Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Waiwayen Kanun Manyan Labarai: Daga Juma’a 13 ga Sha’aban 1440 (19/4/2019)

by
3 years ago
in Uncategorized
6 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Masu karatu barkan mu da yau Juma’atu Babbar rana. Kamar yadda kuka sani a kullum burinmu a Jaridar LEADERSHIP A YAU JUMA’A, bai wuce zakulo muku muhimman al’amura da za su ilmantar, wayar da kai, fadakarwa da kuma nishadantar da ku ba. Bisa hakan, za mu rika kawo muku bitar Kanun Muhimman Manyan Labarun abubuwan da suka auku daga Juma’ar da ta gabata zuwa Alhamis na wannan makon daga dandalin mashahurin marubucin nan kuma masanin harshen Hausa, Malam Is’hak Idris Guibi. Da fatan za ku ji dadin sabon filin namu tare da gamsuwa.
Edita

Assalamu alaikum barkanmu da yau Juma’atu babbar rana, goma sha uku ga watan Sha’aban shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da goma sha tara ga Afrilun 2019.

  1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sa hannu a kudirin sabon albashi mafi karanci na naira dubu talatin ya zama doka daga jiya goma sha takwas ga watan Afrilu. Dokar ta bai wa ma’aikaci damar kai kara kotu in ba a biya shi mafi karancin albashin ba, su kuma ma’aikatu ko kamfanoni masu zaman kansu, in har ma’aikantansu sun kai mutum ashirin da biyar, dole a biya su naira dubu talatin mafi karanci. In ma’aikatan ba su kai ashirin da biyar ba, to ba tilas.
  2. Kotun kula da da’ar ma’aikata ta yanke wa dakataccen babban mai shari’a na kasar nan, Walter Onnoghen hukuncin an kore shi daga mukaminsa na babban mai shari’a, da korarsa daga shugabancin hukumar kula da lamuran shari’a ta kasa, da karbe dukkan kudaden da ke cikin asusunsa na banki har guda biyar, da haramta masa sake rike wani mukami har sai bayan shekara goma. Sai dai Onnoghen na da zabin amincewa da wannan hukunci ko ya daukaka karar bai amince da hukuncin kotun ta da’ar ma’aikata ba. Wasu na cewa ya hango wannan hukunci shi ya sa ya mika takardar ya sauka kwanakin baya, amna shugaban kasa ya ki karbar takardar ajiye aikin nasa. Saboda, da shugaban kasa ya karba, da Onnoghen ya sha. Wasu kuma na zargin tuntuni gwamnatin tarayya ta yanke masa wannan hukunci, ba a dai sanar ba ne sai jiya.
  3. Sojoji da ke rawar soja ta ‘Yancin Tafki sun kashe wasu ‘yan bindiga su wajen talatin da tara a jihar Zamfara.
  4. Sarakunan Zamfara sun sanar da sunayen bayin Allah maza da mata da suke zargin sojojin sama sun kashe alhali ba su ji ba, ba su gani ba, a hare-hare da farmaki da sojojin ke ci gaba da kai wa ‘yan bindiga da kidinafas.
  5. Sanata Shehu Sani ya yi korafin lauyan da hukumar zabe ta kasa INEC ta dauko a batun shari’un korafe-korafen zabe, lauyan gwamna Nasir El-Rufai ne.

Asabar 14 ga Sha’aban 1440 (20/4/2019)

Labarai Masu Nasaba

Har Yanzu Messi Ya Fi Kowa Daukar Albashi A Tamaula

Dakarun MNJTF Sun Yi Barin Wuta Kan ‘Yan Boko Haram Sun Kashe 300 A Tafkin Chadi

Assalamu alaikum barkanmu da yau Asabar, goma sha hudu ga watan Sha’aban, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin ga Afrilun 2019.

