani daki-daki.

Suka ci gaba da bayanin cewa ashe ke nan Karin Magana takaitacciyar magana ce ‘yar kil wadda ta kunshi hikima da zantuttukan ma’ana. Suka kara da cewa:

Karin Magana YAkan zo cikin labaru da zantuka da wake-wake da sauransu. Karin Magana yawanci kukan kurciya ne inda YAkan sanya magana ta yi armashi da dadi kamar an zuba ka-fi-zabo a miya. Kusan Karin Magana kome da ruwanKA ne, YAkan yi katsalandan a duk bangarori na rayuwa. Dubi Karin MaganaN nan da akan ce Duniya juyi-juyi, kwado ya fada a ruwan zafi.

Sai dai da na Rubuta ina neman Karin Magana a Matambayi Ba Ya Bata wato Google, sai ya nuna muna:

Karin Magana – Wikipedia

Ha.m.wikipedia.org/wiki/

Duniya ta fi bagaruwa iya jima!

Wannan karin magana CE kuma habaici ne. Ana yin amfani da ITA ga irin mutanen nan…

Har ila yau a dai shafin ne can kasa na ga an rubuta:

10 Sep 2013 … Indai a tsarge maka Karin Magana NE daidai-wa-daida a Mushakata da HausaK ta gaskiya ba…

A lura da kyau ina amfani da manyan kalmomi ko haruffa ne don nuna jinsin Karin Magana. NE na nuni da jinsin Namiji. CE na nuni da jinsin mace. N na nuni da jinsin namiji. R na nuni da jinsin mace. SHI wakilin suna ne na namiji. ITA kuwa wakilin suna ne na Mace.

A dai wannan lalube da nake yi, a farko-farkon lokacin da gidan rediyon BBC Hausa ya soma neman a aika masa da Karin Magana da ba safai ake amfafi da su ba, suna gama karanta sakon wani, sai na ji mai gabatarwan ya ce:

ITA Karin MaganaRmu ta yau ke nan da muka samu daga…

Ku ma kuna iya aiko mana da Karin MaganaR da ba safai aka cika amfani da ITA ba.

Ina jin haka sai na yi maza na sanya a shafina na sada zumunta na Fesbuk ina tambayar Jama’a cewa anya BBC Hausa sun yi daidai kuwa wajen Jinsin mace da suka ba Karin Magana?

A shirinsu na washegari/kashegari sai na ji sun canza sun ce:

SHI Karin MaganaNmu na yau ke nan da muka samu daga…

Ku ma kuna iya aiko mana da Karin MaganaN da ba safai aka cika amfani da SHI ba.

Bari mu koma shi kansa sunan na KARIN MAGANA. KARI namiji ne, MAGANA kuma mace. Magana ake yi a kan KARIN. Wanne KARI? Kari na Magana. ITA magana da SHI kari. SHI kari da ITA magana. Saboda haka idan muka yi la’akari da bayanan da Malamai suka yi a wannan Makala, za mu fahimce cewa Karin Magana dai namiji ne ba mace ba.

Sai dai kafin in kammala wannan bayani nawa, zan kawo kadan daga cikin muhimmancin Karin Magana, da jerin wasu Karin Maganganun kamar yadda manazarta suka yi nazari.

Muhimmancin Karin Magana

Su Farfesa Ibrahim Yaro Yahaya, da Farfesa Mu’azu Sani Zariya, da Farfesa Sa’id Muhammadu Gusau, da Malam Tanimu ‘Yar Aduwa sun yi bayanin cewa Karin Magana ya dangaci abubuwa da yawa tamkar al’adu da tarihi da fasaha da hikimomin Hausawa ne. Yakan ayyana falsafar Hausawa dangane da wasu abubuwa da suka shafi rayuwa kamar arziki da alheri da ilimi. Karin Magana na taimakawa kwarai wajen kyautata tarbiyya, da daidaita dabi’un mutane, da kyautata zumunta.

Saboda haka za mu iya cewa Karin Magana tamkar hoto ne na rayuwar al’uma, kuma rumbu na dabi’u da al’adu har da addinin na Hausawa.

Domin akwai Karin Magana na lokacin Maguzanci, da na lokacin Addinin Musulunci, da na lokacin zuwan Turawa, har da na bayan zuwa cutar Ebola Nijeriya.

Ga goma daga cikin Karin Magana da ake da su:

  1. Hayaki ba ya buya gidan mai rowa
  2. Inuwar bagaruwa ga sanyi ga kaya
  3. Ga mu ga Allah damo a hannun mata
  4. Dan tsakon jimina gagara shaho dauka
  5. Abin na yi ne an biya wa bazawara Hajji
  6. Don kai ake hula har kunne yake samu
  7. Ba ni na kashe zomon ba rataya aka ba ni
  8. Maradinsa ba ya kunya
  9. Kaza mai ‘ya’ya, ita take gudun shirwa.
  10. Ban sa a ka ba in ji barawon hula.

Kammalawa

Takaddama a game da jinsin Karin Magana dadaddiyar aba ce da wannan Makala take sa ran taimakawa wajen magance ta. Ban da littattafai da dama da aka wallafa na Karin Magana, gidajen Rediyo da Talabijin na ba da tasu gudunmawar musamman filin nan na Wasa Kwakwalwa na Rediyon Nijeriya na Kaduna da Ahmad Aja Gwarzo ya saba shiryawa da gabatarwa. Haka nan Rediyon Firidom da talabijin na DITB da Alheri rediyo da ke Kaduna duk su ma ba a bar su a baya ba.

 

Daga

Is’hak Idris Guibi

Babban Malami a

Sashen Nazarin Harsuna na Kwalejin Kimiyya da Fasaha Ta Tarayya da ke Kaduna.

Imel: guibi2017@gmail.com

08023703754

Mun taba wallafawa a ranar 24 ga Oktoban 2014, lokacin da jaridarmu take fita mako-mako da sunan LEADERSHIP Hausa

Edita

Exit mobile version