Abdullahi Muhammad Sheka" />

Wakilcin Al’umma Da Ce Ne!

Wakilcin Al’umma al’amari ne mai sarkakkiya gaske domin akwai abubuwa masu tsoratarwa da kuma ban sha’awa a cikinsa, saboda haka ne ma ya sa tsarin demokaradiyya ya mayar da hankali kan baiwa al’umma damar zabar wanda suke ganin kila shi ne zai iya fidda jaki daga duma, ko ace zabarsa Kwalliya na iya biyan kudin Sabulu. Wasu al’umma sun tsinci kansu cikin dana sanin zabar wasu daga cikin wakilansu a matakai iri daban daban, wasu kuwa baki har baka domin laya tayi kyan rufi.

Duk da cewa akwai kujerun da doka ta nuna cewa su wadanann wakilan abin da ake so daga garesu shi ne samar da dokokin da za su inganta rayuwar al’ummar da suke wakilta, ba cewa aka yi dole sai sunzo sun bayar da kudi ba. Amma a siyasa irin tamu wannan bashi talakawa ke

duba wa ba, abin da ake bukata shi ne mene ka bani a matsayi na wanda na zabeka, wannan kuma ba dole ya shafi sauran al’ummar da muka hadu wajen zabar wakilin namu ba.

Rt. Honarabul Ado Alhassan Doguwa matashin dan siyasa wanda shekarunsa duka duka basu wuce cikin cokali ba, Mai tsawatarwa a majalisa, ya kafa tarihin da a halin yanzu ba wani wakili a majalisar wakilai ta tarraya da ya kama kafarsa. Da farko dai a halin yanzu shi ne wakili daya tilo a fadin majalisar wakilan tarayyar Najeriyya da ya  zarta sauran dadewa a cikin wannan majalisa, domin ahalin yanzu cikin zango na biyar yake  a matsayin wakilin al’umma Doguwa/T/Wada daga Jihar Kano.

Wannan ya tabbatar da irin amincewar da al’ummarsa suka yi masa sakamakon irin tagomashin da yake kaiwa yankin da yake wakilta Haka zalika shi ne dan majalisar da ya ciri tutar cewa matukar yana cikin kasarnan Najeirya, ya wajabtawa kansa duk makon duniya sai ya koma mazabunsa domin ganawa da al’ummarsa. Sannan kuma idan ana batun samar da ayyukan ci gaba, wannan kuma sai dai ayi addu’a a tashi, domin shi ne wakili da kusan bawai karamar Hukuma, Mazaba ko garin dagaci ba, duk wani akwatu da ake kadauri’a akansa Alhassan Ado Doguwa ya kai masa aikin raya kasa. Karamar Hukumar T/wada na da Akwatu 240 ya yin Doguwa keda a kwatu 116, duk wadanan akwatuna sun rubuta da wani nau’I aikin ci gaba, kama daga rijiyar burtsatse mai amfani da hasken rana, asibiti, hanya, Makaranta da sauran abubuwa more rayuwa.

Ayyukan wakilin al’ummar Doguwa/T/wada sun zama kamar al’amara domin a cikin watanni uku na wannan shekarar Alhassan Ado Doguwa an tabbatar da cewa al’ummar da ya ke wakilta sunyi hafzi da rijiyoyin Burtsatse masu amfani da hasken rana sama da 54, ajujuwa, hanyoyi, asibitoci da kuma taimakon harkokin karatun dalibai ‘yan asalin wannan yanki. Yanzu haka abin da ba’a taba gani ba Alhassan Ado bisa la’akari da yankin da ya fito, yanki ne da ake gudanar da harkokin Noma ka’in da na’in, hakan tasa ya samar da Tirela 30 ta takin zamani wanda kyauta ake rabawa manoman wadannan Kananan Hukumomi biyu da yake wakilta. Haka kuma domin saukaka zirga-zirga daga nan zuwa can wakilin al’ummar ta Doguwa/ T/Wada ya samar da babur 1,000 daya lakadan wanda yanzu haka an gama shirye shiryen rabawa al’ummar da yake wakilta. Matan Karkara a kananan Hukumomin Doguwa/T/Wada su ne shaida domin aduk shekarar Allah ta’ala wakilin nasu na samar da injunan Malkade, Saka tare bayar da jarin bahunan fulawa domin ci gaba da gudanar sana’u iri daban daban. Batun injunan ban ruwa ga manoma kuwa an kai matsayin da a halin yanzu gidan kowa akwai, Haka lamarin ya ke ta fuskar tsaro duk wanda ya san yankin Doguwa/T/Wada yasan sunyi fama da matsalar sace-sacen shanu da garkuwa da mutane, amma yanzu al’amarin ya zama tarihi

domin Alhassan Ado Doguwa ya yi duk mai yiwu domin ganin an samar da wata rundunar soja da suke gudanar da atisaye a cikin dajin Falgore wanda hakan ya kawo karshen waccan matsala.

Idan da ace duk sauran wakilan da aka zaba haka suke gudanar da ayyukan da aka tura su wakilcin al’umma, ko shakka babu da jama’a basu ci gaba da kokawa a wasu lokuta ma wanda har jin wasu al’umma ake suna kokarin yin kiranye domin maido da nasu wakilin gida saboda rashin tsinana masu komai. Haka kuma da yawa al’ummar wasu kananan Hukumomin daga randa aka rantsar da wanda suka zaba shi kenan sai zabe ya zagayo sanann ake sake ganinsu sun kara lallabowa da kokon barar kuri’ar al’umma.

Amma dai al’ummar Doguwa/T/Wada sun nu nawa Duniya hallaci domin ba haka kawai al’umma za su ci gaba da zabar wakili har karo biyar ba tare da gamsuwa da wakilcin da ya ke masu ba, haka ma yanzu duk wanda ke wanann yankin ba’a kai masa maganar wani dan takara, domin dole sai ka fada masu abin da ka yi wanda ya shafe wanda Alhassan Ado ke yiwa al’ummar Doguwa/T/Wada har da kake bukatar su aje gwaninsu wanda suka gwada kuma suka tabbatar da nagartarsa. Daman dai kamar yadda bahaushe ke cewa bukatar maje Hajji Sallah, saboda Alhassan Ado ya zarta sa’a kuma ga dukkan alamu shi al’ummarsa suke da yakinin ci gaba da wakiltarsu.

 

Exit mobile version