Waiwayen Kanun Labaru: Daga Lahadi 17 Zuwa Alhamis 21 Ga Jimada Sani 1442, Bayan Hijira

Labaru

LAHADI

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya samu sabon dogari Kanal Yusuf Dodo, tsohon dogarin Mohammad Abubakar da tun shekarar 2015 yake masa dogari, za shi karatun neman karin girma.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da rajistar ‘ya’yan jam’iyyar APC a Daura ta jjhar Katsina.

Gwamnatin Tarayya, ta fitar da kudi, don raba wa matan karkara su dubu dari da ashirin da biyar, naira dubu ashirin kowacce.

Kidinafas sun yi kidinafin mutum 21 a hanyar Kaduna zuwa Kaciya/Kachia.

Wasu da ke zargin mutanen wani kauye da ke yankin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna, na tare da kidinafas da sauran makasa, sun je kauyen sun kashe mutum goma sha biyu, yawancin mutanen kauyen sun gudu sun bar kauyen.

Jami’an tsaro sun ceto wasu mata biyu daga hannun kidinafas a yankin Gwagwada da ke karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Gwamnatin jihar Kaduna ta amince ajin JSS1, da JSS3 da SS3 na sakandare, na gwamnati da na masu zaman kansu, da wasu zababbun azuzuwan/ajujuwan firamare, su koma makaranta ranar Litinin, daya ga watan Fabrairu na wannan shekarar. Haka nan wasu ajujuwa na makarantun Islamiyya da makamantansu za su koma goben.

Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya dauki alkawarin zai gyara musu a lokacin yakin neman zabe.

Af! Wasu na tambayar sun ji Salim Is’hak Guibi a tashar Liberty/Libati. Tabbas can ya koma da aiki. Yanzun haka da asubahin nan ma, idan aka kunna tashar ta LIBERTY da ke Kaduna, za a ji shi. Zuwa yanzun ya yi aiki a:

  1. Tashar rediyo ta Raypower
  2. Tashar rediyo ta Freedom

iii. Ya zauna a rediyo Nijeriya Kaduna

  1. Tashar rediyo ta Spider
  2. Tashar DITV Alheri Rediyo
  3. Tashar Liberty.

 

 

 

LITININ

Sabbin manyan hafsoshin tsaro na kasar nan sun leka jihar Barno, suka gana da gwamnan jihar Zulum, suka kuma leka harabar rundunar da ke ta fafatawa da Boko Haram da ake kira Operation Lafiya Dole Theatre Command. Sun ce sun je ne don ganin abubuwan da ke nan, da yin sabon shiri. Sai dai wasu bayanai na nuna ‘yan kungiyar ta Boko Haram sun kai wani sabon farmaki jihar ta Barno.

Sojoji a jihar Sakkwato, sun ce sun kashe wasu ‘yan bindiga su goma sha biyu, su kuma sun rasa soja daya a lokacin da suke fafatawa da ‘yan bindigan.

Wasu kidinafas a jihar Kogi sun kashe wata yarinya mai shekara shida Farida, da kuma wani mutum bayan an biya su kudin fansarsa.

Watan jibi na Afrilu, ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, za su cika shekara biyu cur, suna dakon ariyas na sabon albashi.

A cikin wadanda suka bibiyi rubutuna na ranar Lahadi, suka yi tsokaci, akwai Akilu Muhammad da ke cewa ” ___MUNA GODIYA AMMA JIYA CIKIN DARE A SAMAN ECWA KASUWAN MAGANI KIDINAFAS SUNYI AWON GABA DA MUTUM BIYU MRS. L GIWA DA WANI FASTO”

Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, da ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, kafin ya sauka.

A Litinin aka koma makaranta, firamare da sakandare da manyan makarantu a jihar Kaduna.

