Connect with us

TARIHI

Waiwaye Game Da Tarihin Kofofin Katsina

Published

on

Ganuwar Jihar Katsina kamar sauran ganuwowin kasar Hausa ne, don kuwa tana da dadadden tarihi wanda ya fara tun daga karni na 15. Amma kafin mu kai ga maganar wannan ganuwa, ya kyautu mu dan tabo tarihin yadda aka gina ta a wancan lokacin. Dalili kuwa, yin hakan zai yi mana jagora bisa ga batun ganuwar Katsina da tarihin da ke tattare da ginin nata.

Kamar yadda al’adunmu (1995) ta bayyana ta nuna cewa, shi ginin ganuwa alama ce ta kafuwar jama’a a wuri daya domin amfanin kowa da kowa. Dalili kuwa shi ne, ma fi yawan aikin ginin ganuwa aiki ne wanda aka yi da hannu da kuma karfin jiki na mutane. Haka kuma kayan da aka yi amfani da su wajen ginin duk an yi su ne da hannu. A nan za a iya cewa, girman ganuwa da tsayinta duk sun dogara ne ga irin yawan al’ummar da ke zaune a wuri da kuma irin karfin sarautar da Sarkin wurin ke da shi, ta yadda zai iya sanya talakawansa su hadu su yi aikin gayya.

 

  • Kofar Sauri Da Makwabtanta

Kofar Sauri, kofa ce da ke gabas maso arewa da birnin Katsina. A yamma da kofar, ta yi iyaka da Unguwar Rafukka, Nasarawa, Makera da Yammawa. Za mu yi bayanin kofar Sauri din, da kuma unguwannin da ke kusa da ita.

Akwai bayanai guda biyu game da asalin wannan kofa ta sauri, a wani bayanin, an ce, kofar Sauri, ta samo asalin ne daga Shugaban samari, wanda ake kira da Sarkin samari, sannan ya zauna a daidai kofar ta Sauri. Yau da gobe ta sanya aka fara takaita kalmar ‘Samari’ zuwa ‘Samri’, daga nan kuma ta koma ‘Sauri’ inda a karshe kuma ta koma kofar Sauri.

A wani bayanin kuma an nuna cewa, a lokacin mulkin Ummarun Dallaje ne (1807-1835) wani mayaki da ake kira Danbaskore ya kawo wa Katsina hari ta wannan bangare, amma sai ya iske duk kofofin garin a kulle. Sai Sarkin Sauri, wanda wani gari ne da ke can wajen Kaita ta yanzu, ya kawo wa Katsina gudunmawa ya fatattaki Danbaskore da mayakansa. Bayan ya kori maharan, sai Sauri ya sa aka fasa kofa ta cikin ganuwar, ya kutsa kai, ya shiga birnin, ya shaida wa Sarkin Katsina duk abin da ya faru. Jin dadin wanan aiki da Sauri ya yi, ya sa aka sanya wa wannan kofa sunansa, ma’ana kofar Sauri.

A nan za a iya cewa , ita wanan kofa bata kai sauran kofofin Katsina tsufa ba, domin kuwa an yi ta ne a Shekara ta 1807. Amma wasu masana Tarihi suna ganin cewa, akwai kofa tuntuni, kuma an gina ta ne a karni na 15 a daidai lokacin da aka gina sauran kofofin ganuwar ta Katsina. Kuma ta wannan kofa ce fataken da suka tawo daga Kasashen Larabawa da Agadas da Damagaran da Kaita da Shinkafi suke bi su shiga birnin Katsina. Haka nan sauran unguwanin da ke Yammawa da Makera da Nasarawa, dadaddun wurare ne wadanda tun lokacin kafuwar Katsina suna nan a inda suke a halin yanzu.

Bayani ya nuna cewa, saboda dinbin dukiyar da ke shigowa ta wannan kofa ne ‘yan fashi suka rika matsa wa fataken da ke shiga ta kofar. Ba a samu saukin haka ba sai da Sarkin Katsina na wancan lokacin ya hada kungiyar ‘yan sintiri na mayaka, wadanda suka rika gadin kofar.

Kofar Sauri ta kunshi jinsin mutane iri-iri. Akwai adi Habe, wadanda su ne ainihin mutanen farko da suke zaune a kusa da kofar Sauri, tun kafin wata al’umma ta zo wurin tare da Haben da suka iske. Su wadannan Buzaye, asalinsu daga Agadas ne, wadanda suka rika zuwa Katsina fatauci. Sun kasance, suna kawo kanwa da dabino da gishiri da kantu da sauransu, wasu kuma, suna kira. Wadannan mutanen ne ma tushen kafuwar unguwar Makera da ke Nasarawa Rafukka. In sun zo, suna yada zango a gidan Sarkin Zango da ke nan kofar Sauri. A hanjali suka gina rijiya da gidajen zama.

 

  • Kofar Guga Da Makwabtanta

Kofar Guga, kofa ce da ke yamma  maso arewacin birnin Katsina. Daga cikin kofar, ta yi makwabtaka da unguwar Sararin tsako da Sullubawa. A wajenta kuwa, ta yi makwabtaka da Tudun ‘Yan Lifidda da Masallacin Idi na Katsina. Za  mu yi bayanin kofar Guga  da kuma unguwannnin da ke makwabtaka da ita.

Kofar Guga na da sunaye iri uku: kofar Yamma, wadda aka sanya mata saboda kasancewar ta a Yammacin birni . Akwai sunan kofar Tsaro , saboda a da a nan ake ajiye mayaka masu tsaron kofar, koda za a kawo wa garin hari, amma sunan dai da aka fi sanin kofar da shi shi ne, kofar Guga . Ita wanan kalma ta Guga sunan matar Sarkin Gobir ce , Bawa Jan Gwarzo, wadda aka ce ta gudo ta zo Katsina , ta kuma shiga birnin na Katsina  ta wanan kofar,domin ta fallasa shirye-shiryen maigidanta ga Sarkin Katsina Muhammadu Jan Hazo (1740-1751).

Wanan fallasa asiri da Guga ta yi, ya taimaka wajen cin Gobirawa da yaki a kwafsawar da aka yi bayan zuwan nata . Don jin dadin wannan nasara ne, Sarkin Katsina Jan Hazo, ya sanya wa wannan kofa sunan matar, wato Guga. Kofar Guga na daya daga cikn kofofin da aka fara ginawa a farko-farkon karni na 15. Kofar ce ake bi a je Gobir wadda a yanzu ke kasar Sakkwato . Har ila yau , ta kofar ce ake bi zuwa Bugaje da Jibiya da Maradi.

 

  • Kofar Durbi Da Makwabtanta

An sanya wa wannan kofa sunan Durbi ne saboda wani Hakimi na Habe, mai suna Durbi, wanda shi ne Hakimin kasar Mani tun a wajen karni na 15. Ta wannan kofar ce yake fita zuwa Mani, ta nan ne kuma yake shiga idan ya dawo. Daga shi wannan Hakimi na Mani ne aka rika kiran shi da Durbi.

A wani bayanin kuma, an nuna cewa, wannan kofa mai suna Kofar Durbi, ta samo sunanta daga sarautar Durbi-Ta-kusheyi. To daga nan ne, sunan Durbi ya fara  a mulkin Katsina gaba daya, wanda kuma, ko da su Durbawar suka yi kaura, suka koma birnin Katsina, aka bar sarautar Durbi din da sunanta na asali, wato, maimakon Durbi sai ta zama Durbi Katsina. A yanzu duk wanda ke rike da sarautar Durbi, shi ne kuma Hakimin Mani. Tun daga Durbi Saddiku wanda aka yi a shekara ta 1810-1835, an kuma yi Durbi Fandiku (1836-1860) Durbi Gidado (1860-1883), Durbi Dikko (1891-1906), har dai ya zuwa yanzu din nan. Ta ita wannan kofar yake shiga in ya dawo kofar Durbi ta yi makwabtaka da unguwannin da ke cikin ta, kamar unguwar Filin Samji da Rimin Badawa. Daga wajen ta kuwa akwai kuma unguwar Turaka, wato Bariki ko G.R.a.

 

  • Kofar Kaura Da Makwabtanta

Wannan kofa ta Kaura, ta samu asali ne daga wani mutum da ake kira Kaura Gumari, wanda Habe ne, kuma mayaki. Ya zauna tare da iyalansa a Garama da ke nan kusa da kofar. Kamar yadda majiyarmu ta nuna, bayani ya nuna cewa, wasu daga cikin ‘yan’uwan wannan mutun sun yi kaura zuwa Tasawa wanda yanzu ke Kasar Nijar, wasu kuma suka yi kaura zuwa tsafe a inda suka kafa mulkinsu a can wuraren. An ce, Zuriyar wannan mutun ne ke mulkin Tasawa da Tsafe.

Amma , a wani bayanin an nuna cewa, kofar Kaura, ta sami sunanta ne a dalilin Kaura Abubakar, wanda ya yi yake-yake a lokacin mulkin Dallazawa saboda kwazon wannan jarumi ne aka ba shi mulkin kula da garin Rimi da ke gabacin Katsina. Ta wannan kofar ce, shi Kaura Abubakar ke bi ya fita zuwa Rimi ta nan ne kuma yake dawowa. Karewa da kaura, a nan kusa da kofar ce ya gina gidansa na kaura, wanda gidan har yanzu yana nan a matsayin gidan saukar duk kauran Katsina, Hakimin Rimi.

Kofar Kaura, tana daya daga cikin kofofin birnin Katsina da aka gina a karni na 15. A wajen kofar Kaura an sami kafuwar wani gari da ake kira Dandagoro wanda nisan shi da kofar bai wuce kilomita 3 zuwa 4 ba. A  cikin kofar kuwa, akwai unguwar Shararar Fayif.

 

  • Kofar Kwaya Da Makwabtanta

Wannan kofa ta kwaya ta samo asali ne daga wani Basaraken Habe mai suna Sarkin kwaya, wanda ke mulki a wani gari da ake kira kwaya, da ke kudu da birnin Katsina. Aikin wannan Basarake shi ne, sama wa Sarki hatsi, kamar su dawa da gero da sauransu, domin amfanin gidan Sarkin. An ce, ta ita wannan kofar ce Wali Jodoma, wanda Sarkin Katsina na lokacin ya kora, ya bi ya fita ya bar Katsina. Labarin ya nuna cewa, da shi wannan Waliyyin ya fita, sai ya juya baya ya tsine wa kofar ya ce, “ba za a yi wani abin kirki a kofar ba, sai bayan shekara dari biyar.” Ga yadda Katsinawa ke cewa, kusan kowace kofa ta sami ci gaba, gidaje sun isa kusa da su in ban kofar kwaya. To, amma yanzu din nan, da take ci gaba, shekaru dari biyar din ne suka cika. Ita ma wannan kofar, ana jin cewa a karni na 15 ne aka gina ta. Ita ce ake fita a je garuruwan Dutsinmma da Safana da Runka har zuwa Kankara.

Alal hakika, kofar Kwaya, a halin yanzu, ta wuce sauran kofofin ci gaba. Ta kofar ce, ake bi a je manyan-manyan Makarantun Boko na Katsina. Misali, a kudu da kofar Kwaya aka gina ‘Federal College of Education’, da Hassan Usman Katsina Polytechnic ‘ da Katsina Unibersity’ da Umaru Musa ‘Yar’adua Unibersity’ daga shekarar 1980 zuwa yanzu. Baya ga wadancan, ga babbar kasuwar Katsina ‘Katsina Central Market’ da babbar tashar, mai daukar fasinjoji zuwa kudancin Katsina zuwa Funtua, Kaduna, Lagos da sauransu, wadanda aka yi wajen shekarar 1989. Ga kuma sabon asibitin kashi da aka gina.

Kofar Kwaya ta yi makwabtaka da wasu unguwanni a cikinta da wajenta. A cikin kofar Kwaya akwai shararar Fayif wadda ta kafu ba-baya nan, da bai wuce shekaru 60 ba. A kusa da kofar daga ciki, akwai shaharariyar Kwalejin nan ta Arabiya wato ‘Arabic Teachers College’, wadda aka gina a shekara ta 1967 da kuma gidan hamshakin dan kasuwa, mashahuri, mai suna Dahiru Barau Mangal. A wajen kofar kwaya, akwai wata unguwa, wadda ita ma, ba ta wuce shekaru 60 da kafuwa ba. Wannan unguwar, ita ce sabuwar unguwa.

 

  • Kofar ‘Yandaka Da Makwabtanta

Kofar ‘Yandaka tsohuwar kofa ce da aka gina a karni na 15. Ta samo sunanta ne daga Basaraken Habe na garin ‘Yandaka da ke yammacin birnin Katsina. Ta wannan kofar ce ‘Yandaka ke bi idan zai fita zuwa ‘Yandaka, ta nan ne kuma yake shiga in ya dawo Kofar ‘Yandaka ta yi makwabtaka da Gafai daga arewa; Masanawa daga gabas, tare da Marinar Kadabo da ‘Yantaba, duk daga gabas din. A kudu kuwa, za a iya cewa, Kofar ta yi makwabtaka da rafindadi, mun dai riga mun yi bayanin Rafindadin Gafai da Masasanawa. Yanzu wadanda suka rage, ba mu ce komai a kansu ba, su ne Marinar Kadabo da “Yantaba. Dukkan wadannan unguwanni da muka ambata, suna cikin ganuwar garin na unguwar kofar “Yandaka. A wajen kofar, akwai wasu wurare masu muhimmanci da za mu yi magana a kansu, kamar garin babbar Ruga da Filin Folo na Katsina, wadanda duk suke a yamma da kofar ‘Yandakan.

 

  • Kofar Marusa Da Makwabtanta

An gina kofar Marusa a wajen karni na 15. Ana jin an gina ta ne a daidai lokacin da aka gina sauran ganuwowin Katsina, kuma ta sami sunanta ne daga wani Basarake na Habe da ke mulkin Dutsi, mai suna Marusa Usman. Ta wannan kofar ce Marusa din ke bi in zai tafi Dutsi, ta nan ne kuma yake shiga idan ya dawo. Daga nan ne aka sanya mata sunan Basaraken ta zama kofar Marusa Usman.

Kofar Marusa, ta yi makwabtaka da wasu unguwanni da ke cikin kofar da wadanda ke wajen ta. Akwai dai unguwar Kerau daga cikin ta wanda shekarunta ba su wuce 60 da kafuwa ba, koda yake, a da can, tun lokacin mulkin Habe har ya zuwa na Dallazawa, an yi wani wuri da ake kira unguwar Dantura, wadda a halin yanzu babu wannan unguwa saboda Kerau ta hade ta, ta koma cikin Kerau din.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: