Dandalin Ishak Gulbi" />

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 16 Zuwa Alhamis 19 1442, Bayan Hijira

Kanun Labaru

LITININ

Manyan makarantu na gaba da sakandare mallakar gwamnatin jihar Kaduna sun koma makaranta. Haka nan duk makarantu na firamare da na sakandare za su koma makaranta tara ga wannan watan.

‘Yan sanda sun kama wadanda ake zargi sun yi wasoson kayayyaki a jihar Kaduna su casa”in da uku, wata ruwayar kuma ta ce mutum dari da hamsin da bakwai aka kama, har da wadanda suka kwashi kaya a ofishin shiyya na hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC.

A jihar Katsina sojoji sun ceto mata uku masu shayarwa da goyonsu, sai dai sun kashe uku daga cikin ‘yan bindigan, su kuma suka kashe soja daya.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa matasa goma sha biyar da suka nuna kwazo wajen kirkire-kirkire ciki har da wani dalibi na jami’ar Ahmadu Bello, Zariya. An ba kowanne kyautar kudi da sauransu.

Kungiyar kare hakkin bil’Adama ta SERAP da wasu kungiyoyi daban-daban har 261, sun kai Hukumar Gidajen Rediyo da Talabijin ta Kasa NBC kara kotu, saboda cin gidajen talabijin na Channels, da AIT da sauransu tara.

Lai Mohammed ya ziyarci tashar talabijin ta TBC da aka kona a lokacin zanga-zanga a Legas, inda ya ce abin da aka musu hari ne ga dimukradiyya da kuma ‘yancin fadin albarkacin baki.

Gwamnatin Tarayya ta bude sabon dandali na intanet da ‘yan kasuwa kanana da matsakaita za su iya samun tallafinta.

Gwamnatin jihar Legas ta dage duk wata doka ta hana walwala a jihar.

Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin an biya sauran ma’aikata albashin watan jiya su an manta da su. Sannan idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi, alhali an dade da biyan sauran ma’aikata. Sannan malaman jami’o’i akwai masu bin albashin wata da watanni.

Hadiza Bala Usman ta ce motoci ashirin da bakwai masu zanga-zanga suka kona har da gine-gine a shalkwatar hukumar tashoshin jiragen ruwa da ke Legas. Ta ce sai dai duk abin da suka lalata yana da inshora.

Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Af! A ranar daya ga watan Nuwamba, na shekarar 2014, jiya shekara shida daidai na yi wannan rubutu da zai biyo baya a kasa, bayan na sha da kyar, sakamakon shugabantar alkalai da na yi, a gasar mawakan Hausa mai suna ZAKARAN GWAJIN DAFI. Gasar da wasu suka shirya da hadin gwiwar rediyon Nijeriya Karama a Kofar Gamji wato Gamji Gate. Musbahu Ahmed ya yi na daya, Yaro Dan Hausa ya yi na biyu, Yaro mai Da’a ya yi na uku, Halima Dan Zaki marigaiya ta zo ta daya a mata. Kuma aka ba kowanne mota. Na ce na sha da kyar ne saboda ni na san me na gani kafin gasar, da lokacin gasar da aka kwana uku ana yi, da kuma bayan gasar har da watannin da suka biyo baya. Bayan wannan ne na yi wannan rubutu:

‘Da karfe goma na safiyar Litinim Dan Ajilo Xanguzuri ya kaddamar da wasu wakokinsa a cibiyar mata da ke nan cikin garin Kaduna, inda aka gayyaci Kamfanin Guibi-Hausa Serbices ya gabatar da Makala a kan Waka da ka’idojinta.

TALATA

Ilahirin gwamnonin jihohin Arewa, da Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan, da Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, da Ministoci, da Shugaban ‘Yan sandan Nijeriya, da kusoshi bangaren tsaro, da Sarakuna na duk na Arewa, sun yi dafifi a nan Kaduna, don gano bakin zaren hana al’adar #ENDSARS ta samu gindin zama a zukatan mutanen Arewa, da batun tsaro, da gudunmawar da Sarakuna za su ba da, da jinjina wa malamai magadan Annabawa saboda kokarin da suka yi bangaren hana zanga-zangar yin tasirin a zo a gani a Arewa.