  1. Sojojin sama sun kamo wani kidinafa, da ceto wanda ya yi kidinafin a Kaduna.
  2. A jihar Adamawa an kai wa al’umomi uku hari, aka kashe mutum a kalla goma sha biyar, iyalai fiye da dari suka rasa matsuguni. Mutanen kauyen Bolon sun yi zargin fulani ne suka kai musu harin.
  3. A jihar Taraba, Jukunawa da Munci sun sake bai wa hammata iska har mutum biyar aka kashe.
  4. A jihar Zamfara sojoji da ke rawar soja ta sharar daji sun kashe ‘yan bindiga bakwai. Sai dai na ji a shirin Ra’ayi Riga na BBC Hausa na jiya da daddare cewa, har yanzun ana ci gaba da kashe talakawan jihar Zamfara da kidinafin, da biyan miliyoyin naira don karbar kudin fansa. Zamfarawa sun yi korafin sojojin na kin zuwa inda kidinafas din suke, suna dogewa da cewa ba a musu umarni daga sama ba.
  5. Hukumomin sojan sama sun ce za su kaddamar da binciken zargin da sarakunan jihar Zamfara suka yi cewa sojoji na kai wa farar hula da ba su ji ba, ba su gani ba, hare-hare ta sama suna kashe su.

Lahadi 15 ga Sha’aban 1440 (21/4/2019)
Assalamu alaikum barkanmu da asubahin yau Lahadi, goma sha biyar ga watan Sha’aban shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da daya ga Afrilun 2019.

  1. Hukumar NJC da ke kula da al’amuran masu shari’a ta kasa ta amince da bukatar shugaban kasa, ta kara wa mukaddashin babban mai shari’a na kasa Muhammad Tanko wa’adin wata uku.
  2. Hukumar kula da da’ar ma’aikata CCB ta tunatar da duka masu rike da mukaman siyasa, zababbu ko nadaddu su bayyana kaddarorin da suka mallaka kafin su sauka. In sun ki, to ga misali nan a wajen Onnoghen.
  3. A wajen yawon bude ido da watayawa na yankin Kajuru da ke jihar Kaduna, wasu ‘yan bindiga sun yi wa baki kwanton-bauna suka kashe biyu, suka sace uku.
  4. A bayan asibitin ido na kasa NEC da ke wuraren sabuwar Fanteka da ke jihar Kaduna an yi kidinafin wasu Fulani.
  5. A jihar Jigawa wasu barayi sun kashe wani babban limami bayan sun masa fashin naira dubu dari hudu.
  6. Gwamnatin Nijeriya ta nuna rashin jin dadinta a kan hukuncin kisa da aka yanke wa ‘yan Nijeriya su takwas a Daular Larabawa.
    Af! Mutanen Udawa da na Kuriga da ke jihar Kaduna na ci gaba da barar addu’arku kamar yadda suka bayyana halin ha’ula’in da suke ciki.

Sai kuma yadda ba wuta ba ruwa suka auri talakan da ke cikin garin Kaduna.
Can kuma a jami’ar jihar Kaduna KASU aka ci gaba da yi wa dalibai tarar naira dubu biyar ta makara zuwa a sa musu hannu a kan kwasa-kwasan da za su yi.

Litini 16 ga Sha’aban 1440 (22/4/2019)
Wasika ce ta musamman ga Gwamnan Jihar Kaduna wadda muka wallafa a shafinmu na wasiku, shafi na 28. A garzaya can domin jin abin da ta kunsa kamar yadda mai shafin ya rubuta.

Talata 17 ga Sha’aban 1440 (23/4/2019)

Assalamu alaikum barkanmu da yau Talata, goma sha bakwai ga watan Sha’aban, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa, kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da uku ga Afrilun 2019.

  1. Gwamnatin jihar Binuwai ta kafa dokar hana sakewa da walwala a jihar.
  2. Wani mai mota ya kade ‘yan kungiyar agaji ta boys brigade a jihar Gwambe, ya yi sanadiyyar mutuwar mutum a kalla goma.
  3. ‘Yan bindiga sun kashe mutum a kalla goma a jihar Katsina.
  4. An sace wasu mutane a tsakanin hanyar Birnin Gwari da Kaduna.
  5. Mutanen Kasuwar Magani da ke yankin Kajuru ta jihar Kaduna na ci gaba da tsokacin ana musu dauki – dai-dai a yankin.
    Af! Cikin dare wuraren karfe biyu mun samu ruwan sama a cikin garin Kaduna.

Laraba 18 ga Sha’aban 1440 (24/4/2019)
Assalamu alaikum barkanmu da yau Laraba, goma sha takwas ga watan Sha’aban, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da hudu ga Afrilun 2019.

  1. Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya:
    a) Karbi bakuncin Sarkin Katar/Katar.
    b) Soki kisan da aka yi wa wata baturiyar Birtaniya, da wani dan Nijeriya a wajen yawon bude ido da ke Kajuru ta jihar Kaduna.
    c) Kiran a hanzarta magance rikici na al’umar jihar Adamawa da irin wannan rikici a jihar Taraba.
    d) Sannan shugaban za shi ziyarar aiki jihar Legas.
  2. Sojojin saman Nijeriya sun kashe ‘yan bindiga sun haura goma a jihar Zamfara.
  3. Wasu fulani sun kai hari wani kauye Kingage da ke Lamurde a jihar Adamawa, an kashe mutum daya da kona gidaje fiye da goma sha daya.
  4. ‘Yan sandan Sakkwato sun ce ba su hana iyalan Sambo Dasuki fitowa su yi zanga-zanga ba.
  5. Sojoji sun kashe mutum biyar wajen hana wasu kai farmaki ko hari jihar Binuwai.
  6. Babban hafsan hafsoshin mayakan kasa na kasar nan ya ce zai gama da ‘yan kungiyar Boko Haram da ke jihar Barno.

…………………………………..
Alhamis 19 ga Sha’aban 1440 (24/4/2019)

Assalamu alaikum barkanmu da yau Alhamis, goma sha tara ga watan Sha’aban, shekarar 1440 bayan hijirar cikamakin annabawa kuma fiyayyen halitta, Annabi Muhammad S.A.W. Dai-dai da ashirin da biyar ga Afrilun 2019.
1. Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da ayyuka daban-daban a jihar Legas.
2. Majalisar Dattawa ta dage amincewa da kasafin kudi na 2019 har sai zuwa talata idan Allah Ya kai mu.
3. Majalisar Dattawa ta amince da sunan ‘yar/diyar MKO Abiola a matsayin babbar daraktar NDIC.
4. Barayi sun addabi mazauna layin Rock Road/rokrad da ke Tudun Nufawar Kaduna.
5. Matsalar ruwa ta sa masallata da dama da ke cikin garin Kaduna yin taimama, gidaje da dama ruwan sha ko na dora sanwa ya gagara.
6. Matsalar wuta ta durkusar da masu sana’o’i da dama da ke cikin garin Kaduna.
Mu yini lafiya.
Af akwai iyalan wani dan kasteliya, da suka shaida mun cewa sun shiga wani mawuyacin hali na kuncin rayuwa, sakamakon bata wa wasu sojojin sama rai da ‘yan kasteliya suka yi, sojojin suka bi su har shiyyarsu suka karairaya na karyawa suka yi tafiyarsu. Cikin wadanda suka karairaya har da shi. Tunda aka karya shi, suka shiga wani hali babu wata kulawa in ji iyalan. Da fatan hukumar kasteliya za ta duba wannan kuka nasu.

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

‘Gwamna Nasir El-Rufa’i Ka Fitar Da Mu Daga Wannan Ukubar’

Next Post

Kabilar Dayak: Masu Tsuntsun Daukan Ruhin Mamaci Zuwa Wata Sabuwar Duniya

Labarai Masu Nasaba

Messi

Har Yanzu Messi Ya Fi Kowa Daukar Albashi A Tamaula

by Abba Ibrahim Wada
1 day ago
0

...

An Yi Lugudan Wuta Ta Jiragen Yaki Kan Isis An Kashe Kwamandanta Bin-umar A Tabkin Chadi

Dakarun MNJTF Sun Yi Barin Wuta Kan ‘Yan Boko Haram Sun Kashe 300 A Tafkin Chadi

by Leadership Hausa
5 days ago
0

...

CAN Ta Shirya Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Kisan Deborah A Duk Jihohin Nijeriya

CAN Ta Shirya Zanga-Zangar Yin Allah Wadai Da Kisan Deborah A Duk Jihohin Nijeriya

by Sulaiman Ibrahim
6 days ago
0

...

Ramadan: Diyar Marigayi Sheikh Ja’afar Ta Fara Tafsirin Al-qur’ani A Masallacinsa Da Ke Kano

An Kashe Mutum 172, An Yi Garkuwa Da 23 A Arewa Maso Gabashin Nijeriya Cikin Watanni 3 —Rahoto

by Leadership Hausa
1 week ago
0

...

Next Post

Kabilar Dayak: Masu Tsuntsun Daukan Ruhin Mamaci Zuwa Wata Sabuwar Duniya

Leave Comment

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

%d bloggers like this: