Wakilan Juventus Suna Ingila Don Kammala Batun Komawar Mandzukic Man U

Wasu rahotanni daga kasar Ingila sun bayyana cewa tuni wakilan kungiyar kwallon kafa ta Juventus suka sauka a birnin London domin kammala maganar dan wasan gaba na kungiyar, Mario Mandzukic, wanda Manchester United take zawarci.

Dan wasan dan kasar Crotia mai shekaru 33 dai an dade ana maganar cewa zai koma Manchester United domin cigaba da buga wasa kuma har yanzu bai bugawa kungiyar kwallon kafa ta Jubentus wasa ba a kowacce gasa.

Sai dai kamar yadda rahotanni suka bayyana dan wasan yana daukar horo ne shi kadai a kungiyar domin ya kasance cikin shiri ya yinda kuma babban daraktan Juventus, Fabio Paratici ya sauka a Ingila domin kammala Magana.

Kociyan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United dai yana fatan kungiyar zata dakko masa Mandzukic domin taimakawa matasan ‘yan wasansa na tsaakiya da suka hada da Marcus Rashford da Anthony Martial da kuma Marson Greenwood.

Mandzukic, tsohon dan wasan kungiyoyin kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munchen da kuma Atletico Madrid ya buga wasanni 160 a kungiyar ta Jubentus inda kuma ya zura kwallaye 43 tun bayan shigarsa kungiyar a shekara ta 2015.

Sannan kuma wasu rahotanni sun bayyana cewa acikin tattaunawar daza’a ayi tsakanin Manchester United da Jubentus din daraktan na Jubentus zai shigar da bukatar kungiyarsa na ganin ta sake sayan dan wasa Paul Pogba.

 

Exit mobile version