Dandalin Ishak Idris Gulbi" />

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 25 Zuwa Alhamis 28 Ga Jimada Sani 1442 Bayan Hijira

LITININ

Gwamnatin jihar Kogi ta yi barazanar za ta garzaya gaban kuliya, don kai karar kwamitin nan na shugaban kasa na kwarona PTF, da cibiyar raba alkaluman kwarona NCDC , muddin suka ci gaba da bata wa jihar Kogi suna a kan abin da ta ce ta gano, ana damfarar Baba Buhari da shi ne wato kwarona.
Kungiyoyi sun garzaya gaban kuliya, don kai karar Baba Buhari, a kan saba wa kundin tsarin mulkin kasar nan da ya yi, ya ba wanda ba dan sanda ba Muhammed Adamu, mukamin shugaban ‘yan sandan Nijeriya. Sun ce daga ranar da shekarun ritayar Mohammed Adamu suka cika, daga ranar shi ba dan sanda ba ne, kuma ba ma’aikacin gwamnati ba ne.


Wasu lauyoyi na shirin kai Baba Buhari kara gaban kuliya, saboda ya kyale Boboye da ba ma’aikacin gwamnati ba, yana shugabantar hukumar kula da kiyaye hadurra ta kasa FRSC. Sun ce tun a watan Nuwamba shekarunsa na ritaya suka kai da ya kamata ya sauka a nada wani.
Gwamnatin jihar Kaduna da ma’aikatar ilimi ta jihar Kaduna da mahukunta jami’ar jihar Kaduna, sun yi barazanar kai wadanda suka kitsa labarin wai za a sauya wa jami’ar jihar Kaduna suna, kara gaban kuliya. Sun ce sam a yanzun dai, babu wannan yunkuri na sauya sunan jami’ar zuwa Jami’ar Magajin Gari Sambo.
Makasa da kidinafas na ci gaba da cin karensu babu babbaka a sassan jihar Kaduna. Karen da suka ci ba babbaka shekaranjiya asabar, shi ne sun kashe mutum a kalla goma sha tara. Ka ji fa mutum daya, biyu, uku, hudu, biyar, shida, bakwai, takwas, tara, har goma sha tara, 14 a yankin Birnin Gwari, 5 a Kajuru. Sun kuma kona gidajen talakawa son ransu, da jidar kayansa. Kafin nan sun tare hanyar Birnin Gwari suka dinga harbin motocin matafiya, suka kashe na kashewa, suka jidi na jida wato kidinafin. Suka jikkata wasu da harsashi suna asibiti.
Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun da wa’adinsa ke shirin karewa wato Jaja, ya je ya cika musu alkawarin da ya daukar musu lokacin yakin neman zabe, na idan sun zabe shi zai gyara musu gada. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai je ya gyara musu ba.
Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.
Af! Jiya a tashar talabijin ta Brekete ta su Ahmed Isa, na ga wasu kwararru bangaren shuke-shuke, na bayanin cewa, gemun nan na dan masara, da har Musa Dankwairo ke waka yana cewa “Ga abin goye kowa da gemunai” Idan ana yin shayi da shi, yana maganin hawan jini. Wato a dafa shi a matsayin shayi.

TALATA
A ranar Talata, 9 ga watan Fabrairu Majalisar Dattawa da ta Wakilai duk suka koma aiki, inda ake sa ran su amince da sabbin hafsoshin tsaro da Shugaban Kasa Buhari ya zaba.
Wanda ya maye gurbin Buratai, Attahiru, ya leka inda sojojinsa suke fagen daga a jihar Yobe da ta Barno, don karfafa wa sojojin gwiwa, da batun za a hada kai da sojojin Kamaru da na Cadi, domin gamawa da ‘yan Boko Haram, da ma sauran wadanda ke dama wa bangaren tsaron kasar nan lissafi.
Sanata Ndume ya ce jama’ar Arewa Maso Gabashin kasar nan ba za ta ci gaba da dogaro da sadakan da ake ta ba ta ba, sakamakon gudun hijira da kungiyar Boko Haram ta jefa ta ciki. Ya ce mafita ita ce kawo karshen matsalar tsaro a yankin. Mutanen Gwoza su dubu 27 Gwamna Zulum da Ndume suka tallafa wa da kayan abinci da kuma rancen kudi.
Wani madugun fataken miyagun kwayoyi, ya yi kashin koken wato hodar ibilis, dauri tamanin da shida a tashar jiragen sama ta Abuja.
Likkafar man fetur sai kara gaba take yi domin kowacce gangar danyen man ta yunkura zuwa dala sittin. Da ke nuna kasar nan ta soma murmurewa daga rashin kudi.
Kotu ta ba Orji Uzor Kalu damar ya tsara kalubalantar kai shi kotu da gwamnatin tarayya ta yi ta hannun EFCC, a tuhumar da ake masa ya wawuri wata naira biliyan 7 da ‘yan kai a lokacin da yake gwamnan jihar Abiya.
‘Yan sanda sun tsaurara tsaro a yankin Birnin Gwari ta jihar Kaduna, da a ‘yan kwanakin nan makasa da kidinafas ke ta cin karensu ba babbaka suna kashe jama’a da sace na sacewa.
A dai jihar ta Kaduna, ‘yan sanda sun ce kidinafas sun kashe mutum daya, suka yi kidinafin mutum goma sha daya, da ji wa mutum daya rauni.
A jihar Zamfara wani rikakken dan fashin daji ne da wasu mutum biyar, suka ce sun tuba sun ajiye makamai.
Af! Allah! Allah!! Allah!!! Ka mana maganin abin da ya dame mu Amin.

