Dandalin Ishak Idris Gulbi" />

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 2 Zuwa Alhamis 5 Ga Rabi’ul Auwal 1442, Bayan Hijira

Waiwayen Kanun Labaru

PRESIDENT BUHARI MEET DR AHMAD LAWAN AND GBAJABIAMILA 1A4B .: President Muhammadu Buhari receives President of the Senate Dr Ahmad Lawan and Speaker Rt Hon Femi Gbajabiamila for a meeting on the ongoing protests across the country, at the Presidential Villa Abuja. PHOTO; SUNDAY AGHAEZE OCT 18 2020.

LITININ

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawal da na Majalisar Wakilai Gbajabiamila, sun gana da Shugaban Kasa Muhamadu Buhari a kan masu zanga-zangar #ENDSARS kuma bayan sun gama ganawar Ahnad da Femi sun yi kira ga masu zanga-zangar su yi hakuri su tsahirta su daina zanga-zangar haka nan don baiwa gwamnati damar aiwatar da abubuwan da suka bukata kuma gwamnati ta amince. Sai dai Ahmad Lawal da Femi Gbajabiamila sun mance da masu zanga-zanga na Arewa ciki har da Aisha Buhari da ke bukatar a kawo tsaro a Arewa.

A Litinin aka fara horas da dakarun ‘yan sanda na musamman da suka maye gurbin SARS.

Kugiyar ma’aikatan manfetur da gas ta kasa NUPENG ta ce babu gaskiya a labarun da wasu suka yada cewa za ta dakatar da aikace-aikacenta saboda masu zanga-zangar #ENDSARS.

An daga jarabawar NECO saboda zanga-zangar #ENDSARS da ake ci gaba da yi.

Kaf din ma’aikatan kwalejin foliteknik ta Kaduna Kaduna Polytechnic sun koma aiki bayan hutun kwarona.

Makarantun jihar Kaduna sun koma bayan hutun kwarona.

Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata takwas suna dakon ariyas na sabon albashi.

Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru ba su da hanya. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Af!

A daya daga cikin rubutuna na makon jiya na jero lambobin yabo da aka ba ni, da wadanda suka ba ni ciki har da shahararriyar makarantar nan ta Kamtos International Schools da ke Kinkinau a nan Kaduna. Da yake Daraktan makarantar ya ga wancan rubutun nawa, sai na tsinci ya yi wannan tsokaci a dandalina na wasaf na Ishaq Guibi kamar haka:

Assalamu alaikum warahmatullah.

Tsokaci Akan Gaba Mai Harafin “I”

Kamtos Int’l Sch Kaduna, wannan makaranta dake kinkinau no.8 Ahmadu Chanchangi road. Ta amfana kuma tana cikin amfana da gudun mawar da Dr. Is’haq Idris Guibi ke bayarwa ga al’umma ta hanyar ilmantar dasu akan abubuwan dake faruwa a fadin najeriya da wajenta.

Kasurgumin malamin makarantane kuma jibgegen ma’aikancin jarida (Dan jarida) mai fafutukar ganin talaka yasamu sa’ida a rayuwarsa. Wannan Kalmar yabo dayasamu daga wannan makaran nada nasaba da namijin kokarisa da kwamitin wannan biki na shekarar ya gani kuma ya zakulo shi.

Idan da iyaye dake da yara a makarantu sakandire da furamari zasu rika biybiyar karatun yaransu da kuma ziyartar makarantun tare da bada shawarwari da cikakken iko wa malaman makaranta akan yaransu da tarbiyyar yaranmu ta inganta tare da iliminsu.

Daga qarshe ina fatan Allah yayi mana albarka kuma yasa muyi karshe mai kyau amin.

Aliyu Ibrahim Safana

Director,

Kamtos int’l Sch. Kaduna

TALATA

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ta hannun ministan matasa, ya nemi wadanda ke ci gaba da zanga-zangar #ENDSARS su yi cikin lumana babu tashin hankali ko barin wasu zauna-gari-banza su labe da su, su ta da zaune tsaye.

Masu zanga-zangar #ENDSARS sun ta da kura a jihar Kano saboda zargin ‘yan sanda sun kashe musu wani, su kuma ‘yan sanda suka musunta.

Masu zanga-zangar #ENDSARS a jihar Edo sun sa gwamnatin jihar ta sa dokar hana walwala ta sa’a 24 har sai yadda hali ya yi saboda banka wa ofisoshin ‘yan sanda uku wuta, da sanya ‘yan gidan yari tserewa.

An girke sojoji a wasu yankuna na Abuja don tabbatar da doka, sai da kungiyoyin al’uma sun yi kashedin idan wani soja ya harbi wani daga cikin masu zanga-zangar #ENDSARS ba za su yarda ba. Jiya da yamma an kashe mutum biyu a tsakanin masu zanga-zangar da suka gwabza ya su-ya su.

Gwamnatin jihar Kaduna ta kaddamar da nata kwamitin bincike na shari’a na wadanda ‘yan sanda suka zalunta, da ba shi wata shida ya kammala aikin da aka sa shi.

Ana sa ran daliban kwalejin foliteknik ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic, su soma komawa makaranta ranar biyu ga watan gobe. Su kuwa daliban jami’ar jihar Kaduna jiya suka soma jarabawa.

Af!

