Wajibinmu Ne Daƙile Sake Ɓarkewar Yaƙin Basasa –Buhari

Daga Khalid Idris Doya

A ranar larabar nan shugaban Nijeriya Buhari a birnin Abuja a sa’ilin da ke ƙaddamar da ranar tunawa da ranar tunawa da sojoji ta 2018 inda ya yi shelan ƙira ga illahirin al’umma da su kansance masu taimaka wa jami’an sojoji da kuma iyalan sojojin a kowani lokaci. Buharin ya kuma bayyana cewar gwamnatinsa a shirye take ta ci gaba da baiwa sojoji dukkanin goyon baya domin magance dukkanin matsalolin da suke fama da su.

Sai ya bayyana cewar za kuma su kasance masu tabbatar da halayen kwarai daga jama’a inda ya ke cewa wajibinmu ne su babbatar ba a sake samun ɓarkewar yaƙin basasa a Nijeriya ba.

A cikin jawabin na shugaban ƙasa ya ce: “maza da mata ina muku lale a bisa halartarku wajen ƙaddamar da ranar tunawa da sojoji na 2018 da kuma assasa asusun taimakonsu. Kamar yanda yake bisa al’ada wannan taron an saba yinsa domin tunawa da jaruman da suka sadaukar da kansu da rayuwarsu a yayin yaƙin duniya na farko da ta biyu, da kuma jaruman da suka sadaukar a yaƙin basasan Nijeriya da kuma waɗanda suka yi aiyukan kula da tabbatar da zaman lafiya a dukkanin faɗin duniya haka kuma da waɗanda suke kan aikin tabbatar da tsaro musamman waɗanda yanzu haka suke ci gaba da fafatawa wajen shawo kan matsalar tsaro da ya addabi arewa maso gabashin Nijeriya da wasu sassan Nijeriya”. in ji Buharin

Shugaban Nijeriya ya kuma ƙara da cewa “Yana da kyau mu tuna jaruman ‘yan mazan jiya gami da karrama jaruman da suka sadaukar da ransu wajen kare ƙasar nan wajen tabbatar da kasancewa Nijeriya dunƙulalliyar ƙasa. Jaruman da suka sadaukar da rayuwakansu a yayin da suke kan aiyuka domin su tabbatar da samar wa faɗin ƙasar nan zaman lafiya. Ƙoƙarin da ‘yan uwanmu mata da maza suka yi wajen haɗa Nijeriya waje guda ba za mu mance da wannan ba, a bisa haka ne muke gudanar da wannan bikin”. Ta bakinsa

Buhari ya ƙara da cewa “Wajibinmu ne mu tabbatar ba a sake samun ɓarkewar yaƙin basasa ba a Nijeriya, za mu tabbatar da kare rayuwakan jama’a ta fuskancin hana zuwan wannan yaƙin. Za kuma mu shawo kan dukkanin barazanar da ke kunno kai ka’akari da kwarewar da muke da shi a kan yaƙi”. In ji Buhari

Shugaban sai ya jinjinawa wa sojoji maza da mata da suka ba da ransu da komansu wajen kare Nijeriya da shawo kan matsalolin tsaro da ake fama da su a Nijeriya.

Sai  kuma yaba sosai da halayen kwarai da sojojn ke nuna a cikin ƙasar a yayin da suke kan aiyukanku “Dukkaninku na gamsu da mene ne kuke aiwatarwa”.

Ya ce: “Wannan gwamnatin za ta ci gaba da baku ƙarfin iko da kuma tabbatar da samar muku da ababen more rayuwa kana da tabbatar da jin daɗi da kuma walwalarku, za mu tabbatar da an samar muku yalwatattun ababen more rayuwa”.

Shugaban Nijeriya ya buƙaci sojojin da su ci gaba da sadaukar da kansu domin kare ƙasa da al’umman ƙasa, inda ya sha alwashin ci agba da mara musu baya domin ganin sun samu kwarin guiwar ci gaba da aiyukan da suka kamata. Yana mai amfani da wannan damar wajan yin ƙira ga jama’a da suke kasance masu baiwa sojojin cikakakken goyon baya domin samun nasarar aiyukan da suka sanya a gaba. Ya sha alwashin cewar gwamantinsa za ta ci gaba da tafi da sojoji domin shawo kan matsalolin tsaro da suke addabar Nijeriya.

Haka kuma, Buhari ya yi amfani da wannan damar wajen bayyana tallafinsa ga sojojin domin ƙara musu kwarin guiwa a kan aikace-aikacensu.

 

Exit mobile version