Kungiyoyin kare hakkin al’umar Musulmi sun soma korafi, a kan yadda ake yi wa ‘yan Arewa da Musulmi kisan wulakanci, da kona masallatai ko rushe su, da sanyawa dukiyoyinsu wuta a jihohin Inyamurai. Na baya-bayan nan shi ne na Nsukka.

‘Yan Boko Haram sun kai hari kusa da Chibok, suka kashe mutum a kalla goma sha biyar, da kona gidaje masu yawan gaske.

Daga daya ga watan nan an kara kudin wuta. Kafin karin idan na ba da naira dubu daya ana ba ni awo 36 da ‘yan kai. Ranar da aka yi karin na sayo kati na dubu daya, aka ba ni awo 30 da ‘yan.

A watan Yuli, da Agusta da Satumba na shekarar nan, Gwamnatin Tarayya ta samu Naira Biliyan 424 da ‘yan kai, harajin tamanin kaya wato BAT. Da ke nuna an samu karin kashi 54 da rabi da ‘yan kai.

Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa kamfanonin jiragen sama da Naira Biliyan Hudu wato BAIL OUT.

Hukumar EFCC na nan tana bincikar tsohon shugaban Hkumar Tara Kudaden Shiga na Cikin Gida FIRS Fowler saboda zargin ya yi wata damfara ta Naira Biliyan Biyar. Haka nan ECFF ta sake gurfanar da tsohon gwamnan Binuwai kuma Sanata a yanzun, Suswan saboda zargin ya wawuri wata Naira Biliyan 3 da ‘yan kai.

Hukumar Jarabawa ta Yammacin Afirka WAEC, ta fitar da sakamakon jarabawarta ta shekarar nan, inda ta rike sakamako guda dubu dari biyu da goma sha biyar, da dari da arba’in da tara. Saboda zargin magudi.

‘Yan sandan SWAT da suka maye gurbin na SARS, sun soma samun horo a jihar Nasarawa.

‘Yan sanda sun kwato karin wasu taraktoci guda 30 da masu wasoso suka wawushe a jihar Adamawa.

Kwamitin Majalisar Wakilai ya bukaci Gwamnatin Tarayya, ta dan tsahirta da niyyarta ta jinginar da tasoshin jiragen sama hudu da ta ce za ta jinginar da su.

Yara, na boko da Islamiyya da Hadda, da ba a dade da komawa ba, sun ce “baba an ce a kawo kudin makaranta” Abin ya zo in ji mai tsoron wanka.

Af!

A kamfanin Guibi-Hausa Serbices, bayan aikin horas da ma’aikatan rediyo da talabijin da jarida, yana kuma sana’ar fassara. Kamfanin ya fassara takardu bangaren siyasa, da kimiyya, da tattalin arziki, da bangaren lafiya, da zamantakewa, da jawabai, da littafai. Yana kuma duba Hausar littafi don taceta da tsarkaketa da sauransu.

In ana bukata sai a tintibi kamfanin a

K.1. Layin Adamawa da ke Kinkinau Kaduna. Ko

08023703754.

LARABA

A ranar Talata na ga Nuhu Yunusa Tankarau na gidan rediyon ABU Samaru FM, ya yi rubutu a dandalinsa na fesbuk kamar haka:

Yanbindiga sunkawo mana hari jiya a yankinmu Na Dutsen Abba,Dake yankin karamar hukumar Zaria,inda suka kwashe mana daruruwan shanu,agaruruwan Tankarau Da kafin Mardanni,kuma sunkashe mana mutum days alokacin harin,daga cikin shanun akwai guda hamsin wadanda mallakinmune nida yayana,Dafatan Allah ya mayarmana da alkhairi Ameen,

Gwamnatin Tarayya ta ce ita fa a nata bangaren ta biya wa malaman jami’a bukatunsu, saboda haka ba ta ga dalilin da ya sa malaman ke ci gaba da yajin aiki ba.

A yanzun kidinafas sun bullo da wata sabuwar tsirfa, ta zuwa asibiti ko masallatai su tarkata jama’a su yi awon gaba da su, sai an biya kudin fansa, kamar yadda suka yi a jihar Nasarawa.

Ma’aikatan man fetur da na gas, PENGASSANG da NUPENG, sun ba da zuwa Litinin, ko gwamnati ta yi wani abu a kan albashinsu da suke bi na wata da watanni da kuma batun IPPIS, ko su janye jiki daga ayyukansu daga litinin din.

Kudaden Gwamnatin Tarayya na kasashen waje, sun kara auki daga Dala Miliyan goma sha shida da kusan rabi, zuwa Dala Miliyan talatin da biyar da rabi da ‘yan kai.

Af! A ranar Talata na tallata kadan daga cikin hajar kamfanin Guibi-Hausa Serbices, sai dai na so in yi tuya in manta da albasa.

Kamfanin na sayar da kalmomi/kalamai na soyayya, wato na tsara budurwa ko saurayi, ko tsara bazawara ko bazawari, har a kai ga aure. Wato kamfanin na sayar da tsararrun kalamai masu ratsa zuciyar masoyi ko masoyiya, da za su taimaka a kai ga nasarar sace zuciya har a kai ga aure. Kana irin sonta din nan tana ta ba ka wahala, ko ba ka san kalaman da za ka yi amfani da su ka shawo kanta ba. Sai ka garzayo kamfaninmu ba tsada.

 

ALHAMIS

Ministoci sun soma yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bayani a kan aikin da ya tura kowannensu wajen mutanensa su tattaro, barnar da ta auku sakamakon zanga-zangar #ENDSARS. Fashola ya masa bayanin Legas.

An sake darewa teburin sasantawa tsakanin Gwamnatin Tarayya, da Kungiyar Malaman Jami’o’i ko a samu malaman su koma aji. Bayanai na baya-bayan nan na nuna an tashi taron baram-baram.

Hukumar Zabe Ta Kasa INEC, ta ce a watanni uku na farkon shekara mai zuwa, za ta soma rajistar masu zabe.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta cire dokar hana walwala da ta sa, daga karfe shida na yamma zuwa karfe shida na safe a duka kananan hukumomi 23 da ke jihar.

Kidinafas sun harbe wata matar aure Aisha, mai tsohon ciki da ‘ya’ya uku, shekaranjiya cikin dare, a gidan mijinta da ke Rigachikun ta jihar Kaduna. Sun harbeta ta rasu.

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya ICC a takaice, za ta gudanar da bincike a kan zargin kashe-kashe da ake zargin jami’an tsaro sun yi wa masu zanga-zanga.

Af!

Matasan Arewa sun mayar wa da Gwamnonin jihohin Arewa da Sarakuna da sauran jiga-jigai da kusoshin Arewa da suka taru a Kaduna, suke batun mara wa shugaban kasa baya a kan dokar hana walwala a soshiyal midiya martani. Suka ce abin da kunya, a daidai lokacin da gwamnonin kudu da duk wasu manyansu, suka dukufa ga neman a biya mutanensu diyya, da kururuwa an kashe musu jama’a a Lekki don duniya ta ji, su na Arewa na magana ne a kan soshiyal midiya. Matasan suka ce an kashe mutanen Arewa a jihohin Inyamurai, da lalata musu dukiya har da masallatai, manyan na Arewa sun yi tsit a kai, ba su ta da wasu wakilai na musamman su je can su tantance barnar da aka yi wa mutanen Arewa ba. Ko su ma je da kansu ba sako ba. Soshiyal Midiya ce ta dame su.

Matasan suka ce, kullum matsalar kidinafin, da satar dabbobi, da lalata dukiya, da kashe rayuka, ga fatara, duk sun dabaibaye Arewa, ba su ne a gaban gwamnoni da ministocin Arewa ba, soshiyal midiya ce a gabansu. Suka ce Allah Ya wadaran naka ya lalace, wai rakumin dawa da ya ga na gida.

Suka ce abin da ya fi damun gwamnonin Arewa shi ne yadda za a kasa kudi a Abuja kowanne ya kwashi rabonsa ya yi gaba. Duk wani batu da suke yi a kan tsaro a Arewa, da fatar baki ne. Matasan sun yi wadannan korafe-korafen ne a wani taro na manena labaru a nan Kaduna.

Exit mobile version