LITININ
Assalamu alaikum barkanmu da Juma’atu babbar rana. Za mu fara waiwayen kanun labarun daga litinin, uku ga watan Safar shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin Annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da daya ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin.
Allah Ya yi wa Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dafta Shehu Idris 1936 – 2020 rasuwa bayan wata jinya a asibitin sojoji na fotifo da ke nan Kaduna. Sarkin Zazzau mai shekara 84 a duniya shi ne sarki na goma sha takwas a jerinsu na fulani bangaren Malam Musa da suka soma sarauta a 1804. Shekara 45 Mai Martaba Sarkin Zazzau Shehu Idris ya yi yana sarauta. A ranar Lahadi aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.
Gwamnatin jihar Kaduna ta sanar da laraba 23 ga watan nan a matsayin ranar hutu a jihar Kaduna, don zaman makoki da addu’ar rasuwar Shugaban Majalisar Sarakunan jihar Kaduna Alhaji Dafta Shehu Idris da Allah Ya yi wa rasuwa.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa Farfesa Gambari da ya jagoranci mukarraban gwamnatin tarayya da suka wakilci shugaban kasa Buhari wajen jana’izar Mai Martaba Sarkin Zazzau, ya bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi.
Manyan ma’aikata, da sarakuna da ‘yan kasuwa manya da kanana, da talakawa da idon gari, da ‘yan uwa da abokan arziki na ci gaba da tururuwa zuwa gaisuwar ta’aziyyar rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dafta Shehu Idris.
Gwamna Obaseki na jam’iyyar PDP shi ne ya lashe zaben gwamnan jihar Edo da aka yi ranar Asabar, ya lika Ize-Iyamu na jam’iyyar APC da kasa da kuri’a dubu dari uku da bakwai, da guda dari tara da casa’in da biyar. Iyamu ya samu kuri’a dubu dari biyu da ashirin da uku, da dari shida da goma sha tara. Tuni Obaseki ya gode wa Shugaban Kasa Buhari da ya yi tsayin daka wajen tabbatar da an yi zabe na gaskiya, har ma Shugaban Kasan ya taya Obaseki murnar nasarar da ya samu.
Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na can suna ci gaba da kasancewa a killace. Shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Ga tsadar taki ga ambaliya. Ga gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawarin idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
‘Yan bindiga sun je Gobirawar Chali da ke yankin karamar hukunar Maru ta jihar Zamfara, sun tafi da mutane kusan hamsin, mutum dubu uku da dari biyar suka tsere daga gidajensu. Haka nan a Kasuwar Magani da ke jihar Kaduna wasu kidinafas sun yi kidinafin wasu mutane.
Ma’aikatan lafiya da ke yajin aiki na gargadi na kwana bakwai, sun janye yajin aikin, inda suka ce ana ta musu barazana.
Ma’aikatan kwalejojin ilimi na gwamnatin tarayya na ci gaba da yajin aiki a kan wasu bukatunsu har da ariyas na sabon albashi.
Ma’aikatan kwalejojin foliteknik da na kwalejojin ilimi da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin shekara daya da wata shida suna dakon ariyas na sabon albashi. Wasu malaman jami’a da ma’aikata ma na bin bashin albashin kusan wata hudu.
Af! Na san za a yi mamaki idan na ce sau daya na taba shiga Fadar Sarkin Zazzau a rayuwata. Ita ma na je dauko rohoto ne na nadin Iman Balele Wali a matsayin Limamin Masallacin Sarkin Musulmi Bello da ke Unguwar Sarki Kaduna shekarun baya da nake aiki da gidan talabijin na jihar Kaduna. Ikon Allah na manta shekarar kuma har kiran dan Imam Balele Wali wato Yusuf Balele Wali, da yake tare muka yi karatu a C.A.S. Zariya a 1986 zuwa 1988 a waya na yi, don ya tuna mun shekarar ya ce ya manta.
Allah Ya jikan Mai Martaba Sarkin Zazzau Dafta Shehu Idris, da sauran iyayenmu da suka riga mu gidan gaskiya Amin.
TALATA
Assalamu alaikum barkanmu da asubahin talata, hudu ga watan Safar, shekarar 1442 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Daidai da ashirin da biyu ga watan Satumba na shekarar dubu biyu da ashirin.
Jam’iyyar APC ta taya Gwamna Obaseki murnar sake lashe zaben gwamnan jihar Edo karkashin
Majalisar Dinkin Duniya na bikin cika shekara saba’in da biyar da kafuwa, inda Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya lasafto dinbin gudunmawar da Nijeriya ta bayar ga ayyukan majalisar, har da ayyukan wanzar da zaman lafiya a kasashen duniya da Nijeriya ta taka rawar gani.
Saboda matsin lambar ECOWAS sojojin Mali da suka yi juyin mulki sun nada tsohon ministan tsaron kasa wani BaNdado, Kanal mai ritaya a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya, shi kuma jagoran sojojin da suka yi juyin mulkin a matsayin mataimaki.
