Kwamared Sanusi Mailafiya" />

Waiwaye Kan ‘Yancin Mata A Kasar Hausa

Yau maudu’in mu na wannan satin zai yi tsokaci ne tare da tattaunawa akan ‘YANCIN MATA, musazmman saboda ranar tunawa da mata data gabata satin daya wuce. Ɗaya daga cikin ranakun da Majalisar Dinkin Duniya ta futar a shekarar 1977 domin keƊeta a matsayin ranar mataye ta duniya, itace 8 ga watan kowane Maris.

‘Ɗar Rajin kare hakkin mata Theresa Markiel a tarihance kusan ita ce ta fara kirkiro wannan rana domin tunawa da irin gudummawar mata, da kuma jajantawa sauran mataye da aka dannewa hakkokinsu musamman waƊanda suka fuskanci matsalar FYADE.

A irin wannan rana ana tunawa da manyan mata Ɗan gwagwarmaya da suka rasa rayukansu irinsu Emily Dabison yar kasar Ingila, Emilson Manyoma yar kasar Colombia, Michaela Garcia ‘yar kasar Argentina da sauran su, ana tuna irin gudummawar da suka bayar wajen irin gudummawar da suka bayar a gwagwarmayar su, da kuma yadda suka bugi kirji cewar lalle mata ma za su iya.

A Nijeriya dole mu tuna da irin gudummawar irin su Funmilayo Ransome Kuti, Magaret Ekpo, Elizabeth Adekogbe da sauran su, waƊanda suka bada mahimmiyar gudummawa da jajircewa a gwagwarmayar Kasar nan. Ni babban abinda na dauka Ɗancin mata, ba wai magana akan cewa dole mace sai ta mulki kasa ba, ko kuma mu bude idanu gobe ace mace ce ke Shugabantar Nijeriya, ba kuma ina magana bane akan cewa dole se an samar da daidaito tsakanin jinsunan guda biyu.

Wannan itace akidar da mutane ke ganin taci karo da Addini da kuma al’adun bahaushe. Kafin mu kai ga daukar abun ta fuskar Addini ko zamantakewa mu dubi shin wane Ɗanci mata ke bukata, kuma wane irin cin kashin kaji suke fuskanta a yanzu.

Idan muka Ɗauki masu yakin neman cewa mata dole sai an dama dasu ko gogayya dasu a kowace iriyar mu’amala (Liberation of women), ko kuma masu kallon baiken Ɗan rajin kare hakkokin mata (feminists) zamu ga cewa sunada iya dogaron su, da kuma abubuwan da suka sanya sune dokokin da zasu ginu akai (cardinal principles), sai kuma muyi daidaito da irin yadda yanzu muke kallon Ɗancin da mata suke akai.

Yanzu kawai mu Ɗauki fyade, kowa yasani babu wani Addini da bai daukeshi (rape) a matsayin laifi ba, musamman akan jinsin mata, zamu ga cewar mafiya yawan mutanen dake hakilo akan hukunta masu aikata laifi, anfi kallon su da cewa yan rajin kare hakkin mata ne, ko kuma wadanda ake ganin sunada irin wannan akidar (Feminism). To amma kuma babu me musanta cewar miliyoyin mata ne ke samun kansu cikin wannan ibtila’in, kuma zaiyi wahala kaji ance yau ga wani da ake zargi kuma an kamashi da laifin aikata fyade dumu-dumu an hukunta shi.

Kuma mafiya yawan yaran dake samun kansu cikin wannan ibtila’in zakaga yaran talakawane, wadanda basuda karfin ja da wanda ya aikata wannan laifin a gaban kuliya manta sabo. Sannan babu wanda yake tunanin irin halin da irin wadannan yaran suke afkawa sakamakon wannan fyaden da aka aikata musu.

A Kano kawai nasan cewa da yawan Kotunan dake kardar irin wannan laifin, har sun gaji da kawo masu laifukan aikata fyaden, babban abin damuwar ma shine yadda Gwamnati bata maida hankali akan ganin lalle an hukunta wanda ya aikata wannan laifin.

Kuma fyade yana daya daga cikin manyan laifuffuka bisa kundin kasa (Capital offence), amma meyasa daga kan masu shari’a, zuwa kan jami’an Gwamnati da tabbatar da cewar anyi shari’ar gaskiya basa maida hankali wajen hukunta wanda aka samu da aikata wannan laifin, wanda hakan zai zama izina ga sauran masu aikata irin wannan laifin.

Da yawan matan da suka tsinci kansu an aikata musu fyade, wasun su na samun matsalar tunani da kwakwalwa, likitoci da dama sun tabbatar da cewa wadanda suke yawaita tunanin wannan fyaden da aka musu, suna iya samun ciwon hauka, saboda abune da yake tada tunanin su, sai kuma ya hadu da bakin ciki da jimami. Da yawan su kuma suna kasa shiga al’uma, saboda suna ganin kowa yana kallon su da wannan fyaden, kowa tamkar yasan abinda ya samesu, wanda da dama daga cikin su, suna rasa masu auren su, saboda kawai an taƊa aikata musu fyade, wasu ma da gangan suke kasayin aure saboda suna ganin babu namijin da zai so su da gaskiya, saboda kawai anyi musu fyade.

A gurin maza da yawa duk macen data rasa budurcinta, to kamar ta rasa wata martaba ta ‘ya mace ne, koda kuwa fyade akayi mata wanda kowa yasan ba da son ranta akayi mata haka ba. Irin wadannan halayen da ake nunawa wanda aka yiwa fyade yana dakile musu sha’awar aure da kuma tunanin samun soyayya ta asali, wasun su kuma gori kadai ya isa ya hanasu kwanciyar hankali, tamkar cewa da yardar su akayi musu.

Idan muka koma asalin gundarin zancen mu na dancin mata, zamu ga cewa ana tauyewa mata da yawa dancin su na rike budurcin su har dakunan auren su, an samu wasu marasa tausayi sunyi musu fyade, madadin al’umar su da kuma Gwamnati su bugi kirji wajen kwato musu dancin su, sai hakan yazama babban aiki, wanda mutanen da kadai suke iya daga muryoyin su akan wannan batu, Shine jinsun su na mata wanda al’uma take kallo a matsayin masu akidar nemawa mata daidaito da maza. Zanci gaba

Exit mobile version