Connect with us

TARIHI

Waiwaye Game Da Yadda Rikicin Maitatsine Ya Faru

Published

on

Bismillahi Rahamanir Rahim. A takaice yadda za mu rika kawo muku wannan labari na rikicin maitatsine, wanda za’a gabatar da shi a jaridar LEADERSHIP A Yau Juma’a.

Makasudin rikicin maitatsine ya faru ne a ranar 11/12/1980, wato kusan in ce ya faru ne a unguwar Malafa, Malafa unguwa ce daga gabas, ta yi iyaka da unguwar Fagge wacce take da mashahuran mutane masu Arziki. Malamai da ‘yankasuwa da sauransu, misali A bangaren masu Arziki akwai irinsu Alhaji Garba A.D. Inuwa, da Alhaji Sama’ila maiguza.

A bangaren Malamai kuma, akwai irinsu Malam Umar Sani Fagge, da Malam Haido da su Malam Muktar Atamma, wanda duk a yankin unguwar Fagge suke,  da sauran manyan mutane. Haka zalika, to rikicin ya faro ne a gabas da unguwar Fagge daga  bangaren kudu, yana da dangantaka da unguwar Kofar Wambai, wato K/Wambai.

Ita ce unguwar nan da ta shahara wurin sana’o’in gargajiya, kamar su Dukanci, Takalma da Jakankuna da Bel na d aurawa da sauran sana’oi iri-iri. Haka zalika, su ma na unguwar Fagge, suna da mashahuran mutane kamar irin su Bala Salisu da mashahuriyar kofar nan wanda aka fi sani da K/wambai, daga bangaren yamma unguwar malafa Wanda A nan ne gidan metatsine yake  ta yi iyaka da unguwar Koki, wato unguwar koki ita ce wadda wannan rikici na maitatsine ya fi shafa wadda ko da a unguwar Malafa inda gidan maitatsine yake ba’a samu rasa rayuka da kone-konen gidaje kamar yadda ya faru a unguwar Koki ba.

Ita unguwar Koki tana yamma da gidan maitatsine, a nan unguwar Malafa Alhaji Nasiru Ahali yake farkon zamansa a nan unguwar sai da maitatsine ya kama iyalansa da matansa su hudu (4) da ya’yansa guda goma shabiyu har ya yanka ya’yansa guda biyu, daga ciki kuma ya yi garkuwa da matansa da sauran ahalinsa. Haka zalika a dai wannan unguwa ta Koki, sai da maitatsine ya kama kannen Alhaji Nasiru Ahali irinsu Alhaji Salisu Ahali, sannan a wannan lokacin ya yanka babban d an Alhaji Salisu Ahali, wato umaru.

Bayan haka, ya kama Alhaji Yawale ya kuma kama iyalan Alhaji Yawale (17), inda ya yanka babban d an Alhaji Yawale, sannan yayanka shi bayan yayanka shi, ya samu iyalansa ya ce musu yau kun zama bayi na, na yanka mijinku, daga yau kun zama bayi na, saboda haka ko taso ku yi min godiya sakamakon yanka mijinku da na yi A kakaice shi ya d auki kansa ne a matsayin shi Annabi ne.

A takaice dai duk labarin zai zo muku ta bakin matan da kansu a nan gaba. Sannan a nan unguwa ta Koki wacce maitatsine ya fi yi wa illa, a nan gidan Alhaji Almu yake, wanda ya kama iyalansa, da babban d ansa mai suna Abubakar Yawale ya yanka shi. Sannan shi ma Alhaji Almun ya yanka shi, wanda duk labarin zai zo muku daga bakin wanda abin ya shafa. Bugu da kari, daga bayan unguwar ‘yan ‘awaki wato nan unguwar Malafa kenan, ita ce ta biyu wadda maitatsine ya yi wa illa, ita ma a cikinta akwai shahararren attajiri wato Alhaji Umaru Ta’ambo da sauran manyan mutane.

Maitatsine ya tayar da wannan fitina ne, sakamakon soyayya mai karfi da yake nuna wa d ansa Tijjani Kal’ana.

Dalilin da ya sa ake kiransa da suna Kal’ana shi ne, suna danganta metatsine da annabi kamar yadda ya umarce su, shi annabi ne, dalilin da ya sa suka yarda da annabtarsa, yana hawa kan buzu ya tashi ko ya doki hannayensa ya nuna musu daular duniya da ta lahira, nan Aljannace duk wanda ya bini zai shige ta.

Haka zalika, yana dukan hannayensa kud i su zubo kasa ya basu su je su kasha, to irin wad annan tsafe-tsafen da yake yi sai suka d auka gaske ne, har suka yi imani da cewa shi Malam Marwa maitatsine annabi ne, kuma a irin wannan tafiyar da yake yi yana da d ansa Tijjani da sauran ya’yansa guda hud u wanda ya haifi yara da yawa, amma dukkan su ba sa wuce shekara shida a duniya Allah yake d auke ransu, Tijjani shi ne d ansa d aya, don hakan yake matukar sonsa sosai don haka ba abinda  Kal’ana zai nema ya rasa, kud i ne ko suttura, sai wadda ya ga dama zai sa.

Hakan ta sa yaron ya fara lalacewa, shi ne bariki shaye-shayen giya nema mata da sauran kayan maye iri-iri. Maitatsine ya sangarta kal’ana, har ta kai ta kawo duk d an da aka sayawa keke sai Tijjani ya je ya samu babansa maitatsine ya ce an saya wa wane keke shi kuma maitatsine sai ya ce, ni kuma gobe babur zan saya maka, kuma ya saya masa babura iri-iri saboda gata da izzar kudi.

To ana wannan yanayi ne wata rana ya d ebi abokansa, suka tafi yawon barikinsu da suka saba, sai suka tsokani wani kurma wanda aka fi sani da suna Sa’idu, sai wannan kurma ya buga masa wuka a wuya, ganin haka suka d auko shi suka kawo shi gida Maitatsine ya ganshi hankalinsa ya tashi ya ce a kai shi asibitin Murtala. Bayan an kai shi bai jima ba Allah ya d au ransa.

Tofa mutuwar Tijjani Kal’ana sai ta tunzura maitatsine ya ce, duk wanda yake wannan yanki na Malafa, Koki, Fagge, K/Wambai, Dukawa, sai ya d au fansar d ansa a kansu, sai ya dandanawa kowa d acin mutuwa.

Tofa yana wannan shirin afka wa al’umar unguwa, sai ya je wa’azi unguwar shahuci kusa da gidan Alhaji Ado D andawaki da tawaga mai yawa, da suka kai mutum (2000) a bayansa, to ganin haka sai jama’a suka tsorata suka sanar da ‘yan sanda, bayan ‘yansanda sun zo ne sai suka ga abin ya fi karfin su sai suka fara buga musu barkonon tsohuwa, to fa daga nan ne a kai karan batta su kai kan ‘yansanda

akwai wani D.P.O na Kwalli a wancan lokacin, ana kiransa Muhammad maikifa, wanda suka kona motarsa da ta wani Sufeton ‘yansanda ana ce masa Bukar Karim mutumin Lau a garin Jalingo. Sannan suka kona ‘yansanda guda hudu hud u, wanda bayan sun yi wannan batakashi ne suka dawo gida, suka biyo ta koki zuwa nan Malafa sai suka afkawa al’ummar unguwar, duk wanda suka gani sai sun sara ko su kashe. Daga baya sai suka kewaye unguwar duka, babu mai fita babu mai shiga. Suka zuba dakarunsu ko’ina. Za mu cigaba mako mai zuwa idan Allah ya kai mu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: