Kusan da yawan lokuta na sha tambayar kaina shin menene makomar MATASA a siyasar kasar nan? Gudummawar da MATASA suke bayarwa a kasar nan ba kadan ba ce. Tun daga kan lokacin yakin neman zabe, zuwa lokacin kada kuri’a, har lokacin da za’a kafa Gwamnati da gudummawar matasan ake cimma dukkan wannan nasarorin, to amma shin ‘yan siyasar kuwa suna biyan dukkanin wahalar matasan da romon dimokradiya?
Shin matasa nawa ‘yan siyasa suka dauki nauyin karatun su, matasa nawa ne ‘yan siyasar suka taba bawa jarin kasuwa, kuma ‘yan siyasa nawa ne suka dauki matasan suka raba musu mukamai bayan sun samu nasara? Dukkanin wannan tambayoyin da nike yi wa kaina, idan na yi bincike sai inga sabanin abinda na yi tunani. Sai dana lissafa ‘yan majalisun jiha dana tarayya akalla sun fi a kirga, dukkan su babu wanda ya dauki koda mai bashi shawara guda daya daga cikin matasan da suka dinga take masa baya lokacin yakin neman zabe.
Nasha samun sakonni daga mutane da yawa akan in ja hankalin ‘yan siyasa da suke amfani da MATASA lokacin biyan bukatarsu, amma bayan kwalliya ta biya kudin sabulu, shike nan sun manta da MATASAn da suka yi musu dukkanin wahala, ba zaku kuma ganin su ba har sai lokacin da wani zaben ya taho.
Duk lokacin da zabe ya taho, zaka ga dan siyasa ya tara rundunar MATASA wadanda za su dinga taya shi yawon neman zabe, lungu da sako, birni da kauye, a wannan lokacin zai nuna musu tsantsar soyayya da kulawa, ba don komai ba saboda yana bukatarsu a wannan lokaci. Babban abun takaicin shi ne yadda zaka ga ‘yan siyasar suna rabawa matasan kayan maye da makamai, wannan kusan ya riga ya zama ruwan dare a gurin ‘yan siyasa, kuma ba zaka taba ganin ‘yayansu a cikin ‘yan barandar siyasar tasu ba, ni babban damuwata shi ne su kansu matasan sun riga sun wulakanta kansu, basu da wani amfani ga ‘yan siyasar daya wuce yawon siyasa.
Abin tambayar a nan shi ne, shin wane sakamako suke yi musu ta ‘bangaren cigaban su, wane irin temako suke musu a bangaren karatun su, wane taimako suke musu ta bangaren kasuwancin su? Wannan sune babban abin da matasan ya kamata su dinga tunawa kafin amincewa da kowane dan siyasa. Kai ni ban ma yadda da cewar MATASA za su zama tamkar bayin ‘yan siyasa ba, ya kamata tuni ace an tsabtace siyasar kasar mu daga siyasar banga, tuni yakamata ace an canza tsarin siyasar kasar nan wacce da yawan lokuta take janyo asarar rayuka da kara ingiza MATASA da shan kayan maye. A kasashen da akaci gaba, tuni ‘yan siyasa sun yi nisa wajen amfani da iyalansu kawai lokacin yakin neman zabe, sannan nasan kasashe da dama irinsu Faransa, Rasha, Scotland da sauransu da suka sanya doka me tsanani akan duk matasan da aka kama sun haddasa rigima tsakanin su lokacin yakin neman zabe. Sannan babu wani dan siyasa da zai kaddamar da yakin neman zabensa ba tare da zama da kungiyoyin MATASA ba, dole ne sai sun kaddamar da alkawarurruka da dama da zasu yiwa matasan bayan darewar su kan mulki, sannan duk dan siyasan daya kasa cika alkawarurrukan da ya yi musu, tabbas ba za su kuma kada masa kuri’a ya koma kan mulki ba, wanda hakan ya saba wa siyasar kasar mu.
Miliyoyin kasar nan da dama karatu ya gagaresu saboda rashin samun me daukar nauyin su, da yawan su kuma sunada iyayen gida a siyasa, amma abun bakin ciki babu wanda zai iya biya wa mutum biyu daga cikin su kudin makaranta, babu wanda zai iya siyan jarrabawar shiga jami’a (Jamb) ya rabawa yaran unguwar su wadanda suka yi layi kato bayan kato suka zabe shi, ballantana kuma su bugi kirji su bawa wasun su jari sakamakon irin kokarin da suka yi musu lokacin zabe. Wannan abun kullum yana damuna idan naga MATASA suna yawo kwararo-kwararo su ba sana’a ba, kuma ba makaranta ba, amma kuma idan lokacin zabe yazo, zaka ga sune na gaba-gaba agurin ‘yan siyasa.
Idan har mu MATASA zamu yi wa kanmu fada, muyi wa kowane dan siyasa bara’a a kan wannan mummunan sakamakon da suke mana duk da irin dawainiyar da muke dasu a siyasar su, ya kamata ace kowane dan siyasa kafin yasamu sahhalewar jam’iyyar sa, to sai ya zauna da kungiyoyin matasa, da kuma alkawarurrukan da zai yi musu, wanda idan har ya kasa cikasu, to tamkar ya kifar wa da kansa Gwamnati ne a zabe me zuwa, idan har zamu dauki wannan matakin, to na tabbata matasa zamu samu sakamako me kyau a siyasar kasar nan.