Shekarar 2020 ta zo da kalubale da yawa, daga ciki akwai batun annobar da ta addabi duniya wato cutar Korona, hakan ya tilastawa kasashen duniya rufe kan iyakokin kasashensu, daga bisani kuma aka samu saukin hauhawar cutar, hakan ya jawo sausauta hana zirga-zirga a tsakanin kasashen acikin shekarar.
Kasarmu Nijeriya itama ba a barta a baya ba, tana da nata dokokin wajen kokarin dakile yaduwar cutar, ganin cewa hukumar kula da shige da fice ta Nijeriya (NIS) itace babbar hukumar dake kula da kan iyaka a filin jirgin saman Nnamdi Azikwe na Abuja (NAIA), dole ta tashi tsaye don tabbatar da kariya ga ma’aikatanta da baki masu shige da fice ta hanyar raba gilashin garkuwa, takunkumin fuska, safar hannu da abin tsaftace hannu.
Akalla masu shige da fice 239,114 suka shugo ta NAIA, Abuja tsakanin 01 Ga Janairu, 2020 zuwa 15th Disamba, 2020. A yayin da ‘yan Nijeriya 73,582 da 46,665 wadanda ba ‘yan Nijeriya ba suka fita daga kasar ta filin jirgin saman NAIA, Abuja zuwa wurare daban-daban na kasashen waje. Hakanan, ‘yan Nijeriya 81,277 da 37,590 wadanda ba ‘yan Nijeriya ba sun shigo kasar ta hanyar jirgin saman NAIA Abuja.
An koro ‘yan Nijeriya 625 sannan 24 aka dawo da su gida saboda laifuka daban-daban da suka shafi dokar shige da fice ta kasashen waje. Haka zalika, wasu ‘yan kasashen waje 12 da suka kasa cika ka’idar shigowa kasar Nijeriya an ki karbar su sabida haka an maida su inda suka futo.
‘Yan matan sun kasance cikin wadanda ake fataucin su ne da safarar su da nufin tilasta musu yin karuwanci da yin lalata, mafi yawancinsu ‘yan tsakanin shekaru 18 zuwa 28. Garin da za akaisu shine Dubai, UAE. Baya ga haka, an turasu zuwa hukumar dake kula da fataucin mutane NAPTIP don cigaba da bincike akan wadanda suke safararsu. Hukumar tayi nasarar cafke mutane 6 ( maza 4 da mata 2), sannan kuma anyi nasarar gano mutune 3 mazauna Kasar Dubai, wadanda ke tarbar wadanda aka fatauce.
Kwamitin kula da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe na kasa da kasa, a dai-dai wannan lokacin, ya kama ‘yan Nijeriya 100 wadanda laifukan su ba su da alaka da shige da fice, kamar su lamuran da suka shafi fataucin kwayoyi, Laifukan Yaki da Cin Hanci da kuma Fataucin Mutane.
Wannan Nasarar an same tane saboda jajircewar shugaban hukumar NIS, da ya kirkiri tsarin shigar da bayanan masu shige da fice (MIDAS) don habaka tsarin iyakokin filin jirgin sama.
Da kawo wannan tsarin, Ma’aikatan jirgin sama suna murna da farin ciki musamman ga tsarin kula da masu shige da fice.
Kwanturolan Janar na Hukumar Shige da Fice ta Kasa, CGI Muhammad Babandede, MFR, ya yaba wa Kwanturolar Hukumar Kula da Shige da Fice mai kula da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe na kasa da kasa dake Abuja, Sadat Hassan, pcc, saboda aiki tukuru wajen sa ido ga masu shige da fice wanda wannan ya bada nasarar kame wadannan mutane.
Hukumar ta NIS tana yin kira ga jama’a da su ba da hadin kai ga masu gudanar da aiki a Filin Jirgin saman a yayin da ake gudanar da aikin domin rage hulda da mutane don kaucewa yaduwar cutar Korona