Af! Wasu na ta radar ga Baba Buhari can na ta sabgar jam’iyyarsa ta APC a cikin jama’a a jihar Katsina, ba takunkumi ba tazara abinsa. Alhali ga doka can ya sa wa hannu ta daure talaka wata shida, ko tara, ko duka biyun, idan aka kama shi ba takunkumi, ko ba da tazara da sauransu. Ni ma dai na yi korafin ina ji wa Baba Buhari tsoron kada ya harbu da kwarona. Af watakila gwamna Yahya Bello na jihar Kogi, ya ba shi fahamin kwarona, da ya hana sauran gwamnoni ne!

Is’hak Idris Guibi

 

 

 

TALATA

 

Ma’aikatan cibiyoyin ilimi irin su kwalejojin foliteknik, da kwalejojin ilimi, da jami’o’i da ire-irensu duk na gwamnatin tarayya, na korafin har yanzun watan Janairu bai kare ba, wasu ba a ma shiga sabuwar shekara ba, wasu ba a ma shiga Disamba ko Nuwamba ko Oktoba ba, saboda ba dilin-dilin babu labarinsa.

Da ma kuma watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi, da aka fi shekara da biyan sauran hukumomi na gwamnatin tarayya, su kuwa har yau ba amo ba labari.

Daliban jami’ar Abuja sun yi wata zanga-zanga jiya a kan cewa sai sun biya wata naira dubu biyar harajin lattin biyan kudin makaranta, da korafin an kara musu kudin makaranta, an kuma rufe dandalin intanet na makarantar da za su iya biyan kudin makaranta wato PORTAL.

Ana ta godo da gwamnatin jihar Kaduna, ta bude dukkan makarantun firamare na jiha, ba a ce makarantun ‘ya’yan masu kudi su koma, na ‘ya’yan talakawa su jira tukuna ba.

‘Yan Boko Haram sun kashe wasu ‘yan sanda biyu, suka yi awon gaba da wasu mutum biyu a jihar Barno.

A yankin karamar hukumar Giwa ta jihar Kaduna ‘yan bindiga sun kashe mutum biyu, sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce a ‘yan kwanakin nan, sojoji na sama da kasa da sauran jami’an tsaro, sun kashe ‘yan fashin daji da kidinafas da dama, musamman a dazukan Birnin Gwari, da Giwa, da Chikun da sauransu.

Kidinafas na ci gaba da sako wadanda suka yi kidinafin, bayan an biya su kudin fansa, a Taraba, da Abuja, da sauran wurare.

Hukumar EFCC ta sake gurfanar da Orji Uzor Kalu tsohon gwamnan jihar Abiya, kuma babban mai tsawatarwa a Majalisar Dattawa. A kan zargin ya wawuri wasu makudan kudade a lokacin da yake gwamna.

Gwamnatin jihar Kano ta ce kwarona ba za ta sa ta kafa dokar kulle ba, amma ta kaddamar da dakarun kwarona su dubu biyu, da za su dinga zagayawa Kano suna tilasta wa jama’a aiki da dokar kwarona.

Yari da Marafa na jihar Zamfara sun sasanta.

Kamfanin mai na kasa NNPC, ya ce ya kashe naira biliyan 49 da rabi da ‘yan kai wajen gyaran bututun mai a cikin watanni goma.

Kudaden ajiya na kasar nan na kasashen waje, sun kara auki zuwa dala biliyan 36 da kusan rabi saboda yadda farashin mai ke dan dagawa.

Bangaren lantarki ya yi asarar naira biliyan 26 da kusan rabi saboda matsala ta Gas.

Ana ta ka-ce-na-ce a kan shekarun shugaban ‘yan sandan Nijeriya Mohammed Adamu na ritaya da ke karewa a watan nan. Shin Baba Buhari zai kara masa shekarunsa ne ko zai nada wani sabo?

Bayanai na nuna jami’an tsaro sun sa an kwashe duk manyan motocin da aka ajiye a Mararrabar Jos.

Nijeriya da wasu kasashe sun roki kada a sayar musu da alluran rigakafin kwarona da tsada.

An rufe wasu kasuwanni a Abuja, da kama mutane da dama saboda karya dokar kwarona.

Wasu ‘yan siyasa sun dukufa suna Jonathan dawo dawo.

