Wajibi Ne Musulmi Da Kirista Su Zauna Lafiya –Sheikh Bala Lau

Tashe-tashen hankula sai kara yawaita suke kullum, lamarin da kuma ke da alaka da rashin hakuri, wane jan hankali Malam zai yi wa jama’a akan hakan?

Alhamdulillah, Wasalallahu wasalama Ala Nabiyyi na Muhammad Wa’ala’alihi Wa’asahbihi waman tabi’ahum bi ihsani ilah waumiddin, bayan haka Assalamu Alakum Warahmatullahi Wabarakatuhu. Ina kara jan hankula ga ‘yan uwa mazauna wannan yanki ta arewa maso gabas da mazauna arewa da kuma kasa bakidaya muhimmancin zaman lafiya, zaman lafiya Malam Bahaushe ya ce ya fi zama dan sarki a’a, ya ma fi zama sarkin, domin idan babu zaman lafiya ai babu sarauta. Mu da muke rayuwa a wannan wuri mun san abin da ya faru a wasu masaurautu manya-manya sai da aka rasa kowa a garin idan aka rasa kowa a garin Sarki ma ka ga Kenan babu shi, to idan har da jama’a shi ne za a yi sarauta don haka zaman lafiya yana da muhimmanci kwarai da gaske. Sannan wadanda suke rayuwa a Nijeriya kaf ko dai musulmi ne ko kirista, kuma za ka yi yawo duniya kaf ba mutanen da suke rike da addini suke kokarin yin ibada irin mutanen Nijeriya, wasu Larabawa daga Saudiya sun ziyarci wannan yankin namu na arewa sukaga da ana kiran sallah mutane zasu bar abin da sukeyi su tafi masallaci ba tare da sun ga wani dan sanda ko dagari ko kuma dan agajin da yake korasu su rufe wurin sa’anarsu su je su yi sallah ba, sabanin yadda suke gani a Makka ko a Madina ko kuma a kasarsu, da an kira sallah jami’an tsaro suna yawo suga wanene bai kulli shagonsa ya tafi masallaci ba? Sai malaman suka ce ga abin mamaki ga wadanda al’umma na Annabi Muhammad (S) ana kiransu zuwa ga sallah imaninsu kawai ke raka su ba wani jami’in tsaro, gamunan can da muke rayuwa a Makka da Madina inda aka saukar da ayoyin Al’kur’ani amma idan an kiran sallah bayan imanin kuma sai an sanya tsaro a tabbatar da babu wanda ya saba, idan har mun kaiga irin wannan matsayin, to ya kamata a ce mun kara gode wa Allah Subhanawa Wata’ala sannan mu rungumi wannan zaman lafiya.

Kullum ina fadi, musulmi Allah ya san hikimar da ya sa ya barshi a Nijeriya tare da Kirista su rayu, babu yadda za a yi, hikimar Ubangiji ya fi mu sanin dalilin da ya sa muka zauna haka, inda ya ga dama sai ya bar mu kasa masu addini iri daya, amma ya ce ni musulmi ne wanda ba musulmi  ba kuma in zauna tare da shi, to dole in yi hakuri. Kawai shi dai ya san addini na ga abin da ya karantar da ni, ni ma na san addininsa ga abin da ya karantar dashi, shi ya sa Kur’ani ya gwada mana su yi addininsu mu yi namu, kuna da addinku nima ina da addini na addini na ya shardanta min me zan yi, addininku ya nuna muku me za ku yi? Idan duk mun karanci abin da addininmu ya ke cewa to ya kamata a ce mun bi don mu samu zaman lafiya.

Al’umma mu ji tsoron Allah mu yi hakuri da junanmu, abu kankani sai ka ji an yi kisa, an san zaman lafiya tsakanin manoma da makiyaya tuntuni dama su abu guda ne mai kiwo ya kama dabbobinsa ya daure su kada su yi barna da rana. Manomi da rana yasa ido ya tabbatar da cewa ba wani da ya shiga ya yi mishi barna in an samu barna hukuma ta hukunta tsakani, mai noma da mai kiwo abu guda ne kuma mafi yawa sana’a ne na mafi yawan musulmi, musulmi suna noma musulmi suna kiwo amma yanzu an juya abin ana son a sanya gaba da kiyayya tsakanin makiyaya da manoma sannan an wuce wannan sai a ce ai fada ne tsakanin musulmi da kirista ko kuma a ce ai fada ne tsakanin Hausa-Fulani da sauran kabilu me ya hada wannan? Ina kira garemu mu yi amfani da wannan zaman lafiyar da aka san mu dashi.

 

Akwai masu ganin ‘yan siyasa ke ingiza wutar irin wannan rikicin?

Eh, ‘yan siyasa su ji tsoron Allah,kada su yi amfani da zaman lafiya su canjashi zuwa ga rashin zaman lafiya da kashe-kashe da zubbada jinni don biyan bukatar cimma burinsu kawai na siyasa, in sunyi wannan Allah sai ya kamasu  ya tambayesu  kuma sai Allah ya musu hukunci, menene hikimar ka zama shugaba? Idan ka zama shugaba in baka karewa al’ummarka abubu guda biyar ba shugabancinka bashi da amfani, na farko ka tsare musu addini ka ga kowa yana addini yadda ya kamata addinin Allah ba tare da an gurbatashi ba, amatsayina na musulmi in bautawa Allah shi kadai ba tare da an sanyawa Allah kishiya ba, sannan ka tsare jinin al’ummah ka tabbatar ba’a zubda jinni haka kawai ba, sai da Manzon Allah ya kalli dakin Ka’abah ya ce ‘dakin Ka’abah na da kima da daraja, amma ran mumini mutum daya yafi dakin Ka’abah daraja’ Allah madaukakin sarki ya gwada mana idan mutum ya kashe rai guda daya Kaman ya kashe al’umma baki daya, domin wannan rai ai akwai zuriyarsa to ka kasheshi kamar ka hana wannan zuriya ne zuwa, karewa mutane dukiyarsu ba tare da an lalata musu ita ba, haka kuma karewa mutane kwakwalwarsu ya zamanto ba’ajirkitawa mutane kwakwalwa da kwayoyi, yanzu kwaoyi  sunyi yawa a kasarnan har akwai wasu gurare da unguwanni jam’in tsaro ma na tsoron shiga, to ina gwamnati? Yanzu a ce ga wani yana rike da makami ba za a iya hana shi ba, a ce ga wuri ana sayar da kwayoyin da za’a lalata tunanin ya’yanmu amma an kallo, in mutum ya sha abin da zai jirkita mishi kwakwalwa ba’abin da ba zaiyi ba, ya’yanmu an hanasu karatu ya’yan wasunmu abokanen zamanmu na kasarnan su kuwa sunanan suna karatu, Kenan anason ya’yanmu su girma su zama leburorinsu, kana shugaba baka tsarewa al’ummanka wannan ba, kana kallo ana saida kwaya kamar bakayi abin da ya kamata ba, ana tsarewa mutane nasabarsu kada abari zinace-zinace tayi yawa har akasa gane ya’yan halal da ya’yan haram, babu addinin da bai yarda da aure ba, musulunci yazo da aure haka addinin kirista yazo da aure, babu dalilin da za’abar mutane suna zinace-zinace suna fasikanci ga gidajen karuwar haka, idan shugaba yasan kare wadannan sune suka ratayu a wuyansa ya kamata ya san cewa shugabanci nauyi ne, shi yasa Manzon Allah ya ce ‘ko wani shugaba zaizo gaban Allah a daure ba’abin da zai warwareshi sai adalcinsa’ wani babban abin da yake cutarwa shine duk lokacin da’ayi rigin-gimu an san masu laifin amma akanyi kwamiti na Judicial commission inkuiry, amma saboda tsoron siyasa ko wani abu sai aki hukuntasu, kenan ana  ana bada lasisin cewa kowa ma yaje ya yi barna ba’abin da zai sameshi, ina kira ga gwamnatin tarayya da ta jihohohi ba’abin da zaisa a zauna lafiya sai an kama masu aikata laifi an hukuntasu, domin gani ga wane ya ishi wane jin tsoron Allah, saboda haka ina fata zaman lafiyarmu zai dawo hukuma ta tsaya da yin hukunci sannan iyaye su tsayu da baiwa ya’yansu tarbiya malaman makaranta su zamanto masu tarbiya duk barnar da zai shigo hukuma ta hana in akayi wannan zai a samu cikakken zaman lafiya.

 

Menene illar rashin hukunta masu aikata irin wadannan laifukan?

Illar shi ne gwamnati ba za ta yi tasiri ba, ba za ta yi albarka ba, Mazon Allah(S) a zamaninsa a kwai wanda ya yi zina, aka kamashi za a yi mishi hukunci sai ‘yan uwansa suka zo cewa a roki Manzon Allah kada a zartas mishi da hukunci Husama na cikin wadanda Manzon Allah ke ganin darajarsu da kimarsu aka biyo da wurinsa yazo ya roki Manzon Allah ba a taba ganin fushin Manzon Allah irin ranar ba,yana cewa ‘Husama kai ne zaka hanani zartas da hukuncin da Allah ya ce? Saida Husama ya yi nadamar da bai gayawa Manzon Allah haka ba, sai Manzon Allah ya ce ‘abin da ya halakar da alummomi magabata shine idan mai daraja ya yi laifi sai’abarshi idan marar galihu ya yi laifi sai’ahukuntashi , saboda haka irinsa yake faruwa yanzu, labara yana zuwa mana kan cewa cikin gidan yari sai aje ayi kame akan hanya sai azo a sake wanda akeson a saka mai laifi a maye gurbinsa da wanda aka kamo, wannan ba daidai bane, saboda da haka in anason al’umma tayi tasiri, gwamnati tayi albarka jagorori a rika ganin kimarsu da darajarsu, to ba wai sai in masifa ya samu a rika samo kayayyakin masa-rufi ana rabawa mutane  ana basu hakuri kwana biyu shikenan shiru anemo malaman addini a ce ko bada hakuri ko bada hakuri wannan ba zai taimakemu ba, abin da zai taimakemu shine wanene mai laifin ko dan wanene aka ma shi a yi mishi hukunci, dole Sai mun rufe ido duk wanda aka samu da laifi a hukuntashi ko wayeshi. Abubuwa da yawa sun faru a Nijeriya mun ga fitintinu a jihar Taraba, Gyambu ya faru mun ga fitintinu a jihar Benue a Adamawa ya faru mun gani a Kaduna ya faru a Zamfara inane ya faru har yanzu bamu san wadanda aka kama aka yiwa hukunci ba, shin ba’a gano masu laifin bane? In kuwa an gano me yasa gwamnati bata hukuntasu ba? Saboda haka kacokan laifin ba na kowa bane na hukuma ne, abin da zai sanya adalci daga sama har kasa shine a rika hukunta masu laifi, mu amana ne Allah yasanya mu gaya musu gaskiya, saboda da haka cin amana ne a gano mai laifi kuma a boye shi a ki hukuntashi, ina fata shugabannin daga sama har kasa za su dauki matakin hukunta mai laifi shi zai taimakawa zaman lafiya.

 

Ana wannan ne a daidai lokacin da jami’ar kimiyya da fasaha ta Modibbo Adama dake nan Yola ta shiga rudani bisa zargin wani dalibi ya yi batanci ga Manzon Allah (S), ko malam ya na da wani jan hankalin musamman ga hukumomin makarantar?

Duk dai maganar kusan guda ne, ai bai kamata jami’a tana kallo aci zarafin Manzon Allah kuma ta yi shiru ba Kenan ta taimaka wurin ayi tashin hankalin, a musulunci idan mutum ya zagi Manzon Allah ko ya tuba ba a barin shi sai an tsayar mishi da hukunci, saboda haka kada a bari har yara su dauki hukunci a hanunsu, to ya zamanto hukumar jami’a ta shiga ta zakulo wanda ya yi wannan laifin ta kamashi da hukuncin da ya kamata, in anyi wannan an taimaka wurin a zauna lafiya. Duk aje adawo ku’ina in anason azauna lafiya fa sai anyi adalci, shi yasa Allah ya ce yana ‘umurni da yin adalci da kyautatawa’ saboda haka shugabanni su rikayin adalci talakawa kuma su rika yiwa shugabannin addu’ar Allah yasa su yi adalci da kyautatawa, dole mu rika musu addu’a saboda shugaba ne yana rike da siterin mota shine direba, to in kana addu’ar alkhairi sai kaga an sauka lafiya shine pilot na jirgi in kada addu’a sai a sauka lafiya amma in kana Allah wadai dashi Allah ya yi fushi dashi, idan Allah ya yi fushin dashi sai ya shafe ka, saboda haka talakawa su rika addu’o’I ga shugabanni musamman ma ba zamu manta lokacin da muka kito a baya ba, a wannan jiha ta Adamawa zuwa Borno, Yobe bamu manta da me ya faru ba, an kai lokacin da al’umman musulmi ko sallar magariba da lisha basa iyawa a masallaci kowa a gidansa yake yi, an kai matsayin da kana sahun sallah kana tsoron ta’ina wani abu zai faru? Duk sun faru Allah ya taimakemu da zuwan wannan gwamnati an samu sauke, saboda haka mu rika addu’a saukin nan Allah yasa ya dore wadanda suka zama sanadiyyar saukin suma Allah ya musu rungwame yasa albarka ma jagorancinsu, su kuma su san cewa akwai nauyi akansu na su yi adalci.

 

Ganin yanayin matsin da jama’a ke ciki a kasarnan, na san akwai hubbasar da kungiya ke yi a baya na hurar da matasa da mata sana’o’in dogaro da kai, kamar yanzu ina aka kwana?

Ai har yanzu muna kan shirinmu na maganan ya ya al’ummanmu za su samu abin dogaro,  musamman noma muna nan muna ta kira ga al’umma akan cewa kowa ya tashi ya koyi sana’a, akwai hanyoyin koyar da sana’o’i da gwamnati ta fito dashi akwai yadda ake koyar da mutane sana’a a NDE ya kamata a fadada, yara kuma su nema jihohi su bude cibiyoyin koyon sana’ao’I akwai sana’o’i kanana da cikin lokaci kankani mutum zai koya ya iya,muma mun bude shirye-shirye da dama malumanmu masu wa’azi tsakanin Magariba da Isha’i kowa ya rika sa jan hankali ga matasa cewa kowa ya tashi ya yi sana’a, kada ka dauka idan kana makaranta ba za ka koyi wani sana’a ba, ka koyi sana’ar da za ta taimaka maka ka dogara da kanka, to muna kan jan hankali akai muna kuma fatan da irin wannan jan hankalin al’ummanmu zasu dawo hayacinsu kamar yadda ya kamata. Kuma ina kira ga matasa musulmi maza da mata kowa yaje ya yi rigista an kusa lokacin zabe, gurare daban daban ana layi ana bada katin amma dayawa mutanemu suna sakaci basa fita neman wannan katin zaben hakki ne kuma idan kaga ana ana yin abu ba daidai ba ya’ya zakayi ka canja? sai kayi amfani da katin zaben don ka canja, wasu sun dauka abin da sauki babu sauki, kuri’a daya na iyasa a ci zabe haka kuma kuri’a guda na iya sa a fadi zabe, kuma Annabi ya ce wanda ya ga abin da babu kyau ya canja da hanunsa kana da kuri’a zaka iya canja mulki da ita, wanda bai iyawa ya yi wa’azi wanda bai iyawa yaki abin a zuciyarsa, saboda da haka ina fata duk wanda bashin da katin zabe ya tashi ya dauki wannan dama ko awa nawa ake yi ya yi hakuri domin zaiyi amfani da kori’arsa don ya samar da mutanen kirki, da kuri’armu zamu canja mutanen da bana kwarai ba.

 

Exit mobile version