Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home LABARAI

Wajibi Ne Mu Hada Hannu Wajen Yaki Da Rashawa- PACAC

by Sulaiman Ibrahim
December 19, 2020
in LABARAI
3 min read
PACAC
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

 Kwamitin yaki da rashawa ya nemi kungiyoyi masu zaman kansu da gwamnatocin jihohi da na Kananan Hukumomi da su kara azama wajen yaki da rashawa domin samun ingantacciyar Nijeriya. Babban Sakataren PACAC ‘Presidential Adbisory Committee Against Corruption PACAC,’ Farfesa Isah Radda ne ya yi wannan kiran a lokacin wani gangamin wayar da kai na masu ruwa da tsaki da suka shirya, wanda hadin gwiwa ne da Hukumar wayar da kai ta kasa (NOA) a Minna.

Farfesa Isah Radda lokacin da yake sauraren shugaban hukumar NOA a dakin taron

Farfesa Radda ya ci gaba da cewar kamar yadda jama’a suka bada shawarwari na janyo hankalin gwamnatin tarayya da na jahohi wajen mayar da hankali kan inganta bangaren ilimi, da ayyukan gwamnati, za mu tabbatar a rahoton mu mun sanarwa gwamnati korafe korafen jama’a ta yadda za mu yi aiki gaba daya wajen tsaftace kasar nan daga rashawa.

samndaads

Ya cigaba da cewar gwamnatin Muhammadu Buhari ta taka rawar gani sosai wajen yaki da rashawa, domin ta samar da hukumomin da ta dorawa alhakin sanya idanu akan matsalolin rashawa, wanda yanzu haka suna aiki kamar yadda ya dace, yanzu haka akwai tsaffin gwamnoni da sanatoci da daidaikun jama’a da ke komar hukumomin.

Radda yace daga cikin nasarorin da aka samu an kwato adadin 192,000,000,00 daga tsoffin ‘yan difulomasiyya, sannan an kwato 15.560,800,000,00 ragowar kudin albashin da aka danne. Bayan nan an kwato ragowar kudin ma’aikatan bugi jimlar 30.280.863,588.72, an karbo ragowar 33.106.310.755.53 na alawus din sojoji da sauran masu damara, da wasu 11,000,000,000,00 ragowar kudin tafiyar da gwamnati a kullun, da wasu 7,800,000,000,00 ragowar kudin da ake kashewa a hukumomin lafiya, wanda jimlar kudaden sun kai 97.939.974,344.25.

Dan haka ba yadda kasar nan za ta cigaba dole sai mun hada hannu mun yaki rashawa ta kowace fuska wanda hakan ne zai iya tsalkake mana kasar nan.

Dakta Gbongbo Ibrahim Yahaya Takuma, shi ne shugaban hukumar wayar kai ( NOA) a Neja, yace kungiyoyi masu zaman kan su da shugabanni na da rawar takawa wajen wayar da kan jama’a illar numfashin cutar rashawa wadda itace silar durkushewar tattalin arzikin kasa da na iya janyo musifu da tabarbarewar lamurra.

Da yake jawabi, gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello da ya samu wakilcin kwashinan ma’aikatar sadarwa da tsare tsare, Malam Muhammadu Sani Idris, yace gwamnatin jiha na bakin kokarinta wajen baiwa hukumomin da abin ya shafa damar aiwatar da ayyukan su yadda ya kamata.

Sai dai ina kira ga jama’a da lallai su fara tsalkake kawunan su, wanda idan sun yi hakan za su zama abin koyi ga al’umma, muna bukatar yin aiki tare ta hanyar wayar da kai da anfanin gujewa yaduwar rashawa.

Farfesa Etannibi Alemika, wanda mamba a kwamitin PACAC, ya gabatar da mukala inda ya janyo hankalin jama’a illar rashawa a kowace fuska, da ya shafi zamantakewa, aikin gwamnati da tafiyar tsarin addini yadda ya dace.

Farfesa Femi Odekunle, shi ne shugaban taron, ya yabawa sarakunan gargajiya da kungiyoyi masu zaman kan su wajen baiwa kwamitin goyon baya, inda ya bukaci su yi anfani da bayanan da aka yi da mukalolin da aka gabatar wajen kyautata hali da ayyuka wanda a karkashi su ne rashawa ke yaduwa.

Taron dai ya samu halartar sarakunan gargajiya da manyan jami’an tsaro, da manyan jami’an gwamnati da kuma kungiyoyin kare hakkin dan Adam da masu sanya idanu akan yadda hukumomin gwamnati ke kashe kudaden gwamnati.

SendShareTweetShare
Previous Post

Matsalar Tsaro: Nijeriya Na Bukatar Shugabanni Su Daidaita Dukkan Abubuwa – Obasanjo

Next Post

Matsalolin Da Su Ke Durkusar Da Kasuwanci A Kano -JIFATU

RelatedPosts

A duniyar Nijeriya ta yanzu, da yawan mutane da ma masu lura da al’amuran yau da kullum su na kallon gudanar da zabukan kananan hukumomi

Abubuwan Al’ajabi A Zaben Kananan Hukumomin Kano

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Kuri’un Da Aka Kidaya Sun Haura Na Zaben Gwamna A...

Ranar Bude Makarantu

Korona: Har Yanzu Babu Ranar Bude Makarantu A Jihar Kaduna

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

 Dukkanin makarantun Firamare da na sakandari da suke jihar Kaduna...

Kwalejin Kimiyya

Gwamnatin Tarayya Za Ta Gina Kwalejin Kimiyya Ta Farko A Borno

by Sulaiman Ibrahim
4 hours ago
0

Ranar Litinin Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya kai...

Next Post
JIFATU

Matsalolin Da Su Ke Durkusar Da Kasuwanci A Kano -JIFATU

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version