Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Waiwaye A Kan Wasu Ayyukan NIS A Filin Jiragen Sama Na Abuja A 2020

by Muhammad
December 25, 2020
in RAHOTANNI
2 min read
Filin Jirgi
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Sulaiman Ibrahim,

 

samndaads

Shekarar 2020 ta zo da kalubale da yawa, daga ciki akwai batun annobar da ta addabi duniya wato cutar Korona, hakan ya tilastawa kasashen duniya rufe kan iyakokin kasashensu, daga bisani kuma aka samu saukin hauhawar cutar, hakan ya jawo sausauta hana zirga-zirga a tsakanin kasashen acikin shekarar.

 

 

Akalla masu shige da fice 239,114 suka shugo ta NAIA, Abuja tsakanin 01 Ga Janairu, 2020 zuwa 15th Disamba, 2020. A yayin da ‘yan Nijeriya 73,582 da 46,665 wadanda ba ‘yan Nijeriya ba suka fita daga kasar ta filin jirgin saman NAIA, Abuja zuwa wurare daban-daban na kasashen waje. Hakanan, ‘yan Nijeriya 81,277 da 37,590 wadanda ba ‘yan Nijeriya ba sun shigo kasar ta hanyar jirgin saman NAIA Abuja.

 

An koro ‘yan Nijeriya 625 sannan 24 aka dawo da su gida saboda laifuka daban-daban da suka shafi dokar shige da fice ta kasashen waje. Haka zalika, wasu ‘yan kasashen waje 12 da suka kasa cika ka’idar shigowa kasar Nijeriya an ki karbar su sabida haka an maida su inda suka futo.

 

‘Yan Nijeriya 34 wadanda galibinsu ‘yan mata ne, an ki amincewa da takardar tafiyarsu saboda rashin bin doka da kuma keta dokokin shige da fice da sauran dokokin da ke akwai.

 

 

Kwamitin kula da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe na kasa da kasa, a dai-dai wannan lokacin, ya kama ‘yan Nijeriya 100 wadanda laifukan su ba su da alaka da shige da fice, kamar su lamuran da suka shafi fataucin kwayoyi, Laifukan Yaki da Cin Hanci da kuma Fataucin Mutane.

 

Wannan Nasarar an same tane saboda jajircewar shugaban hukumar NIS, da ya kirkiri tsarin shigar da bayanan masu shige da fice (MIDAS) don habaka tsarin iyakokin filin jirgin sama.

Da kawo wannan tsarin, Ma’aikatan jirgin sama suna murna da farin ciki musamman ga tsarin kula da masu shige da fice.

 

Kwanturolan Janar na Hukumar Shige da Fice ta Kasa, CGI Muhammad Babandede, MFR, ya yaba wa Kwanturolar Hukumar Kula da Shige da Fice mai kula da filin  jirgin saman Nnamdi Azikiwe na kasa da kasa dake Abuja, Sadat Hassan, pcc, saboda aiki tukuru wajen sa ido ga masu shige da fice wanda wannan ya bada nasarar kame wadannan mutane.

 

Hukumar ta NIS tana yin kira ga jama’a da su ba da hadin kai ga masu gudanar da aiki a Filin Jirgin saman a yayin da ake gudanar da aikin domin rage hulda da mutane don kaucewa yaduwar cutar Korona

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Ta’aziyya Tare Da Jinjina Ga Marigayi Sam Nda-Isaiah (II)

Next Post

Dakarun NIS Sun Ceto Jariri Dan Mako Uku Daga Masu Safarar Mutane Ta Teku  

RelatedPosts

Makiyaya Ondo

Korar Makiyaya A Ondo: Cikakken Rahoton Yadda Ta Kaya Taron Gwamnoni Da Shugabannin Fulani

by Muhammad
1 day ago
0

Daga Khalid Idris Doya, Gwamnonin Nijeriya sun kira taron gaggawa...

Kasafin 2021

Hotunan Sabbin Shugabannin Rundunonin Tsaro

by Sulaiman Ibrahim
2 days ago
0

Major-Gen. Leo Irabor, Chief of Defence...

Garban

Garban Kauye Farawa Ne Allurar Dinke Barakar Kumbotso – Muslihu Yusuf Ali

by Muhammad
3 days ago
0

Daga Abdullahi Muhammad Sheka, An bayyana zaben Sabon shugaban Karamar...

Next Post
NIS

Dakarun NIS Sun Ceto Jariri Dan Mako Uku Daga Masu Safarar Mutane Ta Teku  

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version