Wato kamar yadda na fara sharhin rikita-rikitar jam’iyyar PDP a satukan daya gabata, wannan satin zamu yi waiwaye ne a kan ruɗanin dake cikin babban zaɓe me zuwa na 2023. Mu ajiye nuna wariyar jam’iyya a gefe, mu kalli irin abinda ka iya zuwa ya dawo a zaɓen. Bisa ga dukkan alamu ZAƁEN 2023 zai fi na 2019 zafi da rikita tunani, musamman saboda wasu dalilai da dama da hasashena ya fara hasasomin. Mu tattauna ɗaya bayan ɗaya mu gani;
1- Jam’iyyar adawa ta PDP tana ganin ta gaji da azumin rashin mulki tsahon shekaru takwas, kuma a shirye suke yanzu suyi duk abin da zasu iya don ganin sun kawar da jam’iyyar APC daga kan mulki. Duk da cewa akwai rikice-rikice cikin jam’iyyar, amma wannan ba wani sabon abu bane ga jam’iyyun siyasa, amma na tabbata shirin da suke yafi na kowane lokaci ƙarfi don ganin ta kowane hali sun amshi kuskuren su, kuma sunyi alkawarin canzawa.
2- Kudancin ƙasar nan a yanzu suma suna ganin cewar lokaci yayi daya kamata mulki yadawo hannun su, musamman ƴan jam’iyyar APC (Yarabawa), saboda Shugaba Buhari ya cinye shekaru takwas ɗinsa kamar yadda dattijan jam’iyyar sukaga cewar mulkin yazama yana juyawa bayan kowace shekaru takwas. Amma bisa ga dukkan alamu, akwai yiwuwar wannan tattaunawa ta tashi a tutar babu, kamar yadda yafaru a zaɓen 2015 a jam’iyyar PDP, inda manyan jam’iyyar suke ƙeƙashe idanun su cewar se Mai Malafa yakoma kan mulki, duk da cewa Marigayi Umaru ƴar’aduwa bai cinye zango na farko ba ya kwanta dama.
3- Abu na uku da nike gani shine yadda kasuwar ƙabilanci ta samu gurin zama da nuna ɓangaranci a siyasar ƙasar nan, hakan yana temakawa wajen kowane yanki a zaɓen 2023 yayi ƙoƙarin yankin sa shine a sahun gaba wajen manyan muƙamai, musamman kujerar shugaban ƙasa, wannan zata ƙara assasa gasa, rikici da ruɗani ganin kowane ƙabila ya samu wannan kujerar musamman daga jam’iyyar APC.
4- Akwai alamun jam’iyyun mu guda biyu APC da PDP sunfi karkata tunanin su da kawo ɗan takarar Shugaban ƙasa daga arewacin ƙasar kamar yadda akayi a 2019. Hakan zai sanya jihohi 19 da babban birnin tarayya Habuja su zama yanki mafi hatsari a wannan zaɓen. Domin kaso kusan 70 Musulmai ne kuma Hausa/Fulani ne, don haka rikicin tsakanin su ne, kuma kowa a shirye yake yayi duk abinda zaiyi don ganin ya kada abokin karawarsa.
5- Akwai dubunnan al’umma da suka dawo daga rakiyar jam’iyyar APC, bisa hujjar cewa CANJI da GYARAN da suka kasance taken ta, hakan bai cimma wani ɗa me ido ba, kuma wasun su suna kallon cewa babu wani abu da PDP zata iya cimmawa koda an dawo da ita kan mulki. Wannan zata iya sanyawa a kawo wata sabuwar jam’iyyar da zata iya haɗa kafaɗa-da-kafaɗa da waɗancan jam’iyyun masu ƙarfi. Akwai yiwuwar akawo jam’iyyar PRP kuma akawo mata fitaccen ɗan takara daga arewa, wanda hakan babban cikas ne ga jam’iyyun APC da PDP, kuma cigaba ga mutanen da sukai hijira daga can.
6- Yadda talakawa suka ilmantu da zaɓukan ƙasar nan musamman na 2019, miliyoyin al’umma sunyi alkawarin bazasu maimaita kuskuren da suka yi a baya ba. Yanzu suna ganin babu bindiga babu harsashi, babu daɗin baki babu maguɗi, babu re-run ballantana a zanca ra’ayin su, don haka sun shirya ƙwatowa kansu hakki, wanda hakan kuma ƙarara yaƙi ne da ƴan siyasar ƙasar nan.
8- Na ƙarshe shine yadda wasu jigajigan jam’iyyun adawa da me mulki da suka rasa kujera a zaɓen 2019 ko kuma a gaban kuliya manta sabo, zasu dawo da duk ƙarfin su ganin sun koma kan kujerun su. Yayin da a wannan lokacin ne kasuwar canjin jam’iyyun siyasa zata fara cin kasuwar ta.
Wannan kusan shine hasashen abinda zai faru a babban zaɓe na 2023 bayan Shugaba Buhari ya lamushe shekaru takwas akan mulki. Lokaci ne kawai zai gaskata hasashena ko ya ƙaryatani.
Ina amfani da wannan dama in mika saƙon godiya ta ga ɗaruruwan mutanen dake turomin saƙon godiya ta akwatin wayata da adireshin mail ɗina, musamman masu ƙara sharhi akan abinda wannan fili ya tattauna. Allah ya bar zumunci ya barmu tare. In Sha Allahu kamar yadda kuka nema zamu samu sati guda da zamu buga saƙonnin ku idan mun bayyana makalar da zamuji ra’ayoyin ku. Ya ƙara ɗaukaka jaridar mu me fitowa kullum (Leadership A Yau.)