Connect with us

Uncategorized

Waiwaye Game Da Kasar Misra Da Misarawa

Published

on

Egypt Ko Masar Suna ne da duniya ta san kasar da shi, sabanin yan kasar. An samo sunan na Egypt daga kalmar Girka (Greek) AEGYPTOS wadda shi kuma aka samo daga tsohuwar kalmar mutanen kasar (hut-ka-ptan) ko kuma gida na ainihi (House of essence [ka] of ptah).

Teku da kuma Hamada (sparsely populated desert) su su ka yiwa kasar iyaka da makwabtanta. Arewa da kasar akwai Tekun Bahar Rum (mediterranean sea),daga gabas akwai Jan Teku (red sea), yammacin hamada ce ta yi wa kasar ta Egypt iyaka daga Libya da kuma Afrika ta arewa, Hamadar Sinai daga Palasdina da Isra’ila daga tsakiya hamada ta raba ta da Sudan har ya zuwa siririn kogin Nile (nile riber).

A cikin tsaunuka da kogunan kasar akwai su kogin nile da suez canal, mahadin bahar rum da jan teku. Da kuma tsaunin catherine na sinai, mai girman taku 8,748 marabar kasar ta Egypt da Sinai (Sina’a).

A karshen shekara Alif dubu daya da dari tara da chasa’in da shida yawan mutanen kasar 65,200,000 wanda a ciki mutane  1,9000,000 na daune a kasashen waje na wani dan lokaci.

Ana kyautata zaton wasu ‘yan kasar a kasashen larabawa masu arzikin man fetur da kuma arewacin duniya gaba daya, kididdigen da aka yi a shekara ta alif dubu daya da dari tara da casa’in da shida(1996) an samu karin kashi 21.7(ashirin da daya da dingo bakwai) na mutanen kasar sabanin kididdigen(1986) alif dubu daya da dari tara da tamanin da shida. Yanayin girman mutanen kasar ta ragu daga kashi biyu da digo takwas(2.8) zuwa kashi  biyu da digo daya (2.1) tsakanin 1976 zuwa 1986.

Egypt na daya daga cikinal’ummar Larabawa kusan miliyan 250 Mazauna yankin Moroko da Oman. Yaren na Larabci ya na daya daga cikin harshen semetic, wadda ya samo asali daga harshen Afro-Asiatic ma su tushe daya da su harshen Berber, tsohon yaren Egypt, Chadic da kuma Cushitic. Egypt ta dama daya daga cikin kasashe ma’abota harshen Larabci sakamon zuwan Musulunci  a karni na 17 (17th century), duk da cewa kafin ya zama cikakken yaren kasar an dauki karnuka da yawa. Ba Egypt kadai ba har sauran kasashen da su ke yaren Larabci (kasashen Larabawa) yanayin harshen su ya banbanta da rubutaccen Al’kurani, akwai ‘yan banbamce-banbamcen kalmomi tsakanin su (mutanen ‘yan kasar) musamman tsakanin tsofin kasar da kuma matasa, amma hakan ba ya hana su fahimtar juna.

 

Abinci

A rayuwa abinci yana daya daga cikin muhimman al’amuran rayuwar al’umma, wuraren taro da sauran muhimman al’amuran rayuwar mutane kaf sai an sako shi. A wurin mutanen Egypt biredi shi ne muhimmin abincin kasar,a karkararsu mata ne su ke gasa biredi a cikin magashi na laka a gidajensu. A birane kuwa ana sayar da shi a shagunan gashi wato (bakeries)

Saboda muhimmancin biredi a wurin mutanen kasar Egypt ya sa gwamnatin kasar kayyade dai-dai yawan, nauyi da kuma girma na yadda za a sarrafa shi tare da ba da tallafi a kan sa. Akwai wani sanannen abincin da ke tashe a kasar ta masar wanda su ke yiwa lakabi da “koshari” ana  hada shi ne  da shinkafa, makaroni, da miyar tumatur tare da markadaddiyar albasa. Wadannan abinci ana hada su ne a gidaje da kuma shaguna ko tebura na abinci a cikin garin cairo gaba daya

Yanayin cin maiko da kuma abinci mai gina jiki ya dogara ne a kan yanayin aljihun mutanen (shi cin abinci mai kyau  alama ne na arziki) gidaje ma su yalwatar arziki su na cin abinci mai gina jikin da ake samu daga dabbobi kaman nama, kwai, kifi da dai sauran su. Musulmai ba sa cin naman alade, mutane ma su karamin karfi kuma su kan ci irin wadannan ne sau daya a sati wasu kuma a wata. Wuraren cin abinci su na nan a baje a kasar kama daga kan gidajen abinci, shaguna da kuma rumfuna.

Legumes (abinci dangin wake) shi aka fi sanin ‘yan kasar da shi sannan akwai wani nau’i na abinci da ya ke muhimmi ne ga mutane, wannan abinci ana hada shi ne da tsuntsaye marassa tashi wato da wake, gishiri, lemon tsami, da kuma mangyada sukan dafa shi ne a kan wuta dan kadan. Wannan abincin yawanci karya kumallo su ke yi da shi.

Egypt ta samu kafuwa a matsayin kasa lokacin da aka yi watsi da mulkin gargajiya a alif dubu daya da dari tara da hamsin da biyu(1952).

Jagorancin kasar ya koma ga zabebben shugaban kasa mai wa’adin mulki na shekaru shida. Shugaban ke zabar Firaminista da ministoci, sannan su kuma bangaren ‘yan majalisun dokoki ana zabarsu na iya wa’adin shekaru biyar.  Daga mazaba dari biyu da ashirin da biyu a fadin kasar wanda ake zabar mutum daya tal daga kowacce mazaba dan wakiltar ma’aikata, dan kasa da dai sauransu.  Bugu da kari shugaban kasa yakan iya zabar mutum goma wadanda ke iya wakiltar wata kungiya amma ba ta majalisa ba, wannan ya ba wa shugaban damar zabar wasu daga jam’iyyu marasa rinjaye. A ‘yan shekarun da su ka shude, wannan ya ba wa shugaban da ke ci yanzu dama dan zabar wasu daga jam’iyyu marasa rinjaye.

 

Auratayya:

Aure na daya daga cikin hukunci mai tsauri da mace ke yankewa, musamman wajen zaben mijin auren a ta su al’adar bayan iyayenta, da waliyyenta, ita kanta mace har da ita a cikin sha’anin auren haka shima namiji.

Dabara anan shine saboda ma’auratan su zama abu daya,wajen shekaru da kuma matsayin karatu al’adan zamani na kokarin maye gurbin al’adar su ta iyaye da kakanni musamman a cikin birane, amma auren zumunci na nan ana ci gaba da yi,  kashi talatin da tara na auren da ake yi na dumunci ne tunda zinace-zinace ya yi karanci a cikin al’ummar dole bukatar auren ya yi yawa, ya dama kusan kowa aure yake yi.

Shi bikin auren iri daya ne da yadda kowa yake yi, ma’auratan za su samar wa kansu muhallin zama, haka kuma za su tabbatar duk wani abubuwa na al’adar biki an yi shi. Mutane su na kashe kudi iya karfin su ko kuma fin haka a shagalin auren, wurin ma su wadata kuwa sai in da mai ya kare.Auren sama da mace daya a cikin musulmai ya yi karanci dan yawanci ba sa yi, bai fi kashi biyar na maza ke da mata sama da daya ba, yawanci mata daya su ke da yi,su kuwa mazaje masu mata biyu ko sama da haka za ka same su da gidaje biyu. Rabuwar aure yana da sauki duk da cewa ‘yan uwa na iya saka baki a cikin maganar, matattun aure sun yi yawa. Bayan rabuwar aure uwa na da ikon rike danta ne kawai lokacin yana karami da zaran ya girma kula da shi ya kan koma hannun mahaifinsa. Ba su damu da yawan mata ko mutuwan aure ba su kawai abun da su ka dauka mai muhimmanci shi ne asali, sunan dangi kadai su ke amfani da shi a gaban sunayen su, sabanin mutanen egypt a yandu da basu damu da sunan  dangi kamar da chan ba a yandu su na amfani da suna ne, sai sunan mahaifi, sai kuma na kaka kamar a misali Hassan Ali Abdallah.

