Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home Waiwayen Kanun Labarai

Waiwayen Kanun Labaru Daga Litinin 1 Zuwa Alhamis 4 Ga Sha’aban 1442 Bayan Hijira

by Muhammad
March 19, 2021
in Waiwayen Kanun Labarai
5 min read
Litinin
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

LITININ

Babban hafsan hafsoshin mayakan kasa na kasar nan Attahiru ya hori sojoji da ke fagen daga na yakar ‘yan boko haram da su himmar kawar da duk wani dan ta’adda da ke yankin Barno.

‘Yan Iswap sun yi wa wani ayarin sojoji kwanton-bauna a jihar Barno, suka kashe sojoji 15.

Wata cibiyar bincike da ke Zariya, ta soma yin wata na’ura mai sansano inda aka bisne bom.

Gwamnatin jjhar Kaduna ta ce sojoji sun dakile wani yunkuri da aka yi na sace ‘yan makarantar sakandare ta kimiyya, ta gwamnati da ke Ikara ta jihar Kaduna. Sai dai wata majiya na cewa tayar motar ‘yan zuwa Sakkwato Maulidi ce ta yi bindiga ta fashe daidai makarantar. ‘Yan makarantar suka tsorata, jami’an tsaro suka je wajen, sai ga labari ya watsu cewa kidinafas ne. Har an kore su.

Sojoji sun ce sun dakile wani yunkuri na kidinafin a gidajen manyan ma’aikatan tashar jiragen sama ta Kaduna.

A jihar Bauci wasu makasa sun kashe wani dan sanda da wani mai gari da ya je wajensa a Nabordo da ke yankin karamar hukumar Toro.

Mutanen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan, ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin ba aikin da shugabannin karamar hukumar na Kudan na yanzun da ke shirin barin gado, da neman ta-zarce suka taba musu. Suka ce ba gyaran gada, ba gyaran hanya, ba gyaran makaranta

Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwmnatin tarayya, na ci gaba da korafin watan gobe sun cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi. Alhali an fi shekara da biyan sauran ma’aikatan.

Af! Ga rubutun da na yi ranar Juma’a 14 ga watan Maris na shekarar 2014, watau shekara bakwai da yin rubutun kamar haka:

“Dan Nijeriya ina maka Barka da wannan yammacin Juma’a. Ya ka ji da rashin wuta, da rashin manfetur, da rashin tsaro, da yajin aikin malaman makaranta da likitoci? Ya ka ji da rashin kyawon hanyoyi da kashe maka ‘yan uwa da rashin ruwa? Ya ka ji da fataken dare da barayin biro? Ya ka ji da shugabanni da ke satar mai da wawure dukiyar kasa? Na ji kayan masarufi ma sun yi tsada saboda wahalar mai. Lallai dan Nijeriya ka shiga halin a tausaya maka”

 

 

TALATA

Rashin aikin yi ya karu da kashi 33 cikin dari a watanni uku na karshen shekarar da ta gabata.

Kamfanin mai na kasa NNPC, ya ce a watan nan kadai, za a kashe naira biliyan dari da kusan uku a tallafin mai.

Marwa na hukumar NDLEA mai yaki da miyagun kwayoyi zai kaddamar da cibiyar tsugunar da ‘yan kwaya a Ogomosho.

Atiku Abubakar ya soki kidinafin ‘yan makaranta da ake ta yi, ya ce shi ma bai yarda a dinga biyan kudin fansa ba.

Kidinafas sun kai mamaya wata makarantar firamare a yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna. Yara ‘yan makaranta kowanne ya yi ta kansa, ba su iya kama ko guda ba, sai malamai uku.

An hana wa wadanda suka kammala karatun digiri a Jami’ar Kwatano shiga aikin bautar kasa da ake shirin yi.

Mutun dubu takwas aka yi wa alluran rigakafin kwaronabairos zuwa yanzun.

Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i, sun ci gaba da korafin watan gobe za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

Mutanen Guibi ta karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da korafin babu abin da shugabannin karamar hukumar na yanzu suka tsinana musu. Ga shi suna neman ta-zarce.

Af! Ya dai kamata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tuna cewa ya dau alkawarin idan aka zabe shi, zai magance matsalar tsaro cikin wata shida. To mulki ya shekara shida a hannunsa. Kuma tabbas shi da sauran gwamnoni da ake ta kashe-kashen bayin Allah, ake zargin suna kallo, Allah Zai tambaye su jini da rayukan mutane.

Na yi nan.

 

 

LARABA

Kasashe da dama da suka hada da Faransa, da Jamus, da Italiya, sun sa a dan tsahirta da yi wa jama’arsu rigakafin kwarona da samfurin Astrazeneca da mu ma aka kawo mana aka soma tsira wa wasu, saboda korafin da wadanda aka yi wa ke yi cewa jininsu na daskarewa. Yawancin wadanda aka tsira wa allurar rigakafin a nan kasar ma suna ta korafi cewa akwai fa matsala. Sai dai kwararru bangaren kare lafiya na hukumar lafiya ta duniya WHO, sun ce za su sake nazarin allurar.

Shugaban kasar Nijar mai barin gado Muhammadou Issoufu ya ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari lambar yabo mafi girma da daraja ta kasar Nijar. Shi ma kuma Issoufun an rangada wa wani titi a birnin Abuja sunansa.

Hukumar EFCC ta bai wa dukkan ma’aikatan banki, nan da daya ga watan Yuni, wata uku ke nan, kowannensu ya bayyana kaddarorin da ya mallaka kamar yadda doka ta tabadar.

Majalisar Wakilai ta yunkura don yin dokar da za ta ba majalisar dokoki ikon kiran shugaban kasa ko gwamnonin gaban majalisar dokoki.

