Umar Faruk" />

Wainar Da Aka Toya A Taron Manyan Shugabannin Tsaro Da Masarautar Zuru

Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Muhammad Adamu Abubakar tare da haxin gwiwar gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu da kuma taimakon shuwagabannin hukumomin tsaro na ‘yan sandan sirri (DSS), da ta tattara bayanan sirri (NIA) da sauransu, ya  gudanar da taron tattaunawa na musamman kan yadda za a samar da tsaro a Masarautar Zuru da ke jihar.

Taron tattaunawar dai an gudanar da shi ne a xakin gudanar taro na garin Zuru a ranar Laraba da daddare, inda duk wani mai ruwa da tsaki a Masarautar Zuru da kuma shuwagabannin kungiyoyi da na addinai da kuma sauran su an gyayace su domin tattauna hanyoyin samar da mafita ga rashin ingantacen tsaro da ake fama dashi a Masarautar ta Zuru da ke da kananan hukumomin mulki huxu kamar Zuru, Sakaba, Fakai da kuma Danko-Wasagu wanda su ne ke fama  da rashin tsaro na satar shanu, garkuwa da mutane da kuma yawan kisan gilla da ake yiwa talakawan yankunan da sauran su.

Inda aka bai wa wasu manyan mutane daga Masarautar dama don bayyana wasu daga cikin matsalolin da ka cima tsaro a yankin na Masarautar Zuru tuwo a kwarya da kuma ba da shawarwari kan yadda za a dakile matsalolin na tsaro a dukkan yankunan Masarautar ta Zuru da ke xaya daga cikin masarautun huxu da ke akwai a cikin jihar ta Kebbi.

A cikin waxanda suka gabatar da jawabai a wurin taron sun haxa da Muhammadu Magoro, Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na kasa, Alhaji Muhammadu Kiruwa Zuru, Shugaban ‘Yan Sa-kai  a Masarautar Zuru Jonh Mani Giwa, Shugaban Kungiyar ci gaban Masarautar Zuru,(ZEDS) Mai-Ritaya Air Bice Mashal Bala Sallau Ribah da kuma Shugaban Kungiyar CAN a garin na Zuru  Pastor Caleb Bakibi .

Sauran sun haxa da Maimartaba Sarkin Zuru, Muhammadu Sani Sami na biyu, Gwamnan jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu, Sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya, Muhammad Adamu Abubakar da kuma Shugaban DSS na kasa, Alhaji Yusuf Magaji Bichi da suaransu .

Inda dukkan nin waxannan mutanen sun bayyana irin mastalolin da kuma yadda za a dakile wannan rashin tsaro. Daga nan ne sufeto janar Muhammad Adamu Abubakar ya haxa wani Kwamitin gaggawa domin sake wani zama na musamman a ofishinsa da ke Abuja domin su fito da kundin tsarin yadda Masarautar Zuru za ta samu ingantacen tsaro kamar yadda sauran yankunan jihar ta Kebbi ke da kyakkyaawan tsaro domin su samu zaman lafiya.

Kwamitin na gaggawa da sufeto janar ya haxa ya haxa da Muhammadu Magoro, Shugaban Kungiyar Miyetti Allah na kasa Muhammad Kiruwa Zuru, shugaban kungiyar CAN na garin Zuru pastor Caleb Bakibi, shugaban kungiyar ZEDS Mai-Ritaya Air Bice Mashal Bala Sallau Ribah, Sarkin Malaman Zuru, Alhaji Abdulraman Balarabe Hamza sai kuma daga karshe wakilin Maimartaba Sarkin Zuru wanda Gwamna Abubakar Atiku Bagudu zai jagoranci waxannan mutanen zuwa ofishin na sufeto janar domin kara tattaunawa a cikin mako mai zuwa.

Bugu da kari sufeto janar ya janyo hankalin al’ummar Masarautar Zuru cewa matsalar tsoro ta kowa da kowa ce ba ta mutun xaya ba ce ko  ya ta’allaka ga gwamnatin ko hukumomin kula da tsaro ba ne kai.

“Saboda haka duk wanda ke da ra’ayi na son ya sadaukar da kansa wurin gudanar da aikin Sa-kai ya ba da sunan sa ga gwamnatin jihar domin ta tantance shi sai a turo ma hukumar ‘yan sanda domin bashi ko basu horo ta yadda za su iya aiki na haxin gwiwa da jami’an tsaro da kuma sanya su cikin tsarin da hukumar ‘yan sanda ta fito dashi wanda jihar Kebbi ta zama ta biyu da ta kaddamar da kwamitin wannnan tsarin samar da tsaro a dukkan yankunan da kuma kauyukan kasar nan shi ne (community policing) . Wanda Jama’a ne za su zama ‘yan sandan kansu a cikin unguwannin su da kuma garuruwansu,” in ji Adamu.

Daga karshe shugaban ‘yan sandan ya gode wa dukkan al’ummar Masarautar Zuru da kuma gwamnatin jihar Kebbi a karkashin jagorancin Gwamna Abubakar Atiku Bagudu kan irin haxin kai da suka bayar wurin tabbatar da cewa sun ba da shawarwari da kuma samar da wasu hanyoyin da za a kara domin dakile matsalolin tsaro a masarautar ta Zuru.

 

Exit mobile version