Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home Waiwayen Kanun Labarai

Waiwayen Kanun Labaru: Daga Litinin 6 Zuwa Alhamis 9 Ga Jimada Ula 1442, Bayan Hijira

by Muhammad
December 25, 2020
in Waiwayen Kanun Labarai
6 min read
Kanun Labaru
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

LITININ

Gwamnatin jihar Kaduna ta umarci ma’aikatanta kasa da matakin albashi na 14, kada su je aiki daga Litinin, su zauna gida suna gudanar da ayyukan nasu daga gidan saboda kwaronabairos.

Majalisar Dinkin Duniya, da Iweala shugabar hukumar kasuwanci ta duniya, sun yaba wa kokarin da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi wajen ceto yara ‘yan makarantar sakandare ta Kankara.

‘Yan sanda tare da hadin gwiwar ‘yan sintiri sun ce sun yi nasarar ceto yara ‘yan makaranta su 84 da suka je taron maulidi, kidinafas suka kwashe su, su a karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina. Sun kuma kwato shanu 12 da ‘yan bindigan suka sace.

Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum a kalla uku, suka kona gidaje da kidinafin wani mai gari, a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja.

Dakaru sun ce sun kashe ‘yan bindiga biyu, suka kama daya, a Katsina-Ala ta jihar Binuwai.

Hukumar Kula da al’amuran ‘yan sanda ta kasa ta kori wasu manyan ‘yan sanda su hudu saboda aikata ba daidai ba, da rage wa wasu biyu mukami, da tsare wasu hudu.

Hukumar kula da al’amuran masu shari’a ta kasa NJC, ta ba da shawarar a yi wa wasu masu shari’a su biyu ritaya saboda tabka karya a shekarunsu na haihuwa.

Wasu daga cikin yaran da aka ceto na makarantar sakandare ta Kankara, sun ce sai da aka biya kudin fansa aka sako su.

Sanata Ndume ya tunatar da Shugaban Majalisar Dattawa, da sauran ‘yan majalisar, cewa su ji tsoron Allah, su tuna cewa su ne shugabannin jama’a, kuma sai Allah Ya tambayi kowannensu, a kan rayukan ‘yan Nijeriya da ake ta kashewa ba abin da suka yi.

Mutanen Buni Yadi da Boko Haram ta dade da raba su da gidajensu, sun yi korafin ba sa iya kai wa ga gonakinsu.

An kashe a kalla mutum uku a wani sabon harin da aka kai a yankin karamar hukumar Zangon Kataf, ta jihar Kaduna.

Malaman jami’a na ci gaba da korafin Gwamnatin Tarayya suke jira ta nuna da gaske take yi, sai su ma su nuna da gaske suke yi, ko dalibai sa samu su koma makaranta da gaske.

Mutanen kauyen Guibi da ke yankin karamar hukumar Kudan ta jihar Kaduna, na ci gaba da godo da shugaban karamar hukumar Kudan na yanzun, Jaja, ya je ya cika musu alkawarin gyaran gada, da ya musu alkawari a lokacin yakin neman zabe, cewa idan sun zabe shi zai gyara musu. Sun zabe shi, har wa’adinsa na shirin karewa bai gyara musu ba.

Ma’aikatan kwalejojin foliteknik, da na kwalejojin ilimi, da na jami’o’i duk na Gwamnatin Tarayya, na ci gaba da korafin suna shirin cika shekara biyu suna dakon ariyas na sabon albashi.

Af! Na lura da wata sabuwar tsirfa a fesbuk. Sai ka ga mace wai ita budurwa ce ta sa hotonta wai tana neman mijin aure har da rantsuwa, amma in kana sonta da aure, wai sai ka yada hotonta zuwa gungun mutane na soshiyal midiya a kalla biyar, sannan wai ka tura mata lambarka ta amince ta aureka. To a yi hattara. Babu mamaki ma gardi ne kidinafa.

 

 

 

 

TALATA

 

Gwamnatin Tarayya ta ce wadanda ba su iya hada lambarsu ta shaidar dan kasa da layinsu na waya ba, an kara musu har zuwa 19 ga watan gobe. Wadanda kuwa ba su ma da lambar shaidar dan kasa, an ba su har zuwa 9 ga watan Fabraru, su je su yi rajistar ta dan kasa, su kuma hada lambar ta dan kasa da layin wayarsu.

Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun amince da kasafin kudin shekarar 2021 na Naira Tiriliyan kusan 14.