Dan haka asalin mutum a wurin su shi ne sunan sa, sabanin kauyukan kasar da wadanda sunan kakanni ya dama wajibi akan kowa, musulmai na amfani da sunan musulunci kadan ke amfani da na kakanni, mabiya addinin kirista kuma su na amfani da sunan addini ko kuma na larabci a maimakon na addini, mata ma su na da sunan addini amma wasu lokutan su na amfani da sunan zamani ko kuma sunaye na kasashen waje, mata basa canja sunayensu bayan aure duk da su kan bar gidajensu su koma gidajen mazajen su ko kuma gidan iyayen mazajen.

Duk da a birane ma’auratan kan nemi sabon gida ne ba tare da sun koma gidan kowa ba, ko da ace ba su hada gida da kowa ba zumunci mai karfi ya na nan. A kan yi taron misali matan gida na da cikakken ikon bada umarni a cikin gida, gado kamar yadda musulunci ya tanadar dukiyar mamaci a kan raba a tsakanin magada, yaransa da kuma matan da ya bari, yara maza kan samu kason da yafi na yara mata don haka ko wani rabon gado dole sai an samu magaji namiji koda kuwa ya damo sai an bi kan dangi gaba daya.

Mutum ba shi da ikon bayar da abun da ya fi kashi daya daga uku na dukiyar sa ta wasiyya haka kuma ba shi da ikon fifita gadon wani da na shi akan wani,a takaice mutum badai iya bayar da wasiyyar dukiyar sa duwa ga wani yaro nashi guda daya ba amma dai iya bayar wa a sadaka ko kuma ya bayar wa mutanen sa ba yan’uwan sa ba ne.

 

Tarbiyya

Tarrbiyya da kuma karatun yaro a kasar Egypt shi ne mafificin albarkar da mutum zai samu, tarbiyayar yaran ya doru ne a kan iyayen su mata, yawancin matan musulmai da wanda ba musulmai ba na bin koyarwar Alkur’ani  wajen shayar da yaransu a shekara biyu, kakanni da sauran dangi na taka mihimmiyar rawa wajen tarbiyyan yara.

Sun fi fifita yara maza akan  yara mata duk da cewa a yarinta akan nuna musu  soyayya iri daya da kulawa, son samun koda namiji daya ana danganta shi da son samun magaji saboda a samu gadon mahaifi duwa da.

 

Karatu:

karatu na da matukar amfani a kasar ta Egypt mutane su na kashe kudi sosai a fannin ilimi, har mutanen da ba su da wadata sosai  na kokarin bawa yaransu ilimi gwargwadon iko, sun dauki ilimi musamman digirin jami’a abu mai amfani a rayuwar su, amma sai dai mutane da dama ba su da kudin da ya wuci matakin firamare dadin kuma yara masu kananun shekaru su kan yi aiki don tallafawa iyayensu.

 

Kiwon Lafiya:

Kiwon lafiya ya na dauki hankalin mutane da kuma gwamnatin kasar, akwai kyakyawar hanyar zuwa asibitin gwamnati a burane da kuma kauyukan kasar gaba daya, akwai kananun asibitoci a kowanne kauye masu kwararrun ma’aikata amma duk da haka mutane kan nemi zuwa asibitin kudi don neman lafiyarsu. Su kan hada maganin asibiti da kuma maganin gargajiya. Kamar a kauyuka akwai ungozoma a misali wacce ba a haihuwa da kuma radin suna kadai amfaninta ya ke ba,   har da shawarwari na neman lafiya ta kan ba wa mata.  Akwai sauran masu magunguna na gargajiya, kamar ma su duba da kuma ma su warkar da shaidanu, bikin zar na nuna alakar  mutanen kungiyar shaidanu da kuma mutanen da su ka shiga..

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: