LITININ
Ministar jinkai Sadiya, da ta al’amuran mata Tallen sun raba wa mata su dubu dari da hamsin, naira dubu ashrin kowacce, tallafi na sana’a na Gwamnatin Tarayya a jihar Bauci.
Ana ci gaba da horas da sabbin ‘yan sanda kurata na musamman (Special Constable) a jihohi daban-daban na kasar nan, har a jiya aka gama horas da sabbin kuratan su dari takwas da saba’in da bakwa a jihar Edo, a jihar Imo kuwa su dari hudu. Har Obaseki ya fara ba na jiharsa aikin su danko masa fursunonin da suka tsere a lokacin zanga-zangar da aka yi.
Haka nan kidinafas sun tare hanyar Kaduna zuwa Abuja jiya, daidai Katari, suka harbi na harbi, suka yi kidinafin na kidinafin.
Haka nan ba a dade ba da kidinafas suka je Rigachikun ta jihar Kaduna, suka kashe mai juna biyu, suka tafi da mijinta. Haka nan ba a dade ba wasu ‘yan bindiga suke je yankin Ikara ta jihar Kaduna suka kashe wani mai gari. Haka nan ba a dade ba, makasa suka je Kidandan ta yankin Giwa ta jihar Kaduna, suka kashe mutane rututu, kuma har yau ba su kyale mutanen yankin sun sakata ba. Haka nan kidinafas na nan sun hana bin hanyar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, haka nan suna kokarin kwace hanyar Kaduna zuwa Zariya. mutanen yankin Zariya sabon Garin Zariya, da Zangon da ke kusa da Samarun Zariya, har da na gidajen jami’ar A.B.U duk da ke jihar Kaduna, ba su tsira daga kidinafas, da barayin shanu, da makasa ba. Haka ma yankin Mando da ke cikin garin Kaduna, kidinafas na kai musu ziyara. Na Mahuta da ke kusa da asibitin ido na Kaduna su ma ba sa iya rintsawa sosai. Haka nan yankin Kasuwar Magani, da ke jihar Kaduna, kidinafas na musu dauki dai-dai da kisan mummuke.
A yankin Dan Musa da Batsari na jihar Katsina, ‘yan sanda sun damke wasu ‘yan bindiga su goma sha biyar, da shanu da sauran dabbobi masu tarin yawa.
Sojoji sun dakile wasu hare-hare da ‘yan Boko Haram suka kai, har da na ‘yan ISWAP, suka damke wani mai kera musu bam a Arewa Maso Gabashin Kasar nan.
Da alamu mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna sun auka hannun ‘yan siyasa ‘yan wala-wala. Shekara da shekaru suna musu alkawarin hanya, har yau shiru. Gadar da sukan samu su haura ta karye. Gadar da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe. Idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.
Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da a kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na gwamnatin tarayya, na ci gaba da korafin idan Allah Ya kai mu, sun cika shekara biyu ke nan, suna dakon ariyas na sabon albashi.
TALATA
Kidinafas, da makasa da sauransu, na ci gaba da cin karensu ba babbaka a jihar Kaduna. Gwamnatin jihar Kaduna ta ce sojoji sun ce sun ceto mutum tara da Kidinafas da suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja suka yi kidinafin shekaranjiya. Sai dai kidinafas din sun kashe wani direba da fasinja. Mutum uku da kidinafas suka je kwalejin foliteknik ta Nuhu Bamalli da ke Zariya har suka harbi wani ne dai ba a ji inda suke ba. To a shekaranjiya da daddare wasu kidinafas sun auka Marabar Kajuru ta jihar Kaduna, suka kashe na kashewa, suka yi kidinafin na kidinafin. Sai jiya da rana tsaka kata. Wasu ‘yan bindiga, suka je wani kauye Albasu, da ke Sabon Birni a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, suka kashe mutum goma, wata ruwayar ta ce mutum goma sha daya.
Ministan Kwadago Ngige, ya ce har yanzun ba su gama gwada sahihanci da ingancin tsarin biyan albashin nan na UTAS da malaman jami’a suka kirkiri abin su, suka ce sun fi amince masa fiye da IPPIS da gwamnati ke kokarin kakaba musu, da suka ce tattare yake da kuskure da cutarwa gare su ba. Da ke nuna alamun babu ranar komawa makaranta ga daliban jami’a.
Sabbin ‘yan sanda sun shaida wa BBC Hausa cewa, watansu shida ke nan ba albashi, da korafin saboda Allah in ba hanci suka ci ba, ya ake so su yi?
Wasu masu zirga-zirga hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun ce kwana bakwai a jere, kullum sai kidinafas sun tare hanyar da karfe bakwai zuwa takwas na safe, su yi dajin da mutane.
Mutanen Zariya sun ce ba fa za su ci gaba da zura hajar mujiya kidinafas na cin karensu babu babbaka a ciki da wajen Zariya ba. Alhali ga su da makarantu na manyan sojoji da kanana a ciki da wajen Zariya, ya zama ga koshi ga kwanan yunwa.
Hukumomin ‘yan sanda sun ce sun kama ‘yan sandan da suka kashe mutum biyu a Sharada ta jihar Kano, kisan da ya haddasa wata zanga-zanga, har kungiyar Aminasti ta yi tir da kisan.
Mutane biyu ‘yan Nijeriya da ke kasuwanci a Ghana, suka yi barazanar za su kashe kansu da kansu saboda takaicin cin zarafin da ‘yan Ghana ke musu a can.
Shugaban ‘yan sandan Nijeriya, ya ki amincewa da takardun barin aiki da jami’an ‘yan sanda ke ta mikawa.
