Connect with us

Waiwayen Kanun Labarai

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 4 Zuwa Alhamis 7 Ga Ramadan 1441, Bayan Hijira

Published

on

Litinin
Kwamitin shugaban kasa a kan cutar kwaronabairos, ya mika wa shugaban kasa rahotonsa, da shawarwari a cikin rahoton, da ya rage ga shugaban kasa ya yanke shawara a kan sabon mataki na gaba da zai dauka yau, tunda yau mako biyun da ya kara na kulle a jihar Legas da Abuja da jihar Ogun ke karewa.
Sojoji sun kashe ‘yan bindiga guda tamanin da takwas a jihar Zamfara , suka ceto mutum biyar da shanu masu yawan gaske.
‘Yan sanda a jihar Kaduna sun kamo wadanda suka yi kidinafin dan darikar katolikan nan kwanakin baya, suka kuma kashe shi a Gwanin Gora.
Gwamnatin jihar Kano ta ce bayanai daga ma’aikatar lafiya ta jihar na cewa mutum daya ne ta san ya riga mu gidan gaskiya sakamakon cutar kwaronabairos, sai mutum saba’in da bakwai da ya harbu. Ta ce bayanai na farko na nuna cututtuka irin su maleriya, da ciwon siga, da hawan jini da sankarau ne suka yi sanadiyyar mace-macen da ake ta gani a jihar. Gwamnatin ta ce tana jiran rahoto na karshe daga ma’aikatar ta lafiya. Sai dai PDP ta nemi shugaban kasa Muhammadu Buhari ya hanzarta ya leka Kano da gaggauta bincike, ita kuwa APC ta zargi PDP da kokarin karkatar da jama’a a kan mace-macen.
Ana nan ana neman wasu mutum biyu da suka harbu da cutar kwarobairos a jihar Barno ruwa a jallo saboda ranta a na kare da suka yi.
Gidauniyar BUA ta ba jihar Kano gudunmawar kudi naira biliyan uku da kusan rabi don taimaka mata a matsalolin da suka shafi kwaronabairos.
Gwamnatin jihar Filato ta mayar da almajirai dari da tamanin da uku jihohinsu na haihuwa. Haka nan an mayar da almajirai guda dari biyar Jigawa daga jihar Kano.
Gwamnatin jihar Kaduna ta rage kwana biyu talata da laraba da ta yarda jama’ar jihar su dinga fita daga kullen da ta tilasta musu, a yanzun laraba kawai za su dinga fita har tsawon kwana talatin. Haka nan ‘yan siyasa da ke rike da mukamai na jihar, da ma’aikatan gwamnati musamman masu daukar albashi mai gwabi-gwabi, za a zaftare musu wani abu daga albashinsu a matsayin tasu gudunmawar ga yaki da cutar kwaronabairos. A duba can sashena na karshe na ‘AF’ na wannan rubutu, domin ganin cikakkiyar sanarwar ta gwamnatin jihar Kaduna, sai dai cikin harshen Ingilishi ce.
Ma’aikata na ci gaba da korafin an tilasta musu kulle, an hana su dilin-dilin.

Talata

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya sanar da karin mako guda a kullen da aka tilasta wa mutanen jihar Legas, da jihar Ogun da Babban Birnin Tarayya Abuja. Sun soma da kullen mako biyu, da ya kare, ya sake sa musu mako biyu, da ya kare ya kara musu kullen na mako guda, yana karewa hudu ga watan gobe na Mayu za a dauki matakan sassauta kullen. Ita kuma jihar Kano shugaban kasa ya sanar da kakaba mata kulle na mako biyu ba shiga ba fita. Duk saboda yakar yaduwar cutar kwaronabaoros. Sauran matakan da shugaban kasa ya ce za a dauka nan gaba, za a kyale zirga-zirga na cikin jiha amma ban da tsakanin jiha da jiha. Babu taruka na addini ko zamantakewa. Ya kuma yi gargadi a kan yadda jami’an tsaro ke kashewa ko cin zarafin talaka wajen tilasta masa kulle.
Gwamnatin jihar Kaduna ta canza shawara, ta ce a yanzun jama’a na iya fita daga kulle ranar laraba, da ranar asabar, karfe goma na safe zuwa karfe hudu na la’asar don kalato abin da za a ci na kwanakin kullen. Ta ce za a samar da ‘yan kasuwanni na wucin gadi a kowacce unguwa, na kayan abinci da magunguna, da sauransu da suka zama wajibi ga jama’a don magance barin unguwa nema.
Ma’aikatan gwamnati na jihar Kaduna sun yi korafin, a kasa da sa’a goma sha biyu da fitar da sanarwar za a zaftare musu wani kaso na albashinsu a matsayin tasu gudunmawar ga yaki da cutar kwaronabairos, sai ga dilin-dilin na wannan watan, wasu an yanke musu dubu dari, wasu dubu tamanin, wasu dubu sittin, wasu dubu arba’in, wasu dubu ashirin. Daidai kurji daidai ruwa. Wasunsu suka ce ashe an ma riga an yanke sannan aka fitar da sanarwar don kada gari ya waye mutum ya ga albashi bai cika ba ya soma tambaya.
Almajirai dari bakwai jihar Gwambe ta mayar jihohinsu na asali guda biyu.

Laraba

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya tattauna da Shugaban Amurka Donald Trump a kan yadda Nijeriya ke bullo wa cutar kwaronabairos ta bayan gida, da alkawarin taimaka wa Nijeriya da na’urorin nan da jami’o’inmu suka soma kerawa, masu taimaka wa mai lalurar kwaronabairos numfashi VENTILATORS.
Majalisar Dattawa da ta Wakilai bayan duk sun koma aiki, ta dattawan ta bukaci Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha da Ministan Lafiya da sauran mukarraban kwamitin da shugaban kasa ya kafa a kan cutar kwaronabairos, su gurfana a gaban majalisar don jin dalilan da suka sa ake ta mace-mace a jihar Kano. Haka nan ita ma Majalisar Wakilai ta yi nata yunkurin a kai. Duk sun soma yi wa kudirori daban-daban na kwarona karatun mayar da su doka.
3. Wakilan Gwamnatin Tarayya sun isa jihar Kano don bin bahasin mace-macen da ake yi da suka daure wa jama’a kai.
4. Majalisar Wakilai ta yi tir da harin da ake kai wa ‘yan Nijeriya a kasar Sin Caina, da neman a tarkata ‘yan Caina da ke zaune a Nijeriya ba da izini ba, a mayar da su kasarsu.
5. Gwamnatin tarayya ta ce daga litinin za ta soma dawo da ‘yan Nijeriya da ke kasashen waje, suke bukatar dawowa gida Nijeriya.
6. Majalisar Dattawa ta amince wa Shugaban Kasa ya ci bashin naira biliyan dari takwas da hamsin daga cikin gida Nijeriya, wanda da ma yana cikib kasafin 2020 don gudanar da ayyuka na raya kasa.
7. Gwamnan Ekiti ya kwaikwayi na jihar Kaduna shi ma ya ba da umarnin yanke rabin albashin duk wani mai rike da mukamin siyasa don anfani da kudin wajen yakar cutar kwaronabairos.
8. Kungiyar kwadago ta kasa ta gargadi masu yanke wa ma’aikata albashi da sunan yaki da cutar kwaronabairos su daina.
Hukumar wutar lantarki na ci gaba da yi wa talaka yankan kauna. Buda baki a duhu, sahur a duhu, yinin kulle ba wuta, ga sauro ga zafi ga cututtuka.
Gwamnatin jihar Kaduna ta ce almajirai biyar da aka dawo da su daga Kano na cikin sabbin wadanda aka gano sun harbu da cutar kwaronabairos.
An ceto wata mata ‘yar Nijeriya da wani dan kasar Siriya da ke Labanan ya yi tallar neman mai sayenta a fesbuk a dala dubu daya. An kuma kama shi.
Cibiyar yaki da yaduwar miyagun cututtuka ta kasa NCDC ta ce za ta yi wa mutum miliyan uku gwajin cutar kwaronabairos cikin watanni uku masu zuwa a kasar nan.
Wasu mahara da suka ji zafin farmakin da sojoji suka kai musu a Sabon Birnin Gobir da ke jihar Sakkwato, sun yi ramuwar gaiya sun tayar da kauyuka tara, inda mutanen kauyukan suka fantsama Nijar neman mafaka.

Alhamis
Wasu ma’aikatan gwamnatin tarayya na korafin sai suna ganin kamar ana raina Baba Buhari ta kin bin umarninsa. Suka ce in ba raini ba, ta ya tun wuraren 23 ga watan nan ya ce a hanzarta biyan ma’aikata, da malaman jami’o’i albashi saboda halin da aka shiga na kwaronabairos, amma yau watan ya kare gobe za a shiga watan Mayu ba amo ba labari? Suka ce in lokacin Obasanjo ne, wani ya isa Obasanjo ya ba da umarni a ki bi sai an ga dama?
Buhun shinkafa dari biyar kwastam ta kama da aka shigo da ita ta barauniyar hanya a Legas.
Ranar litinin mai zuwa za a bude bankuna da ofisoshi na ma’aikatu da ke fadin kasar nan, amma ban da makarantu. Za a bude tare da kiyaye sharuddan hana yaduwar cutar kwaronabairos a cikin jama’a. Su kansu ma’aikata da za su fita aiki ba kowa ne zai fita ba, akwai matakin albashi. Dokar tilasta kullen za ta dinga aiki daga karfe takwas na dare zuwa karfe shida na safe, kuma babu zirga-zirga daga jiha zuwa jiha.
Gwamnatin tarayya ta raba wa wasu jihohi ashirin da hudu naira biliyan arba’in da uku da kusan rabi tallafi daga Bankin Duniya.
Kotu ta yi watsi da bukatar belin Maina da ake zargin ya wawure wasu makudan kudi na fansho.
An mayar da almajirai guda dari da ashirin daga jihar Gwambe zuwa jiharsu ta Yobe.
A jihar Kaduna ‘yan sanda sun kama a kalla mutum dari takwas da tamanin da shida da suke zargin sun saba wa dokar hana yada cutar kwaronabairos, aka gurfanar da arba’in da takwas da ake zargin gaban kotu, da yawancinsu masu gidajen barasa ne, da shugabannin wuraren ibada. Har ila yau a jihar ta Kaduna a yankin Kafanchan an yi wa wani bulala goma, da daurin wata biyu saboda satar kwamfuta laftab/Laptop. Sannan a titin kwansitushan da ke cikin garin Kaduna an yi gobara a wasu shaguna kusan ashirin.
Kungiyar kwadago ta jihar Kaduna ta ce ba ta yarda da taba wa ma’aikata albashi da gwamnatin jihar Kaduna ta yi ba, ko a mayar wa ma’aikata kudinsu ko su kai ruwa rana da gwamnati.
Ma’aikatan wuta na nan suna ci gaba da raba takardar a je a biya kudin wuta. Ba zan ce kudin zama a duhu ba tunda wasu unguwanni sun ce ba laifi su ana ba su wuta. Mu dai a tamu unguwar ko in ce yankin, kudin zama a duhu za a je a biya. Amma ai sun ce za su daga kafa ba yanka saboda halin da ake ciki. Shan wuta kyauta har tsawon wata biyu labarin ya zama na kanzon kurege.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: