Wakar Da Nike Yi Baiwa Ce Daga Allah – Mawaki Yasir Gambo (Abban Yasmin) Roni

Yasir Gambo shahararren mawaki ne a masaurautar Kazaure da ta hada da Roni,Gwiwa,’yan kwashi, Kazaure.Ya yi waka sama da guda 200.

Wakilinmu Yusuf Kabir ya tuntube shi dangane da yadda ya zamanto mawaki, ga abinda yake cewa:”

Sunana Yasir Gambo ina zaune ne a garin Roni da ke Jihar Jigawa. Na yi makarantar Firamare da Sakandire, sannan sai na shiga fagen waka.
2. Akalla yanzu na yi wakoki guda 200 da suka hada da na yabon Manzon Allah (s), na Mauludi, na suna, na bukukuwa, na ta’aziyya da kuma na siyasa.
3. Na fara waka tun shekara 6 da ta wuce.
4. Lallai na fuskanci kalubale musamman daga Mahaifina a kan lamarin wakata, saboda akwai wani abokin Mahaifina da ya kai karata wajen Mahaifinmu a kan lamarin wakar, amma a sadda na yi wa Mahaifin nawa bayani, lallai ya gamsu ya kuma karfafa mini gwiwa a kan hakan.Ta bangaren Mahaifiya ta kuma,lallai ban sami matsala ba.
5. Ina yi wa masoyana albishir da ce wa,lallai su ci gaba da bibiyar wakokina, domin akwai amana a tsakanina da su. Sannan akwai sabbin wakoki da zan fitar da su a kwanakin nan.

A takaice dai abinda zan iya cewa kenan.

Exit mobile version