Masu ba da agaji na Afirka da wadanda ba na yankuna ba, sun yi akawarin bayar da tallafin dala miliyan 17 don sake cike asusun Asusun Hadin gwiwar Afirka, inda wannan, wani yunkuri ne da ke da nufin samar da amincin abinci da kawar da talaucin kauyukan karkara dake a cikin nahiyar ta Afirka.
An yi wannan alkawarin ne yayin wani babban taron masu ba da tallafin kudi wanda hukumar abinci da aikin gona ta Majalisar Dinkin Duniya da shugaban kasar Ekuatorial Guinea Obiang Nguema Mbasogo suka gabatar a yayin babban taron shekara-shekara da aka gudanar a kwanakin haya a yankin Malabo dake a Ekuatorial Guinea.
A jawabin sa a lokacin bude taron a cibiyar taron Sipopo, Shugaban kasar Ekuatorial Guinea Obiang Nguema Mbasogo, ya ce asusun ya nuna canji ne ga yaki da matsalar rashin abinci, inda Shugaban kasar Ekuatorial Guinea Obiang Nguema Mbasogo ya kara da cewa karamar al’ummarsa mai arzikin mai ta ba da gudummawa da yawa daga kudaden shigar mai don nuna hadin kai ga kasashen Afirka.
Asusun dai, wani yunkuri ne na Hukumar Abinci da Aikin Noma na Majalisar Dinkin Duniya, ya karɓi gudummawar farawa ta dala miliyan 30 daga Ekuatorial Guinea.
An yaba wa ayyukan sa na samar da sabbin hanyoyin inganta aikin gona da tsarin abinci na Afirka.
Da ya ke magana a madadin shugaban bankin ci gaban Afirka Dakta Akinwumi Adesina, mataimakiyar shugabar saahen bankin na aikin Noma da Raya Al’umma, Jennifer Blanke, ta ce Afirka na fuskantar kalubale a fannin noma da samar da abinci, ta dogara da kayan abinci sosai.
A cewar shugaban bankin ci gaban Afirka Dakta Akinwumi Adesina, yana da makukar muhimmanci ASTF ya nuna cewa kasashen Afirka suna bayar da gudummawa ga Afirka.
Shugaban bankin ci gaban Afirka Dakta Akinwumi Adesina yaci gaba da cewa, wannan ya danganta ne sosai ga abin da muke yi, inda ya kara da cewa bankin ya lashi takobin samar da manoma da fasahar da za su taimaka wajen bunkasa amfanin gonar.
Har ila yau kuma, taron ya samu halartar shugabannin kasashen Mauritania, Guinea Bissau harda Firaminista Eswatini da manyan jami’an diflomasiyya da ministocin samar da ci gaban kasa da sauran su.
Taken tattaunawar bankin a bana shi ne ‘Hadin kan Yanki don Ci gaban tattalin arzikin Afirka: Kokarin hada kan yankin ya sami ci gaba tare da amincewa da yarjejeniyar kan yankin Yarjejeniyar Kasuwanci ta Afirka a cikin Maris 2018, wanda yanzu haka ya ke gab da kaddamar da ita a watan Yuli.
Shugaban bankin ci gaban Afirka Dakta Akinwumi Adesina ya kuma shedawa mahalarta taron cewa, suna iya dogaro da mu cewa za mu shiga cikin lamarin.
Asusun ya haifar da nasarar aiwatar da ayyukan 18 da suka amfana da kasashe 41 da daruruwan kuma dubban wadanda suka amfana, ciki har da gidaje 160 masu rauni a Nijar wadanda su ka ga canji da tallafin wanda ya ba da damar gaggawa ga jama’ar da cutar ta bulla a cikin Yammacin Afirka a 2014.
Bugu da kari, taron ya tara dala miliyan 17 da dala miliyan 10 miliyan daga daga kasar Angola sai kuma dala miliyan 2.6 daga kasar China, Yuro miliyan biyu daga Faransa, sai miliyan 2 daga kasar Ekuatorial Guinea sai kuma dala miliyan 100,000 daga kasar Zimbabwe.