Gwamna Zulun na jihar Barno ya ce gaskiya sojoji da ‘yan sanda da aka tura kare rayuka a jiharsa sun ba shi kunya. Ya yi zargin ba abin da suka iya sai sa shingen bincike suna karbar taro sisi da kwandala a hannun masu ababen hawa, amma ba sa iya kare su daga hannun kungiyar Boko Haram a jihar.

Sojojin sama sun ce sun samu karin wata nasarar ta lalata motocin yaki da kashe mayakan Boko Haram da dama a dajin jihar Barno.

Wani rahoton na cewa sojoji biyar aka kashe a wani harin na Boko Haram a jihar Barno.

Gwamnatin Tarayya ta ba da umarnin rufe makarantu, har sai sha 18 ga watan gobe, saboda kwaronabairos. Ta kuma bukaci a dinga rage cunkushewa waje guda har fiye da mutum hamsin a lokaci guda, a bukukuwa ko suna ko wuraren ibada.

Af!

Talaka na ci gaba da biyan kudin zama a duhu. Wutar a kullum sai kara tabarbarewa take yi. Ba a ba ka wutar ba, wata ya kare a kawo maka takardar kusan naira dubu talatin, ka je ka biya kudin zama a duhu.

 

 

LARABA

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi rahoto daga kwamitinsa na sa ido a kan kwaronabairos PTF a takaice, inda ya kara wa kwamitin wa’adin wata uku don ganin yadda sabuwar cutar za ta kasance.

Gwamnatin Tarayya ta bukaci ma’aikatanta na gwamnati da ke matakin albashi na goma sha biyu zuwa kasa, su tsahirta da zuwa aiki, su dinga gudanar da aikin daga gida, nan da mako biyar a ga yadda za ta kasance da sabuwar cutar kwaronabairos.

Sojojin sun ce babu gaskiya a zargin da Gwamna Zulum ya musu cewa suna sa shinge suna karbar taro-sisi-kwandala, su da ‘yan sanda, maimakon kare rayukan mutanen jihar Barno.

Kungiyar gwamnonin Nijeriya ta je ta yi wa Gwamnan Jihar Katsina Masari kaico-kaicon abin da ya auku na yara ‘yan makarantar sakandare ta Kankara, tare da alkawarin za su nuna da gaske suke yi wajen shawo kan matsaloli musamman kidinafin da sauransu.

Gwamnonin jihohin tsakiyar Nijeriya sun taru a Makurdi ta jihar Binuwai domin lalubo bakin zaren magance matsalar tsaro irin su kidinafin da sauransu da ke addabar jihohin.

Daliban jami’a ‘yan mata da suka gaji da zaman jiran ranar komawa makaranta, na ta yin aure abin su, wanda ya sa in aka lura auren ya karu a wuraren karshen shekarar nan. Don na ga ‘yan matan na ta rubutawa a soshiyal midiya cewa su fa tunda ba makaranta aure suke so.

Jihar Kogi ta tsere wa Legas bangaren masu zuwa su zuba jari, a watanni uku na karshen shekarar nan. Ga wani can yana cewa Yahya Bello ba ruwansa da kwaronabairos shi ya sa ake tururuwa jiharsa zuba jari.

Wasu kidinafas sun kashe wani dan sanda da ya yi kokarin ceton wasu mutum biyu da kidinafas din suka yi kidinafin a kauyen Bosuwa da ke Maigatari a jihar Jigawa.

A jihar Kaduna an kashe mutum bakwai, aka sace uku a wani sabon hari.

Af! Ina talakan Nijeriya? Ka tuna tsine wa su Jonathan da Namadi Sambo har da kafirta duk magoya bayansu a lokacin yakin neman zaben 2015 da ka yi? Ka manta har jifarsu da kona gidajen magoya bayansu ka yi?

Ka lura a yanzun Jonathan ke wakiltar shugaban kasa a sabgogi daban-daban na kasashen waje? Ko a jiya na ga Jonathan a fadar shugaban kasa ya je ya isar da sakon aikensa da shugaban kasa ya yi kasar Gambiya. Shi ma Namadi Sambo ya je fadar shugaban kasa jiya don isar da sakon aikensa da shugaban kasa ya yi Nijar.

 

 

ALHAMIS

Malaman jami’a sun sanar da sun dakatar da yajin aikin da suka kwashe wata tara suna yi. Dakatarwa da sharadin idan gwamnati ta saba musu alkawari, za su ci gaba da yaji ba tare da sun ba da wani notis ko gargadi ba. Sun ce a yanzun ya rage ga shugabanni jami’o’i da gwamnati su sanar da dalabai ranar da za su koma makaranta, su dai malamai daga yau sun koma aiki. Na ma ga wasu jami’o’i irin su ta Gwamnatin Tarayya da ke Dutsin-ma a jihar Katsina sun fitar da sanarwar an ci gaba da karatu daga yau.

Ana ta muhawara a kan kalaman da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi cewa Allah ne kadai Zai iya magance matsalar da ke tattare da kan iyakar Nijeriya da Nijar. Inda wasu ke cewa gazawa ce karara shugaban kasa ke nunawa.

A hanyar Okene zuwa Lakwaja wata mota ta yi hadari mutum goma sha biyar suka riga mu gidan gaskiya.

A jihar Kwara wata tankar mai da ke mugun gudu ta kwace ta fadi, ta yi sanadiyyar mutuwar mutum shida, gidaje fiye da talatin suka kone, da shaguna fiye da arba’in.

A hanyar Kaduna zuwa Abuja, wata motar daukar kaya, saboda mugun gudu da rashin kyawon hanyar, ta kwace wa direban ta fadi, ta yi sanadiyyar mutuwar mutum goma sha biyu, ashirin da biyar suka ji rauni.

Kidinafas sun je Minjibir ta jihar Kano, an ce gaskiya jami’an tsaro sun fafata da su, duk da haka sun tafi da wani mai hali a garin.

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron majalisar zartaswa na karshe a wannan shekarar, har an fitar da wasu ayyuka.

Af! Ga rahoton da aka turo mun jiya da daddare daga yankin Giwa ta jihar Kaduna:

” Abinda ya faru yau kenan a garin Galadimawa da wasu mahara suka Kawo hari makamancin Abinda ya faru a Kidandan inda harin yayi sanadiyar mutuwar mutum biyu/uku da raunata wasu da kuma Tarawatsa kasuwa kasancewar yau kasuwar garin keci.

Bugu da kari sum kona Babban mota ta daukan kaya wato Daf/Triller da wata karama ta hawa akan hanyar Gwar-gwaje zuwa Birnin Gwari a nan kusa da Garin Kidandan dake yankin Giwa ta Yamma Kaduna state

Haka zalika sum kuma kewaye garin da manyan Makamai suna ta harbe-harbe. Ta ko inna a fili babu wani jamiin tsaro da ya Kawo wani dauki har ya zuwa wnn. Lokaci..

Daya daga cikin Wanda suka kashe shine Commander JTF na Yankin Iyatawa, Kidandan Ward, Giwa LGA Kaduna”

Af!! Wasu na zargin ana biyata ne a kullum nake rubuta alkaluman kwaronabairos. To ni ba wanda ya taba ba ni ko kwandala. Amma idan akwai wanda zai mun hanya a dinga kason kudin da ni, to ba matsala.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Yaren Fula Da Abin Fa Ya Shafi Kiwon Dabbobi A Tsakanin Fulani

Next Post

Ta’aziyya Tare Da Jinjina Ga Marigayi Sam Nda-Isaiah (II)

RelatedPosts

Labarai

Daga Litinin 29 Ga Watan Sha’aban 1442 Zuwa Alhamis 3 Ga Watan Ramadan 1442

by Muhammad
13 hours ago
0

LITININ Yau za a fara duban jinjirin watan Ramadan,  idan...

Waiwayen Kanun Labarai: Daga Litinin 22 Zuwa 25 Ga watan Sha’aban 1442 Bayan Hijira

Waiwayen Kanun Labarai: Daga Litinin 22 Zuwa 25 Ga watan Sha’aban 1442 Bayan Hijira

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Litinin Obasanjo da Dafta Gumi, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya, ta...

Waiwayen Kanun Labaru Daga Litinin 8 Zuwa Alhamis 11 Ga Sha’aban 1442 Bayan Hijira

Waiwayen Kanun Labaru Daga Litinin 8 Zuwa Alhamis 11 Ga Sha’aban 1442 Bayan Hijira

by Sulaiman Ibrahim
3 weeks ago
0

Daga Dandalin Idris Ishak Gulbi LITININ Shugaban Kasa Muhammadu Buhari,...

Next Post
First Bank

Ta'aziyya Tare Da Jinjina Ga Marigayi Sam Nda-Isaiah (II)

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version