LARABA
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin yin titin dogo da zai ci Dala Biliyan Biyu, da zai tashi daga Kano ya bi ta Katsina, ya bi ta Jigawa ya dangana da Maradi ta kasar Nijar.
Majalisar Dattawa ta karanta sakon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na neman amincewarta, a nadin da ya yi na sabbin hafsoshin tsaro, da nada tsofaffin hafsoshin mukamin jakada.
Gwamnatin Tarayya na shirin yi wa ‘yan Nijeriya rajistar shaidar dan kasa ta amfanin da lambar shaidarsu ta banki wato BVN.
NCDC da ta saba raba wa jihohi alkaluman kwarona a kullum, ta ce za ta koma yin rabon daga mako sai mako, maimakon kullum da take yi a yanzun.
Kasar Caina wato Sin da Nijeriya, sun cika shekara hamsin cur suna kawance da dasawa.
Hukumar yaki da mu’amala da miyagun kwayoyi NDLEA, ta ce ta kama kunshin koken wato hodar Ibilis kunshi arba’in a tashar Tincan ta Legas. Bayan wanda ta kama a Abuja da ya yo kashin hodar sinkinta da yawa kamar yadda na kawo muku labarin jiya.
Kudin sauke man fetur bayan an shigo da shi kasar nan, ya karu zuwa naira 180 kowacce lita.
Rundunar nan ta Amotekun, ta ce ta kama fulani makare da wata tantebur da makamai a Ibadan.
Gwamnonin jihohin Arewa sun ce yawon da fulani suke yi suna kiwo wato KIWON SAKE, ya zama tsohon ya yi, su rungumi sabuwar hanyar kiwo ta natsuwa waje guda su yi kiwonsu da ake kira RANCHING.
Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin watan jibi za su cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.
A kananan hukumomi biyar na jihar Kaduna, makasa sun kashe mutum 23, sai dai gwamnatin jihar Kaduna da ta fitar da wannan sanarwa da farko a jiya, daga bisani ta fitar da sanarwa ta biyu cewa ta bi duk inda ta san akwai wadannan makasa, ta murkushe su ta sama.
Af! Muna cigiyar wani danmu Sadik Sani Aliyu Kudan, da ke karatu a Jami’ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, da ya fita gida yau wajen kwana 13 ke nan da sunan zai je yin fenti. Har yau shiru. Saboda haka muke rokon jama’a wanda ya ji duriyarsa ya sanar da ofishin ‘yan sanda mafi kusa, ko ya tintibe mu. Allah Ya bayyana shi cikin koshin lafiya Amin.
ALHAMIS
A ranar Laraba da dare hukumar da ke kaso da raba alkaluman kwarona, ta raba wa jihohi kwarona 1,131 kamar haka:
Legas 297
Abuja 194
Kaduna 83
Kano 59
Oyo 58
Imo 52
Oshun 47
Folato 45
Edo 43
Akwa Ibom 42
Ribas 42
Ogun 29
Kwara 24
Binuwai 21
Nasarawa 16.
Ekiti 7
Bauci 6
Delta 6
Bayelsa 4
Sakkwato 2
Gwambe 1
Kason da aka bayar na wadanda suka harbu da kwarona zuwa yanzun, 142 578
Kason da aka ba wadanda aka ce sun warke 116,937
Kason da aka ba wadanda aka cr masu jinya ne 23,929
Kason da aka ba wadanda aka ce sun riga mu gidan gaskiya shi ne 1,702.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya aike wa Majalisar Wakilai wasikar neman su amince da nadin da ya yi wa tsofaffin hafsoshin tsaron kasar nan, mukaman jakadu. Su kuma amince masa da sabbin da ya nada hafsoshin tsaron kasar nan.
A zaman Majalisar Dattawa na jiya, da na Majalisar Wakilai duk a jiyan, sun tabo batun rashin tsaro da ke ci gaba da addabar kasar nan.
Kungiyoyin kwadago sun nuna ba su yarda da yunkurin da Gwamnatin Tarayya ta yi na kara kudin man fetur ba.
‘Yan kungiyar Boko Haram sun ci gaba da barnar da suka saba yi, ta lalata manyan turakun wayoyin lantark da na wayoyin sadarwa a Maiduguri.
A Gaidam ta jihar Yobe ‘yan kungiyar Boko Haram sun je garin sun ci karensu ba babbaka son ransu, suka gama suka yi tafiyarsu.
Kotu ta ba da umarnin sakarwa asusun banki na jagororin gwagwarmayar kawo karshen ‘yan sandan SARS mara.
Hukumomin sojan Nijeriya, sun nada sabon daraktan yada labaru da hulda da jama’a na soja Birgediya Janar Yerima, don maye gurbin tsohon Birgediya Janar Sagir Musa da aka tura wajen horas da soja da ke Kwantagora.
Auwal Daudawa da ake zargin shi ne jagoran kidinafin ‘yan makarantar Kankara, ya tuba ya yi saranda a ahuwar da ake yi wa ire-irensa. Shi kuma tsohon shugaban kwamitin rikon kwarya na karamar hukumar Jibiya Haruna Musa da ake zargin yana alaka da kidinafas, an ci gaba da tsare.
Gangar danyen mai ta ci gaba da shanawa inda ta kai dala sittin da daya kowacce lita a kasuwar duniya.
A ranar 15 ga watan nan ne Cibiyar Hadahadar Kasuwanci ta Duniya WTO za ta sanar da Okonjo Iweala a matsayin shugabar cibiyar a hukumance.
An rada wa jami’ar jihar Bauci sunan Sa’adu Zungur.
Mu wayi gari kafiya.
Af! Allah Ka mana katangar karfe da kidinafas a duk inda muke Amin.

Exit mobile version