Wani kamfanin na magunguna a Amurka ban da su Fzer, ya yi nasarar kirkiro rigakafin kwarona, da ya fi na su Fzer karfi. An yi gwajin maganin a mutum dubu talatin. Har yanzun ana matakin gwaji ne.
LARABA
Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani Hakimi da dansa, a kauyen Gidan Zaki, da ke yankin karamar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna.
Makasa sun je Kauyen Albasu da ke Sabon Birni a yankin karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna, suka kashe mutum goma sha biyu.
Makasa sun je yankin Ikara ta jihar Kaduna, sun kashe wani Mai Gari suka yi tafiyarsu.
Kidinafas sun je Rigachikun ta jihar Kaduna, suka kashe wata mai juna biyu, suka yi kidinafin mijinta.
Makasa sun je Kidandan da ke yankin Giwa ta jihar Kaduna, suka kashe mutane rututu kuma har yau ba su kyale su ba.
Al’umomi da ke kusa da tashar jiragen sama ta Kaduna, da na kusa da kwalejin horas da kananan hafsoshin soja NDA sun ce nan wuraren kidinafas suka fi sakata su wala.
Masu motocin sufuri zuwa Birnin Gwari sun ce hanyar ta zama tarkon kidinafas.
Mutanen yankin Sabon Garin Zariya da ke jihar Kaduna, sun ce kauyakunsu sun zama tungar barayin shanu.
Mutanen Mando da wuraren aisanta da ke cikin garin Kaduna, su ma sun ce da ido daya suke bacci.
Daga Kudan ma ta jihar Kaduna, labari ne na an yi kidinafin wasu mutanen garin.
Mu wayi gari lafiya.
Af! A ranar Laraba kuwa aka fara kamen masu motoci da takardunsu suka kare aiki, ko lasisinsu ya kare aiki, ko suke amfani da tsohuwar lamba a jihar Kaduna.
Ni dai ina da komai amma lambata tsohuwa ce. Idan kun ji an yi ram da ni to lamba ce. Ga ta da dan karen tsada. Amma harajin nan na naira dubu daya da kowanne baligi da ke jihar Kaduna zai soma biya, sai watan jibi tukuna.
ALHAMIS
A yanzun Nefa sun rage yawan awoyin da suke ba mu wuta. Karfe 12 na dare na yi za a dauke, sai karfe uku da rabi da minti takwas na goshin asubah kamar yadda suka yi lokacin da nake zaune nake wannan rubutu, su dawo da ita. Can wuraren karfe takwas ko tara na safe su dauke, sai kuma, can wuraren karfe biyu ko uku su dawo da ita. In ba a yi sa’a ba karfe biyar su dauke, sai kuma goshin magriba su dawo da ita. Sannan mu kwana uku da wuta, kwana daya babu. Ga wutar ba karfi, da in kana da mitar iya-kudinka-iya-shagalinka mitar ba ta nunawa saboda wutar ba karfi.
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya ce in Allah Yarda ba za a sake yin makamanciyar zanga-zangar tir da halayen ‘yan sanda ba.
‘Yan sanda masu mukamin ASP su goma sha biyu kidinafas suka yi kidinafin a kan hanyarsu ta Barno zuwa Zamfara, inda kidinafas din suka nemi sai an ba su naira dubu dari takwas kowanne dan sanda. Wato naira dubu dari takwas sau goma sha biyu ke nan.
Kidinafas da suka yi kidinafin daliban jami’ar Ahmadu Bello Zariya, su tara a hanyar Kaduna zuwa Abuja, sun nemi sai an ba su jimillar naira miliyan 270 kafin su sako yaran.
Da alamu sai shekara mai zuwa, Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tattaunawa da malaman jami’a a kan yajin aikin da suke yi. Daliban jami’a ba batun komawa ke nan yanzun.
An raba naira biliyan dari shida da ‘yan kai tsakanin Gwamatin Tarayya, da Gwamnatocin Jihohi, da Gwamnatocin Kananan Hukumomi na watan Oktoba, da ke nuna an kusan soma jin dilin-dilin ga masu samu da wuri ke nan.
Kotu ta ba da umarnin a kamo mata Maina. Mainan nan fa da ake ta tirka-tirka da shi a kan zargin wasu kudade na fansho.
Dan autan Fela, Seun ya farfado da jam’iyyar mahafinsa ta Mobement of the People.
Af! Da yake a karshen rubutuna na Laraba, na tabo batun kamen masu takardun mota da suka kare aiki, da wadanda lasisinsu ya kare aiki, da masu tsohuwar lamba ire-irena, da aka soma a fadin jihar Kaduba, wani ya yi tsokaci kamar haka:
“Mal. Guibi, ni Ina ganin kafin a Kama motocin mutane dake da tsohuwar lamba, kamata ya yi su fara da motocin gwamnati. Domin kuwa kashi 99 cikin 100 na motocin gwamnatin Jihar Kadunan, duk su na dauke da tsofaffin lambobi ne. Na biyu, ba Kotu ta hana tilastawa ‘yan Kasa sayen wannan lambar ba, aka ce kowa ya na da ikon amfani da lambarsa? Na uku, sayar da lambar ba aikin Road Safety ba ne? Me ya sa gwamnatin Jihar Kaduna ta karbe wannan aikin daga FRSC? Ita gwamnatin Tarayya ba ta bukatar kudaden shiga ne?”
Wani kuma ya kara da cewa ya za a yi da masu motoci na wasu jihohi da ke bi ta Kaduna su wuce, da su a johinsu ba a hana amfani da tsohuwar lambarba?
Wani kuma ya ce me ya sa ita gwamatin jihar Kaduna ta fi damuwa da abin da za ta samu a hannun jama’a ba kare su daga kidinafas da makasa da barayin dabbobi da ke cin karensu babu babbaka, musamman a ‘yan kwanakin nan a jihar Kaduna ba?