Wato akwai wata ƴar manuniya a siyasance dana daɗe ina ƙoƙarin fuskantar da wasu, amma wataƙila bayan an bayyana sakamakon zaɓukan waɗannan jihohin za su yadda dani. Amma babbar matashiyar da zan yi anan shi ne, jam’iyyar PDP a yanzu haka tana ƙokarin duk yadda za ta yi ta kare kambun ta a jihar Bayelsa, idan har kuma tayi tunanin cewar dole sai ta samu Bayelsa da Kogi, to za ta yi abinda hausawa ke cewa ɓatan-ɓaka tantan. Itama jam’iyya me mulki (APC) tafi bada ƙarfin ta a jihar Kogi, domin kuwa idan ta dage sai ta kwace duka jihohi biyun, to tabbas itama zata kwata abinda ake cewa two zero (2-0).
Nasan a dede yanzu da kuke karanta wannan sharhin, ba’a saki sakamakon zaɓukan da suka gudana jiya a jihohin Bayelsa da Kogi ba. Ba zaɓen ne Ƴar manuniya taba, a’ah, yanayin da aka sanya jihohin kafin gabatar da zaɓen, inda har aka ƙona sakatariya guda ta jam’iyyar SDP, bayan korafin da ‘yar takarar Natasha tayi cewar ana barazana da rayuwar ta. Banda kuma harin da aka kaiwa Shugaban hukumar zaɓen da sauran jami’an yan sanda gabanin zaɓen. Ire-iren wadannan tashin hankula suna janyo tsoro da fargaba matuƙa a lokutan zaɓe, har wasu ma kan ce bazasu je gurin zaɓen ba domin gudun abinda ka iya faruwa. Wannan kenan.
Yanzu mu dubi gundarin zaɓen. A fili take kuma a zahiri, talakawa ko kuma ince masu zaɓe basu fiya damuwa da cancantar ɗan takara ba, tuni an mayar da siyasa Yanki, ƙabilanci da kuma Addini. Tuni mun mayar da jam’iyya me mulki, jam’iyyar Arewa, yayin da kuma muka ɗauki jam’iyyar adawa kacokan mukace ta kudu ce. Wannan kuma shine ummul aba’isin da idan ba’a kawar da hakan ba, zai kuma janyo mana koma baya a Gwamnatocin mu. Dalili kuwa kowace jam’iyyar tana iyakacin ƙoƙarin tane taga ta cinye jihar ta bisa ƙarfin jam’iyyar da take dashi a jihar. Misali, yanzu jihar Bayelsa da kowa yasan jihar PDP, to ta kowane hali burin su suga sunci zaɓen su, koda ace zasu rasa jihar Kogi, kamar yadda na fa’da a sama, haka suma jam’iyyar APC zasuyi a jihar Kogi.
Yankin Bayelsa kowa yasan yanki ne daga kudancin ƙasar nan, kuma jiha ce ta tsohon Shugaban ƙasa Mai Malafa, bana tunanin al’ummar jihar zasu dubi cancantar ɗan takarar jam’iyyar APC a Misali, su kasa bawa na jam’iyyar PDP kuri’a, sabosa jihar ta PDP ce. Haka kuma bana tunanin duk rashin cancantar ɗan takarar PDPn, zasuyi wancakali da hakan su zabi jam’iyyar APC. Haka itama jihar Kogi da take tsakiyar arewa, bana tunanin sun fara tunanin meye makomar su idan Yahaya Bello ya koma, kawai abinda suka damu shine, bazamu bawa jam’iyyar PDP dama har ta mulkemu ba. Duk da rikita-rikitar ma’aikatan jihar da Gwamnan nasu, da kuma masu adawa da Gwamnatin cewar batayi abinda ya kamata a kuma zabar Gwamnan nasu ba. Wanda har hakan yasa iyayen jam’iyyar suka tsuguna gwuiwoyinsu a kasa suna nema masa afuwar mutanen jihar, musamman ma ma’aikata da akace ya dauki tsahon lokaci batare da basu haƙƙoƙin su ba.
Da yawan lokuta masu mulki suna toshe kunnuwan su, kuma su shafawa idanuwan su toka lokacin da suke kan mulki. Basu ganin mutuncin kowa ballantana ya basu shawara. Misali, kowa yasan Gwamna Elrufa’i yana aiki matuƙa a jihar sa, kuma shine na farko daya fara biyan mafi ƙarancin albashi a cikin Gwamnonin ƙasar nan, amma shi Gwamnan jihar Kogi kowa yasan yanada matsala da ma’aikatan jihar, kamata yayi ace tun kafin irin wannan lokacin, Gwamnonin APC da sauran masu ruwa da tsaki sun bashi shawara in har suna san su kuma samun jihar, ba sai aski ya kusa zuwa gaban goshi, suzo suna afi ga TALAKAWA su kuma zaɓen saba, wannan shine kuskuren da mafiya yawan Shugabannni suke yi a lokacin mulkin su na farko, sai lokacin kuma neman kuri’a yayi, suzo suna nuna kuskuren su ko kuma suna kawo wasu ayyukan daya kamata ace tun kafin wannan lokacin sun yi.
Dole ne Shugabanni suyi karatun ta nutsu. Su sani cewar mulki, amana ce garesu. Walau Kirista kake ko Musulmi, to zaka tsaya gaban Ubangiji domin ka fa’di yadda ka tafiyar da mulkin ka, da kuma yadda ka kashe kwandala da sisi na TALAKAWA.
A yanzu hasashena shine kawai kowace jiha zatayi kokarin ta riƙe mutuncin jihar ta. APC zata zauna a jihar Kogi, yayin da PDP zata zauna a jiharta ta Bayelsa.