Gwamnatin Tarayya ta ankarar da iyaye da marika yara, su kula da kyau da ‘ya’yansu a yanzun da kidinafas suka mayar da hankali makarantu.

Bashin da kasar nan ta ciyo ya kai naira tiriliyan talatin ba wasu mutsamutsai zuwa watan Disamba na shekarar da ta gabata.

Gwamnatin jihar Kaduna ta ba da umarnin rufe dukkan makarantu na gwamnati da masu zaman kansu da ke yankin karamar hukumar Kajuru, saboda tsoron kidinafas na iya zuwa su kwashi yara. Gwamna El-Rufai ya ce yana nan kan bakarsa ba zai yi sulhu da makasa ko kidinafas ba.

Wasu da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun je kauyen Katarko da ke karamar hukumar Gujba a jihar Yobe, a a-kori-kura guda biyar, suka sa wa makaranta da asitibi da wurin soja wuta, suka jidi kayan abinci da magani, suka yi gaba. Ba su taba lafiyar kowa ba

Af! Wai ba tuni gwamnatin tarayya ke cewa ta janye tallafin da take yi wa manfetur ba? To na ji kuma tana cewa ba za ta janye tallafi ba tare da ta tintibi dukkan wadanda ya kamata ta tintiba ba. Har na ga wani bayani jita da ke nuna a watan nan kadai biliyoyin naira tallafin zai hadiye.

 

 

 

ALHAMIS

Majalisar Zartaswa ta yi zama karkashin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, har ta ma amince a kashe Dala Biliyan Daya da Rabi wajen gyara matatar mai ta Fatakwal.

Kan Majalisar Dattawa ya rabu a kan kudirin kafa hukumar kula da al’amuran aikin soja Armed Forces Service Commission.

Gwamnatin Tarayya ta biya ‘yan fansho su dubu goma sha shida, da dari biyu da goma bashin kudin fanso da suke bi, Naira Biliyan shida da ‘yan kai.

Shugaban Majalisar Wakilai Femi, ya ce a duk shekara, Nijeriya na asarar Dala Biliyan Talatin, kudaden shiga, da hukumomin tara kudaden shiga ke cogen biyan kudaden zuwa aljihun gwamnati.

Gwamnatin Ingila ta ba hukumar NDLEA ta yaki da miyagun kwayo gudummawar wani jirgin ruwa, don taimaka mata yaki da fataken kwaya.

Sarkin Birnin Gwari Zubairu Mai Gwari na biyu, ya ce jirgin sama na sojan sama ya hau daga Birnin Gwari zuwa taro da aka yi a fadar gwamnati a Kaduna, a kan tsaro, ba ayarin motocinsa da ‘yan bindiga suka yi wa kwanton-bauna suke ta harbi ba. Wasu dai na rade-radin yana cikin motocin, da aka hau harbin motocin sai ya bace, shigen batar-dabo da Sarkin Fika ya yi da aka tare ayarinsa da harbi a hanyar Zariya, da wacce Sarkin Namoda ya yi shi ma da aka yi wa ayarinsa kwanton-bauna a hanyar Kaduna.

Sojoji sun ceto mutum goma da kidinafas suka yi kidinafin a gidajen ma’aikatan tashar jiragen sama ta Kaduna kwanakin baya.

Hukumar yaki da rashawa ta ICPC, ta damke wani tsohon babban shugaban hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu JAMB, Farfesa Ojerinde, saboda sama da fadi da ake zargin ya yi da wata Naira Miliyan Dari Tara.

A jihar Kano, mutum uku suka riga mu gidan gaskiya, 284 ke jinya sakamakon shan gurbataccen ruwa.

Gwamnatin jihar Kwara ta bude makarantu goma da ta rufe a kan takaddama a kan sanya hijabi, ‘yan darikar ECWA/EKWA sun bari daliban makarantar da suka sa hijabi sun shiga makarantar sun yi karatu, amma ‘yan darikar Baptist/Baftis suka ki yarda a shigar musu makaranta da hijabi, har aka yi jefe-jefen juna da duwatsu.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Kafar Watsa Labarai Ta Jamus: Ya Dace Sin Ta Yi Alfahari Da Sakamakon Manyan Nasarori Da Ta Cimma

Next Post

Shaidar Manyan Malamai Ga Shehu Ibrahim Inyass A Matsayin Ma’abocin Faidha (2)

RelatedPosts

Labarai

Daga Litinin 29 Ga Watan Sha’aban 1442 Zuwa Alhamis 3 Ga Watan Ramadan 1442

by Muhammad
6 days ago
0

LITININ Yau za a fara duban jinjirin watan Ramadan,  idan...

Waiwayen Kanun Labarai: Daga Litinin 22 Zuwa 25 Ga watan Sha’aban 1442 Bayan Hijira

Waiwayen Kanun Labarai: Daga Litinin 22 Zuwa 25 Ga watan Sha’aban 1442 Bayan Hijira

by Sulaiman Ibrahim
2 weeks ago
0

Litinin Obasanjo da Dafta Gumi, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya, ta...

Waiwayen Kanun Labaru Daga Litinin 8 Zuwa Alhamis 11 Ga Sha’aban 1442 Bayan Hijira

Waiwayen Kanun Labaru Daga Litinin 8 Zuwa Alhamis 11 Ga Sha’aban 1442 Bayan Hijira

by Sulaiman Ibrahim
4 weeks ago
0

Daga Dandalin Idris Ishak Gulbi LITININ Shugaban Kasa Muhammadu Buhari,...

Next Post
Inyass

Shaidar Manyan Malamai Ga Shehu Ibrahim Inyass A Matsayin Ma’abocin Faidha (2)

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version