Connect with us

BIDIYO

Waka Ita Ce Silar Dukkan Nasarorina Na Rayuwa– Abba S. Boy

Published

on

Tattaunawar WAKILINMU, MUSA ISHAk MUHAMMAD Tare Da MAWAKI ABBA S. BOY KUMA JARUMI A CIKIN SHIRIN KWANA CASA’IN NA TASHAR AREWA 24.

Da Farko Dai Za Mu So Ka Fada Mana Cikakken Sunanka Da Kuma Takaitaccen Tarihinka.

To da farko dai ni sunana Abba Sa’ad ni dan asalin garin Samunaka ne. Amma tun ina jariri mu ka dawo garin Kaduna. A garin Kaduna na girma, a nan na yi komai nawa. A nan na yi harkokina, da fadi-tashi, da kujuba-kujuba, har kuma na samu kaina a matakin da na ke kai yanzu. Wannan shi ne tarihina a takaice.

Ya A Ka Yi Ka Samu Kanka A Cikin Masana’antar Fina-finai Musamman Shirin Kwana Casa’in Na Arewa 24?

Ehh to! Kai tsaye ba zan ce na samu kaina a cikin masana’antar fina-finai ba tunda ban shiga cikinta tsundum ba. Na dai yi aiki da Arewa 24, ka ga wannan ba za a kirawo ta masana’antar fina-finai ba. To amma dai na fahimci tambayar taka. Shi komai a rayuwa nufi ne na Ubangiji, ni gaskiya tun ina karami mutum ne ni mai son gwada abubuwa, kuma na yi abubuwa da yawa a rayuwata. Ka ga na yi aiki a (Cafe), sannan na zo na fara shirye-shirye na barkwanchi wanda a ke kira(comedy). To farko dai ma da waka na fara. Ina nan ina waka ina waka, Saboda ni na taso da son ganin ina gwada abubuwa, wanda na ke ganin zan iya da ma wanda na ke ganin ba zan iya ba. Hakan ne ya sa komai da zan ga ya na tafiya da zamani, ina kokarin in ga na kai kaina ciki, ko na nemarwa kaina dama a ciki. Chan a lokutan baya akwai wani abokina mawaki ne sai ya samu dama cewa Arewa 24 za su yi hira da shi, to sai ya fada min. To hira ce wanda idan za a yi a na so a dan samu gayu da za su zauna a na dan nuna su. To sai na yi kokari na halacci wannan hira. To bayan an gama hirar ne sai na yi kokari na karbi lambar wayar Nomis Gee da kuma Aminu, bayan sun gama yin wannan hirar da abokina. To ta haka ne mu ka fara magana da su kuma na nuna mu su sha’awata ta shiga cikin shirinsu na Dadin Kowa, saboda lokacin ba a fara ma shirin Kwana Casa’in ba. Sai su ka ce min shirin Dadin Kowa ya riga ya yi nisa, amma na yi hakuri akwai sabon shiri da za a fara yi mai suna Kwana Casa’in, in sha Allah idan an zo farawa za su sanar da ni domin na zo tantancewa ta samun shiga shirin. A na farawa kuwa su ka kira ni na halacci tantancewa a Kano, kuma na yi nasarar samun fitowa a matsayin “Abba John”. Wannan shi ne bayanin yadda na samu kaina a cikin wannan shiri.

Bayan An Gama Tantancewa Kuma Ka Samu Nasarar Fitowa A Matsayin Abba John Wanne Yanayi Ka Samu Kanka Duba Da Cewa Shi Ne Karo Na Farko Da Ka Samu Irin Wannan Dama?

Gaskiya na ji dadi sosai a wannan lokaci, saboda ban yi zaton zan samu ba kawai na je na gwada ne kuma sai Allah Ya bani nasara. To sanda a ka kirawo ni a ka ce na samu Kwana Casa’in gaskiya na ji dadi sosai. Saboda na dade ina son (acting) kuma musamman a tasha kamar Arewa 24. To gaskiya da na samu na ji dadi sosai.

Bayan Shirin Kwana Casa’in Da Ka Ke Kan Yi A Yanzu, Ka Kara Samun Damar Shiga Wani Fim Kuwa?

Ehh gaskiya ban kara samu ba zuwa yanzu, sai dai a shekarar da ta wuce a watan Nuwamba wani furodusa ya sanar da ni cewa ya sa ka ni a cikin wani fim dinsa. Sai dai kuma Allah bai nufa an fara daukansa ba har yanzu. To gaskiya dai ban sake samun wata damar ba. Kuma mu na kan aikin Kwana Casa’in har yanzu, saboda shirin bai kare ba.

A Yanzu Idan Ka Samu Damar Fitowa A Wani Fim Bayan Shirinku Na Kwana Casa’in, A Shirye Ka Ke Ka Karbi Wannan Damar Ko Dai Ka Fi Gamsuwa Da Shirin Kwana Casa’in?

To ai duk jarumi ba zai ce maka shi ga iya abunda ya ke so ya yi ba. Kuma su kansu mashirya shirin Kwana Casa’in din su na so su gan mu a cikin wani aikin na daban. To a shirye na ke a kodayaushe wani aiki ya zo, to zan duba shi sosai kuma zan karba, in har ba da wani babban dalili ba. Amma ba zan ce dole sai Kwana Casa’in ba, saboda kwana casa’in yadda ya fara haka zai kare. Kuma daman ita irin wannan dama a na so ka yi amfani da ita ne wajen fadada aikace-aikacenka. To a shirya na ke da izinin Allah duk wani abu da zai zo zan karbe shi, idan har ya zo ta hanyar da ta dace.

Bari Mu Dan Tabo bangaren Wakoki Domin Nan Ma Ba A Barka A Baya Ba, Ya Ya A Ka Yi Ka Fara Waka?

Ehh to kamar yadda na fada maka kafun na fara komai waka ce a bar da na fara. Bayan rasuwar mahaifina na samu kunci a rayuwa, ga talauci da babu, komai dai ya daina tafiya yadda ya kamata, ga kuma aikin Kwamfiyuta din da na ke albashin ba yawa sosai. Hakan ya sa na fara tunanin me zan fara wanda zan rike domin ci-gaba da gudanar da rayuwata, to shi ne sai na fara waka. Duk wani mataki da na taka a rayuwa a sanadin waka ne. Domin waka ce ta sa na san manyan mutane su ma kuma su ka sani. Ta silar waka na fara (Comedy) daga nan kuma na dawo Kwana Casa’in. Kuma har yanzu ina dan yin wakar kawai dai abubuwa ne su ke dan yin yawa. Kuma ina yin wakoki na tallace-tallace, da kuma wakokin abubuwan da su ke faruwa. Kamar misali a wannan annobar ma ta “Korona” ita ma na yi waka a kai. Kuma na samu nasarori sosai a harkar waka domin na samu lambobin yabo, kuma na samu zuwa har wasu jihohi na yi waka ciki har da Jihar Lagos.

A karshe Me Ne Sakonka Ga Masoyanka Masu Kalla Da Kuma Sauraren Aikace-aikacenka?

To ba abinda zan iya cewa sai dai in ce na gode, domin babu abinda zan iya biyan masoyana da shi. Domin tunda na fara shirin Kwana Casa’in kullum masoyana karuwa su ke. Saboda haka ina godiya ga masoyana sosai da sosai. Haka su ma abokan aikina du ka su ma ina godiya agaresu. Ina yi wa kowa fatan alkhairi, Allah Ya biya kowa bukatunsa na alkhairi.

Jarumi Kuma Mawaki Abba Sa’ad Mu Na Godiya Sosai.

Ni ma na gode ssosai-sosai.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: