Connect with us

ADABI

Wakar Gwamma Malama Ta Dokta Mamman Shata Katsina (1953): Raddi Ga Dokta Aliyu Tilde

Published

on

A cikin littafin Shata: Mahadi Mai Dogon Zamani wallafar Madaba’ar Labson Laboratory Kaduna (2013) mun bayyana zuwan Shata Kankiya cikin 1953 bisa ga amsa gayyatar Alhaji Ibrahim (kuma mahaifin Tukur Jikamshi, tsohon mataimakin gwamnan Katsina-1999-2003) a lokacin ya na malamin kada a nan Kankiyar. A wannan zuwan ne Mamman Shata ya fara ganin Malama Gwamma Malama a rayuwar sa, kuma an ma ce a bisa doki ya je Kankiyar don a lokacin mota ba ta yawaita ba. Dalili, shi ne a bisa ga al’ada a lokacin idan bako ya zo a gari to sai an aika Limamin garin da Hedimasta da shugaban ‘yan kamasho da ma malamin asibiti na garin sun zo domin su ne taurarin gari a zamanin. Sai kuma an gabatar da shi ga mai unguwa ko dagaci ko hakimi.

To,  a nan aka tara su Gwamma Malama su ka yi ma Shata lale marhabin. Hatta ‘yan makaranta na karamar Firamare (Junior Primary School) ta Kankiya, irin su Malam Ado Kankiya lokacin ya na aji 3 sai da aka tara su don su ga Shata, su kuma yi masa barka da zuwa. A wurin kuma Gwamma Malama ta yi ma Shatan kari sosai.

Amma Shata na Bilkin Sambo bai tashi yi mata waka ba sai a unguwar ‘Yar’aduwa da ke birnin Katsina a dai cikin wannan shekarar ta 1953, sannan ta samu canjin wurin aiki. Kuma marigayi Ladan Kontagora na FRCN, a wata hirar mu cikin Disambar 2003 ya ce a shagon Ebele Aguna da ke Sabongarin Kano Shata ya sake rera wakar Gwamma Malama din har aka dauke ta a faifan garmaho, a dai cikin 1953 din.

A lokuta kimanin uku (3) na kuma samu labarin rayuwar  Gwamma Malama daga bakunan da bas u karya, watau ‘yan uwan ta watau kamar kanen ta wanda su ke daki guda (uwa daya uba daya) da ake kira Alhaji Isa Sarkin kutare Kankara da ya taba yin malamin asibitin kutare din, da kuma Alhaji Ado Kankiya shi kan sa. Shi Isa Sarkin kutare aikin asibitin kutare ya kawo shi Kankara daga Kankiya, ya dade nan har ma ya yi aure ya hayayyafa, ya kuma yi ritaya. To sai Allah Ya yi zaman sa nan Kankara din. Duk ‘ya’yan sa nan ya haife su,, su ma nan su ka girma har su ka yi aure, su ka ma auras suma. Amma dai mahaifar sa ta usulan ta na Kankiya. Na kuma taba cin karo da wani wanda jika ne a gare ta. Shi ma mun zanta da shi. Duka bayanin da na tattara shi ne ta yi zama a Katsina da Kankara da Musawa da Dutsinma da Kaita da ma Kankiyar, sai kuma Daura, da dai sauran garuruwa. Don ma a lokacin malaman allura suna karanci matuka, ita kuma malam ce ta bangaren allurar kurum. Kuma sun tabbatar mani da cewa ita fannin allura aka ajiye ta. An dai san cewa ba ta yi karatun boko ba kamar dai yanda matan wannan wakatin ba su yi boko ba, illa gwamnati na neman su ta ba su horo sannan a ba su takardar kama aiki. Lokacin malaman asibitin ma na karanci matuka. Kuma sun tabbatar ma ni da cewa ta rasu cikin 1980 daidai. Hatta tsofaffin Kankiya da ma na kauyen Tama da na Charanchi sun tabbatar mani da haka. Ni kuma na fadi haka a hira ta da Rediyon Freedom na Kano cikin 2010, da gidan Rediyon Yamai cikin 2013.

Sai ga shi a kusan shekaru 5 da su ka dan gilma Dokta Aliyu Tilde ya yi hira da wata mata mai suna Gwamma Malama wadda kuma wai Shata ya yi ma waka har ya buga hirar a jarida. Ni kaina ina da kofin jaridar. Ko da ya ke hirar ba wata ta kirki ba ce don matar ba ta bada wani cikakken bayanin haduwar su da makadin ba da dalilin da ya sanya ya yi mata waka.

Ka ga kenan a nan mu na da Gwamma Malama biyu: da ta Dokta Aliyu Kankara da kuma ta Dokta Aliyu Tilde.

Kuma ita waccan gudar Gwamma Malama ta Dokta Aliyu Tilde duk bayanan can na sama na haduwar Gwammar da Dodon kida Doktan mawaka ba ta ba da shi ba sai ta yi ta nokewa. Ga dai filin tambaya Dokta Tilde ya bude mata amma ba wata amsar kirki. To koko don ba ita ba ce orginal Gwammar? Koko kunyar bada amsar ta ke ji saboda dan yau za ya ji amsar wata iri, ba ma dai da ta ke kewaye da jikokin ta a lokacin hirar? Bayan ‘yan watanni da wannan hira ta Aliyu Tilde da wannan mata sai na tafi Kankiya don in tabbatar. Amma da da farko ban yi niyyar zuwa ba, wanda ya matsa mani da in je don in tabbatar shi ne Malam Ibrahim Sheme wanda mu ka wallafa littafin tarihin Shata na farko tare. Kuma ga yanda na ji kalaman bakin Malam Ibrahim Shehe a gaskiya ya na goyon bayan Dokta Aliyu Tilde, don ya aminta da cewa wannan mata itace Gwammar da Shata ya yi ma waka. Na yi kokarin kawo masa hujjoji na na cewa ba ita ba ce amma bai yarda ba.

Amma da ma na je Kankiyar sai na tarar wannan mata ta ma rasu.      Shata, na biyu daga hagu, sai Muhammadu Adamu Dankabo

na hudu daga hagu, a Kano.

Maryam Hadejiya, daya daga cikinmatan da Shata ya wake a lokacin rayuwarsa.

ama kuma wakokin Shata na da wannan saddabarun. Sai ka ga mutum an yi masa waka amma sai jama’a su yi ta dora wakar a kan wani kuma daban.

Misalai anan shi ne a kwanakin baya lokacin da Jaridar Aminiya na wallafa labarurrukan wadanda Shata ya yi ma waka da kuma dalilan yi masu wakokin haka aka yi samun wadannan matsalolin. An yi hira da wani mutum a Kano, ya ce wai shi ne Abba na Titi, alhali Abba na Titi original a cikin unguwar ‘Yansiliyu ta birnin Katsinar Dikko aka yi shi. To galiban, editan jaridar ya kan bugo mani waya ya nemi gaskiyar batun. Ni kuma sai in fada masu gaskiya. Idan wanda aka yi hirar da shi na gasken ne to sai in fada masu, idan kuma jebu ne nan ma sai in fada masu.

A nan, ya kamata a rika tantance tabbacin abu cewa na gaskiya ne kafin a wallafa shi har Duniya ta ji ta kuma gani. Tuni jama’a da su ka gane kuskuren wallafa labarin Gwamma Malama na Dokta Tilde su ke ta fama da ni da in maida martani don a yi gyara ina nokewa. Sai yanzu na ga ya dai dace da in sa alkalami in lurar da maigirma Dokta. Ina fata za a yi wannan gyara .

Mu kwana nan.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: