Wajibi Ne Marubuta Su Kauce Wa Rubutu Cikin Duhun Kai – Hassana Danlarabawa

Rubutu

Fitacciyar marubuciya Hajiya Hassana Danlarabawa, wacce a yau tana sahun farko na marubutan shafin intanet (yanar gizo) da tauraronsu yake haskawa a duniyar rubutu, ta yi kira ga marubuta da su zama masu zurfafa bincike kafin su fara rubutu domin kauce wa yi cikin duhun kai. Hajiya Hassana ta yi wannan kiran ne a yayin da take tattaunawa da wakilin LEADERSHIP HAUSA, ADAMU YUSUF INDABO. Ga dai yadda tattaunawar tasu ta kasance:

 

To Hajiya Hassana masu biye da mu a farko za su so su fara jin wace ce Hassana Danlarabawa?

Assalamu alaikum. Da farko dai sunana Hassana Danlarabawa. Haifaffiyar garin Kano, an haife ni shekaru talatin da suka shude, na yi makaranta daga firamare zuwa sakandire, tare da makarantu na Islamiyya, wanda na kai matakin sauke Al’kur’ani da wasu litattafai. Bayan na kammala sakandire mahaifina ya aurar da ni, a yanzu ina da aure da yara guda biyu, kuma ina ci gaba da karatu a matakin N C E. Ina karanta Hausa/Islamic. Wannan shi ne tarihina a takaice.

 

To ya aka yi kika tsinci kanki a matsayin marubuciya?

Kasancewata marubuciya wani abu ne daga Allah, wanda ya ba ni baiwar rubutu a lokacin da ban yi zato ko tsammani ba, ni ma din kamar kowane marubuci ko kowace marubuciya, da silar fara rubutunsu yakan kasance dalilin su din makaranta ne ko masu nazari, da haka suka samu sha’awar farawa. To ni ma kusan hakan ne, saboda ni makaranciya ce, na yi karatun litattafan da ban san adadinsu ba, tun ina da karancin shekaru kuma nake da sha’awar ni ma na zama marubuciya a dama da ni, amma Allah bai nufa ba sai da rubutun online ya baza duniya, sannan na fara tunanin farawa. Duk da hakan ban fara ba, sai wata rana da muka hadu da wata kawata tun ta firamare, a take muka shaida juna cikin murnar ganin juna. Bayan kwana biyu ta ziyarce ni har gidana, hirar da ta gudana a tsakaninmu ita ce silar fara rubutuna, wanda tana tafiya ni kuma na dauki waya na fara typing, a wannan lokaci na tsinci kaina da zama marubuciyar yanar gizo.

 

Wacce shekara kika fara daukar alkalami da nufin yin rubutu na kirkira kamar yadda aka San ki da shi, kuma wanne ne littafi na farko da kika fara rubutawa?

Na fara rubutu a shekarar  2019 ne. Kuma labarin da na fara rubutawa shi ne SANADIN HOTO, kuma shi ne littafin da ya zo da wani sauyi a shekarar a duniyar rubutu, aka tsinci wani abu daban da na zo da shi wanda ba a saba gani ko karantawa ba, duk da rubutuna ne na farko.

 

To zuwa yanzu kin rubuta littafai sun kai nawa, sunayensu?

Zuwa yanzu na samu nasarar rubuta labarai guda Bakwai cif. Ban da gajerun labarai da nakan rubuta. Sun hada da: Sanadin Hoto, Hasssna Da Hussaina, Cin Amanar Ruhi, Bahagon Layi, Garkuwa Biyu, Bahagon Layi (Sabon Salo), Hayatul Kadri. Wadannan su ne adadin littattafaina da suka fita.

 

To cikin wadannan littattafai naki guda Bakwai, wanne ne ya fi ba ki wahala wajen rubutunsa, kuma me ya sa?

Danƙari! Da yake ni irin mutanen nan ce wadda dabi’ata ta kasance idan na saka kaina yin abu na hada da addu’a ba na jin wahalar aikatawa. Hakan ne ya zame mini tsani wajen yin rubutu ba tare da wahalar komai ba, idan ma akwai wahalar ba za ta wuce ta typing ba. Sai dai duk da hakan duk wani labari cikin labaran da na rubuta akwai yanayin da nake samun kaina a yayin rubutun, amma dai babu wahala a ciki.

 

Cikin wadannan littattafai dai naki guda Bakwai wanne ne bakandamiyarki?

Duk lokacin da irin wannan hirar ta biyo ta kaina nakan ambaci labarin ‘Hasssna Da Hussaina’ a matsayin bakandamiyata, duk da ba shi ne zabin makaranta ba, sai dai ni shi ne zabina, ba don komai ba sai marubuta da dama sun bibiye shi, kuma na kama zukatan masu karatu sosai ta yadda suna karatu suna kuka da hawaye ba tare da sun sani ba, labari ne mai tsayawa a zuciyar duk wanda ya karanta shi, domin ni kaina da na rubuta har a yau idan zan dauke shi na karanta to sai na zub da hawaye, dalilin da ya sa na zabe shi ke nan, ba wai don ya fi sauran litattafan wasu abubuwa ba.

 

To wanne ne zabin makarantan naki?

Makarantana suna da yawa, kuma su ma ba su tattara a kan labari guda daya ba, akwai masu cewa har na gama rubutu ba zan yi littafi kamar ‘Sanadin Hoto’ ba. Akwai wadanda suka zabi ‘Bahagon Layi’ saboda labari ne na nishadi da dauke damuwa, wanda sukai masa lakabi da maganin hawan jini. Wasu kuma sun zabi ‘Garkuwa abiyu’. saboda sun ce suna samun nutsuwa a yayin karanta shi, kamar yadda ni ma na samu wata nutsuwa ta musamman a yayin rubuta shi. Wasu kuma ‘Cin Amanar Ruhi’  suka zaba, a cewarsu labarin yana cike da gandoki da wata sarkakiya da hasashe ba ya kaiwa wurin har sai an je. A yanzu kuma da nake rubuta HAYATUL ƘADRI, sai wasu suke cewa kamar ya fi duk litattafaina dadi ma.

 

To cikin wanne yanayi ko lokaci kika fi jin dadin yin rubutu?

Kowane yanayi ko lokaci in dai sha’awar yin rubutun ta zo mini to ina yi, musamman idan ba ni da wani aiki a gabana, ba ni da tsayayyen lokaci gaskiya.

 

Mene ne Babban buri da Manyan manufofin da kike son ta cimmawa a Rayuwa da duniyar rubutu?

Babban buri in dai a harkar rubutu ne, ba zai wuce a ce na zama babbar marubuciyar da idan za a jero manyan marubutan da suka bayar da gudummawa wurin bunƙasar ADABI ni ma suna na ya shigo ciki, kuma ya zamana a duk lokacin da aka karanta labaraina a karu da wasu abubuwa ko da ba su da yawa. Ya kasance kuma ina da tarin mabiya masu karanta rubutuna don karuwa ba don nishadi kawai ba.

 

Wacce Shawara za ki bayar ko kira ga ‘yan uwa Marubuta, ta yadda za su tsaftace da Inganta Harkar Rubutunsu?

To shawarar ba za ta wuce guda uku zuwa huɗu ba. Na farko dai; a duk lokacin da marubuci yake son ya yi rubutu, to ya fara sanin mene ne shi kansa rubutun da yadda ake gudanar da shi, tare kuma da sanin ka’idojin da ake bi domin inganta shi da kawata shi.

Na biyu; idan ka karanci hakan to a lokacin da za ka yi rubutun ka tabbatar kana amfani da ka’idojin da alamomin rubutun da ka koya, duk inda ya dace  da wata alama ka saka, duk inda ya kamata ka bi wata ka’ida to ka bi.

Na uku; a rika kokari sosai wurin sanya adon harshe a rubutu, wannan yana tafiya da zuciyar masu karatu sosai, bayan adon harshe a kawata rubutun da gandoki ta yadda idan mai karatu ya fara karatu ba zai so ajiyewa ba sai ya kammala. Na hudu; kafin fara rubutu a tabbatar an yi bincike kan abin da za a rubuta, domin kar a yi rubutun cikin duhun kai, shi bincike abu ne muhimmi a bangaren rubutu, domin da zarar ka rubuta abin da ba haka ba ne, ba tare da ka yi bincike ba, mai karatu zai fara yi maka kallon kana da nakasu ko wata tawaya mai girma, zai dauka marubucin bai san me yake yi ba. Haka nan a tabbatar abin da za a rubuta, ko jigon da aka dauka, wanda zai amfani al’ummar da suka karanta ne, ba wai ya bata su ba. Waɗannan shawarwari su nake ganin idan aka bi su tabbas za a samu gyara a harkar rubutu da kuma ci gaba, kuma rubutu zai zama ingantacce, tsaftatacce da za a rika alfahari da shi.

 

Za mu ci gaba a mako mai zuwa in sha Allah.

Exit mobile version