Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 23 Zuwa Alhamis 26 Ga Rabi’ul Awwal 1442, Bayan Hijira

Daga Ishak Idris Guibi

LITININ

Ina ta lekawa Cibiyar Da Ke Aikin Dakile Cututtuka ta Kasa NCDC a takaice har zuwa asubahin nan ban ga ta fitar da sabbin alkaluman wadanda suka harbu da cutar kwaronabairos ba. Ko kudin da ke hannunsu ya kare ne sai an kuma hankada musu wasu?

Mayakan Sama sun far ma wasu barayin shanu da ke kokarin satar shanun a yankin Kuzo da ke jihar A Kaduna, sojojin suka kashe da dama daga cikinsu.

A litinin sauran ‘yan makaranta da ba su koma makaranta ba a jihar Kaduna, suka koma.

Sakamakon wata sasantawa tsakanin Gwamna Matawalle na jihar Zamfara da wasu kidinafas, kidininafas din sun sako wasu mata ashirin da shida, da suka yi kidinafin dinsu a yankin Faskari ta jihar Katsina.

Ana nan ana ci gaba da tirka-tirka tsakanin Gwamnatin Tarayya da malaman jami’o’i, dalibai na ci gaba da zaman kashe wando a gida. Sai dai daliban da ke jami’o’i na kudi wato masu zaman kansu, na ta karatunsu.

Wata kungiya na ta fitar da fostar yakin neman zaben El-Rufai a matsayin shugaban kasa..

Daidai lokacin da malaman jami’a ke kwashe wata da watanni ba albashi, ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, sun cika shekara biyu ke nan suna dakon ariyas na sabon albashi.

Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna ta musu alkawarin hanya har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe. Idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Af! Daliban jami’o’i na Gwamnatin Tarayya ke gida suna zaman kashe wando. Daliban jami’o’i da ke zaman kansu/Jami’o’i na kudi, na makaranta suna ta karatu. ‘Ya’yan su waye ko su wane ne ke gida suna zaman kashe wando? ‘Ya’yan su waye ko su wane ne ke makaranta suna ta karatu?

 

 

TALATA

Talata ta kasance goma ga watan Nuwamba, amma kuma arba’in da daya ga watan Oktoba ga yawancin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya bangaren ilimi. Bari in muku gwari-gwari. Har yau yawancin ma’aikata, misali na kwalejin foliteknik ta Kaduna ba su ga albashin watan jiya ba. Kuma sun kusan shekara ko ma fiye da shiga tsarin IPPIS. Haka ma albashin watan Satumba, sai da watan Oktoba ya raba biyu, sannan suka ga dilin-dilin na watan Satumba. Sannan suna korafin idan Allah Ya kai mu watan Afrilu na shekara mai zuwa, za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi. Ariyas din da aka dede da biyan sauran ma’aikata da ba na bangaren ilimi ba. Laifin da suke dorawa ga tsarin IPPIS.

Kugiyar malaman jami’o’i ta ce ba fa laifinta ba ne dalibai ke ci gaba da zaman kashe wando a gida. Sun ce laifin Gwamnatin Tarayya ne. Ita ke nuna ba ilimin ne a gabanta ba. Wata takwas ke nan ba a biyan malaman albashi.

Kungiyar Ma’aikatan Fetur da Gas, PENGASSAN ta soma yajin aiki bayan karewar wa’adin da ta ba Gwamnatin Tarayya. Da ke nuna idan gwamnatin ba ta yi wani abu cikin hanzari ba, za a shiga wahalar mai da gas. Sun ce suna bin albashi da sauransu.

Shugaban Hukumar Zabe ta Kasa Farfesa Yakubu ya sauka daga mukaminsa ya mika wa Iya Bayis Mashal Ahmed Mu’azu mai ritaya riko, saboda kamar yadda Farfesan ya bayyana, bai kamata ya wuce jiya yana kan mukamin nasa ba, saboda a jiyan wa’adinsa ya kare. Kuma ba a kammala batun sake nada shi da Shugaban Kasa ya yi ba.

Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello ya harbu da kwaronabairos.

Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna, ya ce nan gaba kadan za a yi dokar da za ta tabbatar da karba-karba, na sarauta, a musamman gidajen da suka gaji saurauta, kamar yadda yake a Masarautar Zazzau.

An rantsar da Sarkin Zazzau na goma sha tara, Ahmad Nuhu Bamalli da mika masa Sandar Girma. A wadanda suka halarci bikin a Zariya, har da gwamnan jihar Legas Sanwo-Olu da na jihar Filato Lalong.

Wasu ‘yan bindiga sun kai wa ayarin wani kwamisha na jihar Zamfara hari, har suka kashe daya daga cikin direbobinsa.

Gwamnati ta bayyana cewa babu wani albashi na musamman da aka tsara wa dakarun SWAT da suka maye gurbin SARS.

Af! Pfizer na Amurka, da hadin gwiwar Bio-Tech na Jamus, ya yi nasarar samar da rigakafin cutar kwaronabairos. Sun gwada shi a kasashe shida, a mutum fiye da dubu arba’in da uku, kuma an ga ingancinsa cif-cif. Har Shugaban Kasa Muamadu Buhari ya nuna farin cikinsa, da kuma rokon a samu EQUITABLE DISTRIBUTION na VACCINE din.

 

 

LARABA

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da wani tsari na tallafa wa matasa manoma.

Mataimakiyar Shugaban Majalisae Dinkin Duniya Amina Mohammad, ta gana da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, da alkawarin Majalisar za ta tallafa wa wasu kasashe har da Nijeriya, su samu su farfado daga halin da suka shiga na durkushewar tattalin arziki sakamakon kwaronabairos. Ta ce wannan durkushewa ce ta sa matasa zanga-zanga a duniya.

\ Gamaiyyar Kungiyoyin Matasan Arewa, ta nemi Majalisar Dinkin Duniya ta haramta kungiyar nan ta IPOP musamman idan aka yi la’akari da rawar da ta taka ta hanyoyi daban-daban a zanga-zangar #ENDSARS da ta rikide har da kashe-kashe na kabilanci.

Sojoji na sama, sun kashe ‘yan ISWAP da lalata wurarensu a jihar Barno. Sojojin sun kuma gyara jiragen yaki samfurin Fighter Jet F-7 har guda 9, sai kuma wasu sabbi guda uku daga Pakistan.

Gwamnan jihar Legas Sanwo-Olu ya yunkura don soke fanshon da ake biyan tsofaffin gwamnoni da mataimakansu na jihar.

Kotu a Dubai ta yanke wa wasu mutum shida hukunci daban-daban har da daurin-rai-da-rai, saboda gano su suna tallafa wa kungiyar Boko Haram gudanar da aikace-aikacenta a Nijeriya daga can.

Ana ci gaba da zargin juna, tsakanin kungiyoyin malamai da na sauran ma’aikatan jami’o’i manyansu da kanana, a bangare guda, da kuma Gwamnatin Tarayya a ta daya bangaren, wane ne ke kokarin durkusar da karatun jami’a a Nijeriya?

Af! Allah Ya yi wa Dan Iyan Zazzau, Hakimin Kabala Alhaji Yusuf Ladan rasuwa, kuma a Talata aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar. Uba a aikin rediyo da talabijin. Daya daga cikin wasannin kwaikwayo da yake rubutawa a lokacin da yake aiki da RTK aka mayar da shi littafi, shi ne ZAMAN DUNIYA IYAWA NE da ake amfani da shi wajen koyar da dalibai a mataki daban-daban. Bayan mukamai da ya rike a Rediyon Nijeriya na Kaduna, ya kuma rike rediyon jihar Kaduna. Da ya ji kana karanta labaru ka ce RAWAR DA SARAKUNA ZA SU TAKA ko SUKE TAKAWA, zai sa a kira ka ofishinsa, ya tambayeka ka taba ganin sarkin garinku na tika ko taka rawa?

A lokacin da na fara gabatar da shirin MADUBI a tashar talabijin ta jihar Kaduna KSTb a wuraren shekararun 2000, nakan yawan gayyatarsa shirin, ya fede mana wasu kalmomi na Hausa. A wajensa na san cewa kalmar DURBAR asalinta kalma ce ta Hindu wato Indiyanci. Haka nan EMIR daga Larabci AMIR da sauransu.

Allah Ya jikan Alhaji Yusuf Ladan, Ya sa mu da muka yi saura, mu cika da kyau da imani Amin.

 

 

ALHAMIS

Ana cikin makokin rasuwar Dan Iyan Zazzau Hakimin Kabala Alhaji Yusuf Ladan, sai kuma ga rasuwar tsohon gwamnan tsohuwar jihar Kaduna Alhaji Abdullkadir Balarabe Musa. Kamar ‘yan soshiyal midiya sun san ya kusan rasuwa, suka dinga sa dinbin ayyukan da ya yi cikin dan lokacin da ya yi yana gwamnan jihar Kaduna daga watan Oktoba na shekarar 1979 zuwa watan Yuni na shekarar 1981. An haife shi a 1936 da ke nuna ya rasu yana da shekara tamanin da hudu a duniya. Ya rasu ya bar iyali da manyan ‘ya’ya maza da mata. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aiko da gaisuwar ta’aziyyarsa. Tsofaffin gwamnonin jihar Kaduna Sanata Makarfi, da Ramalan Yero na cikin dinbin wadanda suka masa Sallah a masallacin Sarkin Musulmi Bello.

Allah Ya jikan musulmi da suka riga mu gidan gaskiya, mu da muka yi saura Ya sa mu cika da kyau da imani Amin.

An mike gadan-gadan ana wayar wa da masu korafin sai an cire rubutun ajami (‘Gagara mai shi’ in ji malamina marigayi Rabiu Zarruk da shi ya koya mana AJAMI a karatun digiri na farko a ABU a 1988/1989) daga jikin kudin Nijeriya. Masu korafin sai an cire AJAMIN sun dauka Larabci ne ko kalma ce ta Alkur’ani mai girma, wato a tunaninsu an musulantar da kudin Nijeriya ke nan. To ba larabci ba ne, kuma da za a dauko balarabe a ce ya karanta ya fadi ma’anar ba zai sani ba. Hanyar rubutu ce ta fadakar da wanda bai yi karatun boko ba, ko bai san haruffan boko ba, ya iya sanin naira nawa ne. Akwai littafai da dama har da Baibul da kiristoci na duniya suka rubuta da larabci ko haruffan larabcin da wanda bai sani ba sai ya dauka Alkur’ani ne.

Ofishin Kasafi ya ce da wuya hukumomi guda 428 na gwamnatin tarayya, su iya biyan ma’aikatansu albashin wannan watan da muke ciki na Nuwamba saboda ba kudi.

Majalisar Wakilai ta umarci Shugaban ‘Yan Sandan Nijeriya, ya mika wa Shugaban Majalisar sunayen duk ‘yan sandan da aka kashe sakamakon zanga-zangar da aka yi domin biyan iyalansu diyya.

Wani dan rajin kare hakkin bil’Adama, Mista Okeke ya kai jiga-jigan zanga-zangar #ENDSARS su wajen 47, makadansu da marayansu, kotu, saboda zargin sun masa barna.

A yanzun cututtuka irin su yelofiba da maleriya da kwalara ke ta kisa. Na baya-bayan nan shi ne mutane takwas da yelofiba ta yi sanaddiyar mutuwarsu a jihar Bauci.

Af! Na yi wani kuskure a rubutuna na Laraba. Na ce an rada wa ginin rediyo da talabijin na KSMC da ke titin Wurno daura da titin Rabah da ke Badarawa Kaduna, sunan marigayi Yusuf Ladan. To sunan Muhammadu Ladan ne ba Yusuf Ladan ba.

Kuma har ila yau shi Yusuf Ladan idan ya ji kana karanta labaru ka ce SARKI YA KOKA sai ya sa a kira ka ofishinsa. Ya tambayeka ka taba ganin Sarki na kuka? Kodayake na san wani zai ce ai kuwa a litinin da ta gabata wajen nadin Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Ahmad Nuhu Bamalli, ya ga yana jawabi yana zubar da hawaye. Ba irin wannan kukan Dan Iya yake nufi ba. Dan Iyan Zazzau na nufin kukan wahala.

Exit mobile version