Connect with us

RIGAR 'YANCI

Wajibi Tsohon Gwamnan Bauchi Ya Amayo Biliyan N321, Cewar Bibi Dogo

Published

on

Wani jigo a jam’iyyar PDP, Alhaji Bibi Dogo, ya kalubalanci tsohon gwamnan jihar Bauchi, Barista Muhammad Abdullahi Abubakar da ya amayo tare da maido da zunzurutun kudi har naira biliyan N321, 267, 339 .69, wanda ya zargi tsohon gwamnan da amsa a farkon watannin gwamnatinsa 31 ko kuma ya fito ya nuna aiyukan da ya aiwatar da wadannan kudaden da ya karba a lokacin da ke kan kujerar gwamna.

Alhaji Dogo yayi bukatar dawo da kudaden ne a karshen mako a lokacin da ke ganawa da wasu ‘yan jarida, ya kara da cewa kudaden da tsohon gwamnan zai dawo da su, sun hada da kudin Paris club, kason da jihar ta yi ta amsa da na kananan hukumomi, tallaifin kudin Amurka kan kyautata bangaren ilimi, kudaden shiga, tare kuma da kudaden basukan cikin gida da na waje.

Dogo wanda yayi aiki a kwamitin kwato kadarorin gwamnatin jihar da gwamnati mai ci ta kafa, ya zargi Barista M.A Abubakar da cewa ya amshi naira N33,425,994,087,69 na kason Paris Club daga gwamnatin tarayya na karin farko da na biyu zuwa na uku.

Ya kuma ce, tsohon gwamna Abubakar ya karbi N205,328,523,558,00 na kason jiha da kananan hukumomi daga lalitar gwamantin tarayya cikin watanni 31 na gwamnatinsa, “Ya kuma karbi tallafin kudin Amurka dala $57,000,000 kwatankwacin naira N17,385,000,000,00 da kuma a tsakanin watan Yuni 2015 zuwa Yuni 2016 tsohon gwamnan ya karbi N22,778,721,996,00.”

Dogo ya kuma ce, Abubakar ya kuma amshi N59,734,100,000,00 na kudin bashin ciki da waje da kuma tallafin kasafin kudi naira 11,000,000,000,00 daga gwamnatin tarayya.

Jigo a PDP din, ta kuma kara da cewa tsohon gwamnan ya amshi maguden kudaden ba tare da aiwatarwa tare da kaddamar da wasu aiyukan a zo a gani ba, don haka ya ce akwai bukatar tsohon gwamnan ya dawo da kudaden da ya karba na al’umman jihar.

Wakilinmu yayi kokarin jin ta bakin Kakakin tsohon gwamnan jihar kan wannan zargin lamarin ya citura, amma da zarar muka ji martaninsu za mu shaida wa duniya.
Advertisement

labarai