Connect with us

RIGAR 'YANCI

Wakilcin Nura Nakowa Alheri Ne Ga Al’ummar Rano – Idi Gwangwan

Published

on

Shugaban jam’iyyar APC na karamar hukumar Rano, Alhaji Idi Gwangwan ya bayyana dan majalisarsu na jiha mai wakiltar yankin, Hon.Nura Alhasan Nakowa da cewa, wakili ne nagari dake sauke nauyin al’ummarsa.

Alhaji Idi Gwangwan ya ce, zaben da al’ummar Rano suka yi masa sunyi zabe na alheri kuma shine dan auta me karamin shekaru a majalisar jihar Kano. Amma yana da tunani da hangen nesa basu taba zaton zai zame musu mafi alkhairi a karamar hukumar ba. Domin bai wuce kwanaki 30 da zuwa majalisa ba yasa aka yi aikin ido na mutane 339 bayan ‘yan kwanaki da wannan ya raba Babura ya sake raba tallafin ya kira mata guda 283 kowacce ya bata turmin atamfa bayan aikace-aikace wadanda yake na Makarantu da Masallatai makarantun islamiyya irin abubuwa da ya yi ba abin da za su ce dashi sai dai Allah ya saka da alkhairi.
Ya ce, kamar yanda a baya suka zabi tsohon kakakin majalisar Kano. Right Hon Kabiru Alasan kwalliya ta biya sabulu yanzu ma ta biya suna godiya akai. Irin tarbiyya da dan majalisar Rano Hon. Nura Nakowa ya samu daga manyansa yana kula da shawarar manya saboda haka duk abinda ya yi ba mamaki suna godiya da fatan Allah ya saka masa da alkhairi.
Idi Gwangwan ya ce, su a Rano ko gobe aka ce a sake fitowa sunanan yanda suka zabi tsohon Kakakin majalisar Kano sau biyu shekara Takwas sannan ya tafi majalisar tarayya shima sunanan za su bashi goyon baya da yardar Allah.
Alhaji Idi Gwangwan ya ce, dan majalisar nasu ya gudanar da kudurce-kudurce a majalisa ba abinda yafi damun al’ummar Rano samar da ruwansha Hon. Nura Nakowa yakai kuduri Gwamna ya sawo manyan injuna guda uku sunanan an kaisu Tiga. Ya kuma sake kai yanda za’a ga an hada injunan sukai ruwa daga Tiga zuwa Rano har Kibiya.
Ya ce, bayan haka akwai kudurin masarauta da Allah ya tabbatar da da sauran kudure-kudure na samar da taki dan habaka noma da kuduri na fadada Asibiti na Rano ana ta aikace-aikace ansa gadaje sama da 400 a ciki.
Idi Gwamgwan ya gode wa al’ummar Rano da kuma kira a dada taya Gwamna da addu’a suna kuma fata wannan masarauta Allah ya daukaketa ya jikan Sarkin Rano da sauran sarakai ya kawo daukaka da cigaba al’ummar Rano da jihar Kano.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: