Wakar Rabi’u

Salam, Alaska Abu ai shi ne na dawo ‘yan Nijeriya, yauma sako ne na kawo ma Arewa har Kudu zan zo ku yi mini oyoyo mana, a lafiya yau ga shi kasa ana ta yawo ba a yin fada ba ka ji ana ta waiyo-waiyo zaman lafiya dadi ba wai yawan fada ba, mu daina tsangwamar juna, mu daina nuna gaba, kuma mu daina yin fada na kabilanci. Bara ba bana ba sannan mu bar kashe juna, ba fa’ida ba ne idan da matsala to sulhu baa bin gudu ba ne ba, a sanya nutsuwa ai gyara ba wai da takubba tunda mun sani tashin hankali ba.

Abin sabo ne a baya mun gani kisa ba mu san sila ba sai a sanya Bom a yi ta kisa ba mu san dalili ba ko a sanya Bindiga a yi ta kisa ba wai da sandina ba. Wancan lokaci ko taro ba san shiga muke yi ba, shiga masallaci ko coci fargaba bata fice ba balle gidan biki ko kasuwa, tsoro ba zai bari ba yanzu babu zancen tsoro natsuwa ta samu duba godiya muke ga babban sarki Ubangijin mu Rabbi, yanzu sabuwa aka dauko, Allah ba zai bari ba fada ake tayi da Fulani basan ganin nake ba, Taraba da Benuwai da Fulani mai ya sa bakwa bari ba kunata karkashe junanku ba fa’ida ne ba.

Shugabanni kuna kallo bawai karya nake ba, ran mutane ake ta kashewa bawai na akuyoyi ba, hakkin kune kare rarayuka bawai zaman kushin ba, Allah kai ne kake gyara ba wai Dan Adam ba, kai ne ka gyara wancan wannan ba zai gagare ka ba, don Allah mu daina yin fada mu daina tsangwamar juna kuma mu daina karkashe juna mu daina yin fada na kabilanci bara ba bana bane ‘yan Nijeriya  mu (Kano) Nijeriya ce (Legas) Nijeya ce (Borno) Nijeriya ce (Ibadan) Nijera ce (Katsina) ma Nijeriya ce (Ekiti) Nijeriya ce (Sokoto) ma Nijeriya ce (Oyo) Nijeriya ce (Yobe) ma Nijeriya ce (Ogun) Nigeriya ce (Bauchi) ma Nijeriya ce (Taraba) ma Nijeriya ce (Yole) ma Nijeriya ce (Benuwai) ma Nijeriya ce (Gombe) ma Nijeriya ce (Zamfara) ma Nijeriya ce (Nija) ma Nijeriya ce (Kwara) ma Nijeriya ce (Filato) ma Nijeriya ce (Kogi) ma Nijeriya ce (Adamawa) ma Nijeriya ce (Kebbi) ma Nijeriya ce (Dalta) ma Nijeriya ce (Kaduna) ma Nijeriya ce (Anambara) ma Nijeriya ce (Osun) ma Nijeriya ce (Bayelsa) ma Nijeriya ce (Nasarawa) ma Nijeriya (Jigawa) ma Nijeriya ce (Ribas) ma Nijeriya ce (Ibonyi) ma Nijeriya ce (Abuja) ma Nijeriya har da inda bamfadi ba, mu duka Hausawa ‘yan Nijeriya ne Yarbawa ma ‘yan Nijeriya ne har ma da Ibo duk ‘yan Nijeriya ne, Musulmammu da Kirista mu duka ‘yan Nijeriya ne.

Exit mobile version