Waiwaye Game Da Adabin Zamanin Da Na Kasar Sin

Daga Amina Xu,

Takaitaccen bayani

Adabi, wani kashi ne mai kuzari sosai a cikin al’adun kasar Sin. A cikin dogon tarihi, adabin gargajiyar kasar Sin ya hada da manyan ra’ayoyin al’adun kasar Sin, ya bayyana burin jama’ar kasar na neman gaskiya, da alamun kasar na musamman. Akwai nau’o’i daban daban na adabin kasar Sin, kamar tatsuniyoyi na zamanin da da can, da wakokin daular Tang da ta Song, da labaran daular Ming da na Qing da dai sauransu. A cikin shekaru sama da dubu daya, an samu shahararrun marubuta da bayanai masu dimbin yawa.

 

Tatsuniyoyi na zamanin da da can

Mutum dake cikin littafi mai suna Hongloumeng-Jia Baoyu

Mutanen zamanin da da can sun rubutu wadannan tatsuniyoyi a kokarin kafa wata duniya mai ban al’ajabi da kuma nisa sosai bisa tunaninsu a yayin da suke fuskantar wata duniya cike take maras gani.

Mutanen zamanin da da can sun samar da tatsuniyoyi tare. A cikin dogon tarihi, an yada su baka da baka, har zuwa lokacin da aka samar da kalmomi, sai an rubuta su a takardu. Abubuwan dake cikin tatsuniyoyin su kan bayyana tarihin zamanin da, wadanda suka hada da tatsuniyoyin bayyana asalin duniya, kamar “Pangu ya raba sama daga kasa”, da “Nvwa ta samar da bil’adam” da dai sauransu, da tatsuniyoyi dangane da gwagwarmaya tsakanin bil’adam da halittu, kamar “Houyi ya harbe rana 9”, da “Kuafu ya bi rana”, da “Jingwei ya yi kokarin binne teku” da dai sauransu, da tatsuniyoyin nuna babban yabo ga sadakar da kai, kamar “Shennong ya dandana magunguna”, da “Gun and Yu sun magance bala’in ambaliyar ruwa” da dai makamantansu.

Littafi mai lakabin Shanhaijing-Yinglong

Tatsuniya mai suna “Nvwa ta gyara sararin sama” na nufin cewa, a zamanin da da can, ba zato ba tsammani sararin sama ya fashe, inda aka samu wani babban rami. Daga bisani, an yi ambaliyar ruwa mai tsanani a kasa, tare da dabbobi da yawa. Bil’adam na fuskantar babbar matsala. A daidai wannan lokaci, mahaifiyar bil’adam Nvwa ta dauki wannan alhaki, ta tace duwatsu masu launuka biyar domin gyara sararin sama. Bayan haka, an sake shimfida zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasa, mutane kuma sun sake jin dadin zaman rayuwa.

Tatsuniya mai suna “Gun da Yu sun magance bala’in ambaliyar ruwa” na nufin cewa, wani waliyi mai suna Gun da dansa mai suna Yu sun daidaita matsalar ambaliyar ruwa, tare da ceton bil’adam. A zamanin da can, an yi ambaliyar ruwa mai tsanani, har duk kasa ta bace. Da ganin haka, waliyi Gun ya ceci kayan sarkin sararin sama mai suna Xirang, wato wani irin kasa dake iya girma da kansta, domin dakatar da tafiyar ambaliyar ruwa. Amma bai yi nasara ba ta wannan hanya. Bayan lamarin, sarkin sararin sama ya kashe shi. Sai bayan shekaru 3, Yu ya tsalle daga cikin Gun. Ya daukin alhaki na mahaifinsa, ya ci gaba da kula da harkokin yaki da ambaliyar ruwa. A maimakon hana tafiyar ruwan, Yu ya dauki matakin kafa hanyoyi ga ambaliyar ruwa. A cikin shekaru 8 da ya kula da wannan aiki, Yu ya taba isa gidansa har sau uku ba tare da shiga a cikin har sau daya ba. A karshe, Yu ya ci nasarar yaki da ambaliyar ruwa, wadda ta shiga teku yadda ya kamata.

Dutse mai zane a kansa na daular Han-Nvwa

Duk wadannan kyawawan tatsuniyoyi, sun bayyana burin mutanen zamanin da can na samun fahimta da cin nasarar yaki da bala’un halittu, da bayyana ra’ayoyin kakanin al’ummar kasar Sin masu ban girmamawa sosai na yin gwagwarmaya da halittu.

Wadannan kyawawan tatsuniyoyi sun yi babban tasiri ga bunkasuwar adabin kasar Sin, ma iya ce wannan ne asalin adabin kasar Sin. Daga bisani, shahararrun marubuta da yawa sun rubuta bayanai masu kyau sosai ta hanyar karbar abubuwa masu daraja da yawa daga cikinsu

Littafi mai suna Shijing

Littafi mai suna Shijing, babban littafi na farko ne dake tattara wakokin kasar Sin. Ya tara wakoki 305 da aka samar daga farkon daular Xizhou zuwa tsakiyar daular Chunqiu, gaba daya ya kai shekaru kimanin 500. An ce, jami’an gwamnatin daular Zhou su kan tara wakoki daga jama’a. Kuma a lokacin, an kafa wani tsari ga jami’ai da su bayar da wakoki ga sarki. Bayan da jami’ai suka tsara su, sai wadannan wakoki sun zama wannan littafi mai suna Shijing. An ce, duk wakokin dake cikin littafin, ana iya rera su.

Littafi mai suna Shijing

Da farko, an rada wa wannan littafi suna “Shi”, ko “Shi dari uku”. Daga bisani, Confucius ya dauke shi a matsayin littafin horo. Sai bayan daular Han, an canza sunansa zuwa “Shijing”.

Akwai abubuwa da yawa a cikin littafin Shijing. Mafi yawansu sun bayyana hakikanin zamantakewar al’umma a lokacin, musamman ma soyayya tsakanin maza da mata, da rayuwar aure. Bayan haka, wasu wakoki sun bayyana rayuwar ma’aikata, yayin da wasu suka bayyana gwagwarmayar fararen hula domin neman dadin zama, yayin da wasu suka yi Allah wadai da yake-yake, wadanda suka yi babbar illa ga rayuwar jama’a. Mafi yawansu suna da kalmomi 4 a cikin kowace jimla, wadanda suke da dadin ji sosai.

Alal misali,

Wannan yarinya dake daukar tsiro mai suna Xiao,

Da zarar ban ga ta ko kwana daya ba,

Sai na ji kaman watanni 9.

Wannan waka mai suna Caige na nufin begen wani namiji ga masoyiyarsa. Ma’anarta ita ce, wannan yarinya ta je daukar tsiro mai suna Ai, ko da yake ban ga ta kwana daya ba kawai, amma ya yi kaman shekaru uku gaba daya. Bisa wannan waka, an samu karin maganar “Ba a gamuwa da juna ko kwana daya ya yi kama da shekaru uku”.

Littafi mai suna Shijing, ba ma kawai wani madubin da za a yi amfani da shi wajen nazari kan zamantakewar al’ummar daular Zhou ba, har ma asalin tarihin wakokin kasar Sin, da na wakokin kasar baki daya. Babban sakamakon da aka samu a fannin tunani da fasahohi ya yi tasiri mai zurfi ga bunkasuwar wakoki a gaba.

Wani kashi dake cikin zanen daukar tsiro mai suna Wei

Wakar Chu Ci

Wakar Chu Ci, wani sabon salo da aka samu bayan littafain Shijing. An samar da ita a kasar Chu dake kudancin kasar Sin a kimanin karnin 4 kafin haihuwar annabi Isa. A yayin da aka samar da ita, an karbi abubuwan dake cikin wakoki da adabin jama’ar kasar Chu. A sakamakon haka, wakar Chu Ci na da alamar kasar Chu sosai.

Qu Yuan, babban wakilin marubuta wakokin Chu Ci. An haife shi a kasar Chu, wanda ya kasance marubuci mai son kasa kwarai da gaske da a kan nuna masa girmamawa. Yayin da ya tarar da cewa, kasar Chu za ta lalata, ya damu sosai tare da rubuta wakoki da yawa domin bayyana ra’ayinsa na son kasa. Daga bisani, ya je gudun hijira cikin dogon lokaci. A karshe dai, ya kashe kansa ta hanyar jefa cikin kogin Miluo. A sakamakon haka, duk lokacin ranar abincin Zongzi ta Sin, a kan dafa Zongzi① da gudanar da ayyukan gasar kwale-kwale masu sifar dabbar Dragon da dai sauransu domin tunawa da shi. Muhimman wakokin da ya rubuta sun hada da Lisao da Tianwen② da Jiuge③ da dai sauransu.

Wakar Lisao, wata wakar siyasa da aka rubuta domin bayyana ra’ayoyi mai kyau kwarai. Gaba daya ta kunshi jimloli sama da 370, da kalmomi sama da 2400, inda marubucinta ya bayyana abubuwan da suka abku a cikin rayuwarsa, da da’a, tare da bayyana kulawarsa ga makomar kasar Chu da niyyar da ya dora na tsayawa tsayin daka kan burinsa. A cikin wannan waka, ya yi amfani da dabbar Dragon, ya hau wata mota mai launuka iri-iri, ya kai ziyara a sararin sama tare da masu tsaro na waliyin duniyar wata da na iska da na rana baki daya, a kokarin cimma burinsa. Amma a karshe, an tilasta masa wajen tafi daga kasar Chu. Ra’ayin Qu Yuan na son kasa da tsayawa tsayin daka kan buri ya burge mutane zuriya bayan zuriya, tare da horar da su.

Ban da marubuci Qu Yuan, Song Yu da Tang Le su ma sun taba rubuta wakokin Chu Ci. A karshe, wakar Chu Ci ta kasance wakiliyar wakoki na wani wa’adin musamman na kasar Sin. A sakamakon haka, an kira ta wakar mai salon Sao.

Wakar Jiuge-Dodon dutse

A cikin wakar Chu Ci, an yi amfani da tatsuniya da yawa, wadda ta samu ci gaba bisa wakar Shijing mai jimloli hudu kawai. Ta kara abubuwan dake cikin wakar nan, tare da kara karfinta na bayyana abubuwa. Ta bayyana wani salon musamman na soyayya, tare da samar da wata sabuwar hanya ga samun bunkasuwar adabin kasar Sin.

Bayani

.Garin Quyuan

① Zongzi, wani irin abinci na kasar Sin, a kan dafa su ta hanyar ajiye shinkafa a cikin ganyayen gora ko ganyayen tsaure, daga bisani an dafa su a cikin dafaffun ruwa.

② A cikin wakar Tianwen, an fid da tambayoyi sama da 170 game da sararin sama ta hanyar amfani da salon waka

Chu Ci

③ Wakar Jiuge, jerin wakoki ne da Qu Yuan ya rubuta bisa tatsuniyoyin jama’ar kasar Chu, wadda ta hada da “Donghuang Taiyi”, “Yunzhongjun”, “Xiangjun”, “Xiangfuren” da dai sauransu.

 

Exit mobile version