LITININ
Gwamnatin jihar Kogi ta yi barazanar za ta garzaya gaban kuliya, don kai karar kwamitin nan na shugaban kasa na kwarona PTF, da cibiyar raba alkaluman kwarona NCDC , muddin suka ci gaba da bata wa jihar Kogi suna a kan abin da ta ce ta gano, ana damfarar Baba Buhari da shi ne wato kwarona.
Kungiyoyi sun garzaya gaban kuliya, don kai karar Baba Buhari, a kan saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan da ya yi, ya ba wanda ba dan sanda ba Muhammed Adamu, mukamin shugaban ‘yan sandan Nijeriya. Sun ce daga ranar da shekarun ritayar Mohammed Adamu suka cika, daga ranar shi ba dan sanda ba ne, kuma ba ma’aikacin gwamnati ba ne.
Wasu lauyoyi na shirin kai Baba Buhari kara gaban kuliya, saboda ya kyale Boboye da ba ma’aikacin gwamnati ba, yana shugabantar hukumar kula da kiyaye hadurra ta kasa FRSC. Sun ce tun a watan Nuwamba shekarunsa na ritaya suka kai da ya kamata ya sauka a nada wani.
Gwamnatin jihar Kaduna da ma’aikatar ilimi ta jihar Kaduna da mahukunta jami’ar jihar Kaduna, sun yi barazanar kai wadanda suka kitsa labarin wai za a sauya wa jami’ar jihar Kaduna suna, kara gaban kuliya. Sun ce sam a yanzun dai, babu wannan yunkuri na sauya sunan jami’ar zuwa Jami’ar Magajin Gari Sambo.
Makasa da kidinafas na ci gaba da cin karensu babu babbaka a sassan jihar Kaduna. Karen da suka ci ba babbaka shekaranjiya asabar, shi ne sun kashe mutum a kalla goma sha tara. Ka ji fa mutum daya, biyu, uku, hudu, biyar, shida, bakwai, takwas, tara, har goma sha tara, 14 a yankin Birnin Gwari, 5 a Kajuru. Sun kuma kona gidajen talakawa son ransu, da jidar kayansa. Kafin nan sun tare hanyar Birnin Gwari suka dinga harbin motocin matafiya, suka kashe na kashewa, suka jidi na jida wato kidinafin. Suka jikkata wasu da harsashi suna asibiti.
Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun da wa’adinsa ke shirin karewa wato Jaja, ya je ya cika musu alkawarin da ya daukar musu lokacin yakin neman zabe, na idan sun zabe shi zai gyara musu gada. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai je ya gyara musu ba.
Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.
Af! Jiya a tashar talabijin ta Brekete ta su Ahmed Isa, na ga wasu kwararru bangaren shuke-shuke, na bayanin cewa, gemun nan na dan masara, da har Musa Dankwairo ke waka yana cewa “Ga abin goye kowa da gemunai” Idan ana yin shayi da shi, yana maganin hawan jini. Wato a dafa shi a matsayin shayi.
TALATA
A ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu Majalisar Dattawa da ta Wakilai duk suka koma aiki, inda ake sa ran su amince da sabbin hafsoshin tsaro da Shugaban Kasa Buhari ya zaba.
Wanda ya maye gurbin Buratai, Attahiru, ya leka inda sojojinsa suke fagen daga a jihar Yobe da ta Barno, don karfafa wa sojojin gwiwa, da batun za a hada kai da sojojin Kamaru da na Cadi, domin gamawa da ‘yan Boko Haram, da ma sauran wadanda ke dama wa bangaren tsaron kasar nan lissafi.
Sanata Ndume ya ce jama’ar Arewa Maso Gabashin kasar nan ba za ta ci gaba da dogaro da sadakan da ake ta ba ta ba, sakamakon gudun hijira da kungiyar Boko Haram ta jefa ta ciki. Ya ce mafita ita ce kawo karshen matsalar tsaro a yankin. Mutanen Gwoza su dubu 27 Gwamna Zulum da Ndume suka tallafa wa da kayan abinci da kuma rancen kudi.
Wani madugun fataken miyagun kwayoyi, ya yi kashin koken wato hodar ibilis, dauri tamanin da shida a tashar jiragen sama ta Abuja.
Likkafar man fetur sai kara gaba take yi domin kowacce gangar danyen man ta yunkura zuwa dala sittin. Da ke nuna kasar nan ta soma murmurewa daga rashin kudi.
Kotu ta ba Orji Uzor Kalu damar ya tsara kalubalantar kai shi kotu da gwamnatin tarayya ta yi ta hannun EFCC, a tuhumar da ake masa ya wawuri wata naira biliyan 7 da ‘yan kai a lokacin da yake gwamnan jihar Abiya.
‘Yan sanda sun tsaurara tsaro a yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna, da a ‘yan kwanakin nan makasa da kidinafas ke ta cin karensu ba babbaka suna kashe jama’a da sace na sacewa.
A dai jihar ta Kaduna, ‘yan sanda sun ce kidinafas sun kashe mutum daya, suka yi kidinafin mutum goma sha daya, da ji wa mutum daya rauni.
A jihar Zamfara wani rikakken dan fashin daji ne da wasu mutum biyar, suka ce sun tuba sun ajiye makamai.
Af! Allah! Allah!! Allah!!! Ka mana maganin abin da ya dame mu Amin.