Al’umar Kinkinau na ta korafin an kawo wa kowanne gida ko shago takardar a je a biya kudin zama a duhu na watan Satumba, naira dubu talatin, wasu naira dubu ashirin da tara da wasu kwabbai ko sulalla a sama. Af! Kudin wutar da ba su sha ba, ba kudin zama a duhu ba. Ka ga kullum ko in ce kowanne yini sai ka biya naira dubu daya kudin wuta, ko ka sha ko ba ka sha ba. Nawa ne ma albashi mafi karanci wato MINIMUM WAGE a Nijeriya? In ka cire naira dubu talatin kudin wuta a wata saura nawa?

Na yi nan.

LARABA

Majalisar Dattawa ta ba shugaban kasa Muhammadu Buhari shawarar ya yi wa ‘yan Nijeriya jawabi a kan zanga-zangar da ake ci gaba da yi.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi ganawar sirri da Magashi da Olanishakin a kan zanga-zangar da ake ci gaba da yi.

Shugaban ‘yan sandan Nijeriya ya ba da umarnin girke ‘yan sandan kwantar da tarzoma a ko’ina cikin fadin kasar nan don kare rayuka da dukiyoyi daga mabarnatan da suka fake da masu zanga-zangar lumana suna aikata barna.

Gwamnoni sun kafa dokar hana walwala ta sa’a ashirin da hudu a jihar Legas, da jihar Oshun, da Imo, da Edo, da Abiya, da Jos, da Ondo, da Ekiti saboda yadda ake zargin wasu zauna-gari-banza sun fake da masu zanga-zangar #ENDSARS suna aikata barna. Misali motocin da aka kona a Abuja na wajen miliyan saba’in da biyar, da gidaje da kayan ‘yan kasuwa da aka lalata har da kisa, masu kayan sun ce sai bayan da masu zanga-zangar sun gama sun wuce ne, wasu zauna-gari-banza suka biyo baya suka sa wa wuta.

Gwamnatin Tarayya ta soma farautar fursunoni su wajen dubu biyu da wasu zauna-gari-banza da suka fake da masu zanga-zanga suka balle gidajen yari biyu da ke jihar Edo, suka saki fursunonin.

Zuwa yanzun ‘yan sanda sun kama zauna-gari-banza su goma sha biyu da bindigogi biyar da suka diba a ofisoshin ‘yan sanda da suka kai wa farmaki a jihar Edo.

  1. Tinubu ya yi kira ga masu zanga-zangar #ENDSARS su tsahirta da zanga-zangar haka nan, su bai wa gwamnati damar aiwatar da abubuwan da suka nema.

Har zuwa wuraren karfe hudu na asubah ina ta leka dandalin hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC a takaice ko zan samo muku sabbin alkaluman wadanda suka harbu, ban ga sun sa ba.

 

ALHAMIS

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kiran a yi hakuri tare da fahimtar kokarin da gwamnati ke kan yi don biyan bukatun masu zanga-zanga.

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya yi kira ga shugabannin al’uma su taimaka su sa baki don kwantar da tarzomar da matasa ke kan yi.

Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar,, da Obasanjo, da Oni na Ife, da Gbajabiamila shugaban majalisar wakilai, da Tinubu, da Clinton,, da Hillary Clinton da sauran mashahuran shugabannin duniya, da mutane na ciki da wajen Nijeriya, sun nuna rashin jin dadinsu a kan kazancewar zanga-zangar lumanar #ENDSARS da kuma kisan da ake zargin jami’an tsaro sun yi wa matasan. Har Shek Dahiru Bauci ya ce ba a kashe wuta da wuta.

Kungiyar kare hakkin bil’Adama ta amnasti da ta Human Right Watch sun zargi sojoji da kashe masu zanga-zanga su goma sha biyu, a Legas, zargin da sojoji suka kira FAKE NEWS.

Fusatattun masu zanga-zanga da ke zargin jami’an tsaro sun bindige wasunsu a Lekki Plaza da ke Legas, sun banka wa ginin tashar TBC, da tashar talalabijin ta jihar Legas, da shalkwatar hukumar tashoshin jiragen ruwa, da shalkwatar hukumar kiyaye hadurra ta kasa wuta. Suka kuma kai hari gidan Oba na Legas, da gidan mahaifiyar gwamnan Legas, da sauran muhimman gine-gine da kaddarori musamman na gwamnati.

Hukumar Gidajen Rediyo da Talabjin ta kasa NBC, ta gargadi gidajen talabijin da rediyo da su dinga yi suna kiyayewa da ka’idojin aikinsu wajen ba da rahoton zanga-zangar da ake yi, don gujewa kara iza wutar tashin hankali da tunzura jama’a.

Wasu ‘yan bindiga sun kai hari Talatar Mafara ta jihar Zamfara, suka kashe mutum a kalla 22, da satar dabbobi.

Af! ‘Yan bindiga sun kashe mutane har ashirin da biyu tashi guda a Talatar Mafara ta jihar Zamfara. Ga wadanda aka kashe a Kidandan ta Giwa da ke jihar Kaduna. Ga na Kagara da ke jihar Neja. Ga na Jibiya da sauran sassan jihar Katsina. Ga na yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna, da kudancin jihar Kaduna, da kidinafas da ke satar na sacewa, da yi wa mata da ‘yan mata fyade, da cinikin mutum har da mata masu shayarwa da masu juna biyu. Su… Af! Bakina da goro. Af! Ga wani can ya ce Guibi ba a tauna goro da asubah sai asuwaki.

Na yi nan.

Exit mobile version