Kusan sati biyu kenan wannan shafi yana ta tattaunawa akan matsalar tsaro ta taki ci taki cinyewa musamman a arewacin Kasar. Bari muyi waiwaye akan wasu abubuwa da suka faru a baya.
Lokacin da Goodluck Ebele ya ayyana cewar zai kuma yin takara a zaɓen 2015 da Buhari ya ci zaɓe, nayi rubutu akan dama ya hakura da wannan takarar, dalilai na kuwa a lokacin basu wuce yadda ake take hakkokin bil’adama a kasar nan, da kuma yadda ƴan Boko Haram suke cin karen su babu babbaka a lokacin. Ga duk wani mai kishin al’umma a wannan lokacin, bana tunanin zaiyi tunanin bama Ebele ba, ko wa jam’iyyar PDP ta tsayar, bazai samu kuri’un al’umma ba. Hakan ce kuwa ta tabbata, domin kowa ya juyawa Mai Malafa baya saboda rashin kataɓus dinsa a kashe-kashen da Boko haram suka dinga yi. Har na kafa misali a wannan lokacin da wani tsohon Shugaban Kasar Amurka Lyndon B Johnson, wanda tsohon Mataimakin Shugaba F Kennedy ne, bayan an kashe Kennedy aka zaɓe shi a matsayin Shugaban kasa na 36. Johnson ya samu duk wani tagomashi a kasar, yayi duk wani kokari don ci gaban Kasar sa, amma babban abinda ya janyo masa koma baya shine yadda ƴan Kasar suka dinga ganin wallensa akan yakin Vietnam da sojojin Amurka suka dinga mutuwa. Adawa har daga cikin jam’iyyar sa ya dinga samu duk saboda wannan yaki na Vietnam wanda Amurka ta aika da sojojin ta. Babban abin mamaki shine, yadda wannan Shugaba ya bugi kirji ya ayyana cewar ya janye takarar sa a karo na biyu, saboda yadda ya bakantawa Kasar sa rai, ya kuma janyo asarar dubunnan sojojin a yakin na Vietnam. Har kawo yanzu ana martaba Johnson Baines saboda wannan namijin kokari. A wannan lokacin na kintata irin adawar da Jonathan yake samu har daga cikin jam’iyyar sa, wacce ga duk wani mai hankali da tunani, ba zaiyi fatan Mai Malafa ya maimaita ba. Wannan kenan.
A shekarar data gabata ta 2019 tsakanin watan hudu ko na biyar, firaministan Kasar Mali Soulmeylou B Maiga ya ayyana cewar dashi da ƴan majalisar sa sun ajjiye Shugabancin su, saboda sun kasa wani kataɓus akan yadda rikicin Fulanin ƴan Kasar da wasu kabilu yaki ci yaki cinyewa. Ya ayyana hakan ne washegarin ranar da aka kai wani hari kan Fulani da kusan mutane 150 suka rasa rayukansu a inda ake cewa Central Mali. Wannan kisan ya tada hankalin kafatanin ƴan Kasar, kuma wannan ajjiye Shugabancin da Firaministan yayi, ya janyo wasu suka kirashi da cikakken ɗan kishin kasa. Wannan kenan.
Mailafiya ba kamar Sanata Abaribe bane da zance Shugaba Buhari ya sauka daga kan mulkin sa, kuma ba kamar ƴan jam’iyyar PDP nike ba, da zan dinga murna akan abinda ke faruwa saboda aga gazawa da kasawar wannan Gwamnatin. To amma dukkan mu har da ita Gwamnatin babu wanda zai musanta cewar harkar tsaro ta kuma taɓarɓarewa a kasar. Babu wanda yake musanta cewar mun ga kasawa da sakaci daga gurare da dama, sannan kuma babu wanda zai kasa kalubalantar wannan Gwamnatin, walau MU da ake ganin muna kareta, da kuma waɗanda ake ganin suna mata ADAWA.
Idan har Shugaba Buhari ba toshe kunnuwan sa zaiyi akan kiraye-kirayen da ake masa ba, to inaga babu abinda ya dace a yanzu daya wuce a sanya dokar ta ɓaci a harkar tsaro. A tunkari ƴan Boko Haram, masu satar al’umma da kuma masu kisan sari ka noke. Wannan itace kaɗai hanyar da zata tabbatar da cewa wannan Gwamnatin da gaske take. Amma a yanzu dubunnan mutane da dama sun fara dawowa daga rakiyar wannan Gwamnatin. Wanda hakan koma baya ne ga tunanin CANJI da haɗakar jam’iyyun da ta gina APC.
Mun ga yadda al’umma suka dinga ihu lokacin da wannan Gwamnatin ta dawo. Saboda kowa yana ganin lokacin kawar da Boko haram, farfado da tattalin arzikin kasa, tare da kawar da cin hanci da rashawa. A dukkan abubuwan da suka kawo jam’iyyar haɗaka ta APC, kusan tana kokarin cika wannan alkawarurrukan, amma ta bangaren tsaro kusan mutane basuda abin cewa, saboda yadda har kawo yanzu mutane ke cikin zaman dar-dar, banda kashe-kashen Boko haram, garkuwa da mutane da kuma kashe-kashen dake faruwa a jihohin Zamfara da Katsina.
Mutane kowa na ta rokon Gwamnati ta sallami jagororin rundunonin tsaro ta kasa. Koda ace Gwamnati bazata koresu ba, to ya kamata ta canza salon yadda zata tunkari waɗannan ƴan barandan.
Allah ka kawo mana ɗauki. Ka taimaki wannan Gwamnatin wajen kawo karshen wannan ibtila’in da muke ciki.
Caption
Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Borno Farefesa Babagana Zulum da kuma Mai Martaba Shehun Borno Abubakar Umar El-Kanemi a yayin da shugaban kasar ya kai ziyarar jaje jihar Born sakamakon harin da ‘yan Boko Haram suka kai kauyen Auno, ranar 12 ga watan Fabrairu 2020.