Dandalin Ishak Idris Gulbi">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home Waiwayen Kanun Labarai

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Lahadi 10 Zuwa 13 Ga Jimada Sani 1442, Bayan Hijira

by Dandalin Ishak Idris Gulbi
January 29, 2021
in Waiwayen Kanun Labarai
5 min read
Waiwayen Kanun Labaru: Daga Lahadi 10 Zuwa 13 Ga Jimada Sani 1442, Bayan Hijira
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Lahadi

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya halarci wani taro na kungiyar raya tattalin arzikin Afirka ECOWAS ta bidiyo/intanet, har sun tattauna a kan kwaronabairos.
Majalisar Dokoki Ta Tarayya ta dage ranar da ta yi niyyar komawa zaman majalisar.
Gwamnan jihar Kabbi zai taimaka wa talakawan jihar su dubu ashirin da biyu da fulotai don gina gidaje na kashin kansu.
Kidinafas da makasa a jihar Kaduna, sun ci gaba da kashe na kashewa a wasu sassan jihar musamman yankin karamar hukumar Giwa.
Gwamnatin jihar Kaduna ta kori wasu malamai su sittin da biyar da aka dauka ta bayan gida a karamar hukumar Sanga, su ma jami’an da ke da hannu a daukar an sallame su.
Jama’a na ci gaba da korafi a kan dandana kudarsu da suke yi wajen neman lambar shaidar dan kasa.
Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.
Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar ta Kudan, Jaja, da wa’adinsa ke shirin karewa, ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawarin zai gyara musu a lokacin yakin neman zabe.

samndaads

Litinin
Gwamnatin jihar Kaduna ta amince manyan makarantunta na jiha su koma makaranta yau Litinin 25 ga wannan wata. Saura makarantunta na sakandare da na firamare da na naziri, nata da na masu zaman kansu, a ji ranar da su ma za su koma.
A ranar Litinin shugabannin kungiyar Miyetti Allah, suka gana da gwamnonin jihohin Kudu Maso Yammacin kasar nan, biyo bayan karewar wa’adin da gwamnan jihar Ondo ya ba filani makiyaya, su fice daga dazukan kiwo na jihar.
Gwamnatin jihar Oyo da ‘yan sanda, sun nemi yarbawa da fulani da suka yi hatsaniya a al’umar Igangan, su hadu a shalkwatar ‘yan sanda ta jihar don gano bakin zaren yadda za su zauna lafiya.
Wasu barayin shanu su fiye da hamsin, sun kashe mutum biyar a karamar hukumar Pakoro ta jihar Neja, suka sace shanu fiye da dubu daya.
Wasu makasa sun kashe shugaban karamar hukumar Ardo-Kola ta jihar Taraba, Salihu Dogo, tare da wani dan uwansa, sai dai ‘yan sanda sun kama mutum biyu da suke zargin suna da hannu a kisan.
Sojoji na sama da kasa, sun kashe wasu mahara a babura, a yankin karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Mutane goma sha biyar suka rasu sakamakon wani hadarin mota a hanyar Kaduna zuwa Abuja.
Ana ci gaba da damfarar masu neman aikin gwamnati a Abuja, daga naira miliyan daya, zuwa miliyan biyu.
Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.
Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya dauki alkawarin gyara musu a lokacin yakin neman zabe.
Af!
Waiwaye Adon Tafiya:Rubutun Da Na Yi Ranar 24/1/2015. Yau shekara shida daidai:
“Ina nan ina ta juyayin shawarar da Kanar Dasuki ya bayar da a dage zabe zuwa nan gaba, da kuma batun da ya yi cewa yawancin sojojin Nijeriya da ake da su a yanzun ragwaye ne da suka shiga aikin soja saboda rashin aiki yi. Ni kuma sai ina ganin masu horas da soja na yanzun da sauran shugabanni soja na yanzun har da Manyan hafsoshin sojan Nijeriya da shugaban kasa kansa har da Kanar Dasuki su ne manyan ragwayen. Su bai wa Buhari su ga wanda ba rago ba. Namiji mijin maza ba mijin ‘yar lukuta ba”

 

Laraba
Babban labarin da ya auku ranar Talata idan ka sayi jaridu, shi ne kan gaba, shi ne na sauya manyan hafsoshin tsaron kasar nan, da maye gurbinsu da sabbi, da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi. Sabbin da ya nada su ne Manjo Janar Leo Irabor, babban hafsan tsaro, sai Manjo Janar I. Attahiru, babban hafsan hafsoshin mayakan kasa, sai Riyal Adimiral A.Z.Gambo babban hafsan hafsoshin mayakan ruwa, sai Iya Bayis Mashal I.O.Amao babban hafsan hafsoshin mayakan sama na kasar nan. An dade, kama daga ‘yan majalisar dokoki na tarayya, wato Sanatoci da ‘Yan Majalisar Wakilai, zuwa sauran jama’a ke ta yin kira ga Shugaban Kasa Buhari ya sauya tsofaffin manyan hafsoshin da sabbi saboda zargin sun gaza wajen tabbatar da tsaro, Allah bai nufa ya sauya su ba, sai a Talatar.
Sojoji sun kama wani dan bindiga da ake zargin yana da nasaba da yawancin hare-haren da ake kaiwa a jihar Kaduna.
Al’umomin jihar Neja, na ci gaba da dandana kudarsu a hannun makasa, da suka mamaye yawancin garuruwa da kauyukan jihar.
Hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO, ta sanya ranar 8 ga watan gobe, zuwa 10 ga watan jibi, a matsayin ranakun rubuta jarabawarta da dalibai ke rubutawa ba a karkashin makarantu ba, wato EXTERNAL.
Malaman jami’a sun soma ganin dilin-dilin na wani alawus da suka dade suna korafi a kai wato EARNED ALLOWANCE. Sai dai wasunsu har yau ba su ga dilin-dilin na albashi da suke bi ba.
Af! Akwai wadanda suke ba ni shawarar saboda tsaro in daina fadin inda nake ko ga ni zan yi tafiya ko ina waje kaza da sauransu, a soshiyal midiya. Hmm! Ga wadanda suka dade suna bibiyar rubutuna, ban yi tsammanin na taba ambaton zan yi tafiya, ko ina kan hanyar tafiya ga ni a waje kaza, ko na iso waje kaza, da sauransu ba. Kuma idan har na ambaci ina waje kaza, to tabbas bana wajen, na dade da barin wannan waje. Kuma nakan ba da labarin na je waje, ga abubuwan da suka auku har da hotuna. Lamarin ya shude ko dadewa da shudewa, in ari NAHAWUN HAUSA, wato shudadden lokaci na daya/farko da na biyu. A duba littafin An Introduction To Hausa Grammar na M.K.M. Galadanci, ko Nahawun Hausa na Ahmadu Bello, ko Rayayyen Nahawun Hausa na Hambali Jinju, domin karin bayani. Wani lokaci nakan batar da bami in ce Kai Tsaye. Na taba kuskure a wayata na danna LOCATION, wani babban dan sanda ya kira ni a waya, ya ce na yi kuskure na danna, wayata na nuna inda nake, nan take na dauko wayar, na ga tabbas na taba wannan maballi. Na kashe maballin.
Addu’ar ita ce Allah Ya ci gaba da kare mu a kullum kuma a duk inda muke AMIN.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Shawarata Ga Mace Ki Yi Kokari Ki Dogara Da Kanki Kafin Ki Yi Aure – Maryam

Next Post

Illolin Shan Ruwa Mai Sanyi Yau Da Gobe

RelatedPosts

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 10 Zuwa 13 Ga Rajab 1442 Bayan Hijira

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 10 Zuwa 13 Ga Rajab 1442 Bayan Hijira

by Dandalin Ishak Idris Gulbi
3 days ago
0

Daga Dandalin Ishak Idris Gulbi LITININ An ceto fasinjojin nan...

Labaru

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 3 Zuwa Alhamis 6 Ga Rajab 1442 Bayan Hijira  

by Dandalin Ishak Idris Gulbi
1 week ago
0

LITININ Jama'a na ci gaba da korafin gidan talabijin na...

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 25 Zuwa Alhamis 28 Ga Jimada Sani 1442 Bayan Hijira

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 25 Zuwa Alhamis 28 Ga Jimada Sani 1442 Bayan Hijira

by Dandalin Ishak Idris Gulbi
2 weeks ago
0

LITININ Gwamnatin jihar Kogi ta yi barazanar za ta garzaya...

Next Post
Illolin Shan Ruwa Mai Sanyi Yau Da Gobe

Illolin Shan Ruwa Mai Sanyi Yau Da Gobe

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version