Af! Allah Ka raba mu da sharrin mutum Amin.

 

 

LARABA

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya koma Abuja, bayan kwana hudu yana gida Daura, inda har ya kaddamar da rajistar ‘ya’yan jam’iyyar APC a jihar Katsina.

Wasu bayanai na nuna an nada karamin mataimakin shugaban ‘yan sandan Nijeriya wato A.I.G. Zanna Mohammed Ibrahim a matsayin mukaddashin shugaban ‘yan sandan Nijeriya. Kodayake wasu bayanan na nuna fadar shugaban kasa ta musanta labarin.

Pantami ya kara wa’adin kammala rajistar ‘yan kasa, da ba su lambar shaidar dan kasa, da hade lambar shaidar da layin waya, zuwa shida ga watan jibi na Afrilu.

Farashin gangar danyen man Nijeriya, ya yunkura ya kai dala hamsin da takwas kowacce ganga, wato ya karu da kashi biyu cikin dari. Kasafin shekarar nan 2021, an tsara shi ne a kan dala arba’in kowacce gangar danyen man. Da ke nuna an samu rarar dala goma sha takwas kowacce ganga ke nan.

Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’i, SSANU, da ta kananan ma’aikatan NASU, sun ce duk da sun yi taro da Ngige, yajin aikinsu yana nan.

Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi sun cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi, da aka dade da biyan sauran ma’aikatan hukumomin gwamnati, su har yau shiru.

‘Yan bindiga sun kashe mutum uku a kananan hukumomin Lere, da Birnin Gwari na jihar Kaduna.

‘Yan bindiga sun kashe mutum biyar a karamar hukumar Sabòn Birni da ke jihar Sakkwato.

Kotu ta dage gurfanar da Orji Uzor Kalu a gaban kotu, har sai ranar bakwai ga watan Yuni na shekarar nan.

Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar na yanzun, Jaja, ya je ya gyara musu gadar da ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Jama’a na ta kira ga sojojin da suka kwace mulki a hannun Suu Kyi ta Myammar su saketa daga inda suke tsare da ita.

 

ALHAMIS

 

Taron Majalisar Zartaswa ta Tarayya FEC, ya amince da kirkiro da sabbin jami’o’i guda ashirin masu zaman kansu, har da Maryam Abacha American Unibersity, da ya zama a yanzun haka a Nijeriya ana da jami’o’i masu zaman kansu har guda casa’in da tara.

Kotu ta ba da umarnin bude kasuwar Wuse ta Abuja, da sauran wuraren kasuwanci da aka kulle a Abuja, sabida zargin sun karya dokar kwarona.

Gwamna Darious na jihar Taraba, ya roki gwamnatin tarayya, ta bai wa talakan Nijeriya lasisin mallakar bindiga AK47 don kare kansa daga kidinafas da sauran makasa.

Gwamna Ortom na jihar Binuwai ya warke daga kwarona.

A Shiroro ta jihar Neja, makasa sun kashe mutum 21, kidinafas suka yi gaba da mutum 40.

A Bassa ta jihar Filato makasa sun kashe mutum biyu.

A jihar Katsina, dakaru sun kashe makasa uku.

Makasa sun kashe mutum 13 a Sabuwa ta jihar Katsina.

A jihar Kwara ‘yan APC sun dambace a wajen yin rajistar ‘ya’yan jam’iyyar, har da yi wa juna rotse, da farfasa gilasan mota, da harbi da kujera.

Osinbanjo ya ce oh da yanzun fa ya cika shekara biyu da tafiyarsa lahira! Shekara biyu a daidai wannan lokaci jirgi mai saukar ungulu da yake ciki ya rikito kasa da shi, Allah Ya taimake shi da yake yana da sauran shan ruwa a gaba, ya tsallake rijiya da baya aka ciro shi.

Af! Allah Ka mana katangar karfe da sharrin masharranta Amin. Allah kada Ka ba makiyi sa’a a kanmu Amin.

 

Exit mobile version