‘Yan sanda sun ceto sauran jami’an hukumar kiyaye hadurra su shida da suka yi saura a hannun kidinafas, da kidinafas din suka yi kidinafin su wajen ashirin da bakwai a jihar Nasarawa.
Hukumar yaki da rashawa ta jihar Kano na shirin gabatar da wasu tuhume-tuhumen da take yi wa Sarkin Kano Sanusi na biyu.
Malaman makaranta da iyayen yara sun yi zanga-zanga a jihar Kwara, ta nuna bacin ransu a kan ci gaba da rufe makarantu masu zaman kansu a jihar da sunan kwaronabairos.
Af! Gabadaya yinin Litinin, har zuwa karfe hudu na asubahin da na yi wannan rubutu, ina ta jiran wutar lantarki ta yi karfi in yi wani aiki, aiki kuma muhimmi amma kyandir ya fi ta kumari. Kuma ga kudin wutar an ninka ninkin ba ninki.
Af! Ga wani can yana tuna mun cewa in ce an ninka kudin zama a duhu dai.
LARABA
Hukumar Zabe ta Kasa INEC ta mika wa gwamna Obaseki takardar shaidar sake lashe zabensa.
Tsohuwar Shugabar Kasar Laberiya Ellen Johnson ta jinjina wa Rochas Okorocha da ke bikin cika shekara hamsin da takwas da ya yi a duniya.
Gwamnan jihar Barno Zulum ya sanar da gudunmawar naira miliyan ashirin da gida ga iyalan wani Birgediya Dahiru Bako, kwamandan wata runduna ta musamman ta ashirin da biyar da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kashe wani kwanton-bauna da suka yi wa sojoji a hanyar Demboa.
Wasu kidinafas sun kai hari a jihar Nasarawa suka kashe mutum guda, suka yi kidinafin mutum goma da ji wa wasu da dama rauni.
Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna na can suna ci gaba da kasancew a killace shekara da shekaru ba hanya. Wata da watanni ba wuta. Ga tsadar taki ga ambaliya. Ga gadar da sukan samu su hara ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan, Jaja, ya musu alkawari ifan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
Gwamnan Kaduna ya ba ma’aiktan jiharsa hutun aiki a Laraba,Gwamnan ya ba da hutun don ranar ce uku da rasuwar Mai Martaba Sarkin Zazzau Alhaji Dafta Shehu Idris. An ba da hutun don zaman makoki.
Af! Ga wadanda ke iya ganin hoton da na sa, aikin shinkafa ne wata mata ‘Yar Guibi ke yi.
ALHAMIS
Bari in fara da batun wutar lantarki da na dauka da aka kara wa talaka kudin zama a duhu za ta inganta ashe za a ci gaba da zaluntar talaka ne. Jiya tun da sassafe da aka dauke mana wutar, gabadaya har zuwa yanzun karfe hudu saura minti ashirin na goshin asubah da nake wannan rubutu babu wuta babu dalilinta. Kuma haka talaka zai biya kudin wannan zama a duhu idan wata ya kare kuma a zamanin mulkin masu tausayi da gaskiya. Kaico!
Gwamnatin Tarayya da kungiyoyin kwadago sun yanke shawarar tattaunawa a kan karin kudin zama a duhu da na mai da gwamnati ta yi.
Kungiyoyin Kwadago sun ce ba gudu ba ja da baya za a wayi gari da zanga-zanga ranar 28 ga watan nan don nuna wa gwamnati ba a yarda da karin kudin zama a duhu da na mai da gwamnati ta yi wa talakan da ke cikin wani mawuyacin hali ba.
Gwamnatin Tarayya ta amince za a yi titin dogo daga Kano zuwa Maradi ta kasar Nijar da gwamnati ta ce za ma a samu saukin jidar danyen mai don kaiwa a tace shi ta jiragen.
5. A alhamis din nan shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi kasar Guinea Bissau/Gini Bisau don halartar bikin zagayowar ranar samun ‘yancin kai na kasar.
Shugaban Kasa Buhari ya nuna kaduwarsa da bindigar da wata tankar mai ta yi a Lakwaja saboda matsalar birki, har fiye da mutum ashirin da uku suka riga mu gidan gaskiya.
Gwamna Zulum na jihar Barno ya cika alkawarin da ya dauka na bai wa iyalan Kanal Dahiru Bako kwamandan birged ta musamman da ‘yan Boko Haram suka kashe naira miliyan ashirin. Jiya laraba aka yi masa sallar jana’iza.
Ana cikin waiwayar rana ta musamman ta ishara a duniya wato International Day of Sign Language. Sannan mu a Nijeriya ana makon bebaye inda gwamnatin tarayya ta dau alkawarin kare hakkokinsu.
Af! Allah! Allah!! Allah!!! Ka agaza wa talakan Nijeriya ya daina biyan kudin wutar da bai sha ba, wato kudin zama a duhun ma ya yi tashin gwauron zabi. AMIN.