Daga CRI Hausa
Wakilin kasar Belarus ya gabatar da jawabi jiya Juma’a a madadin kasashe 70 a yayin taro karo na 46 na hukumar kare hakkin Bil Adama ta MDD, inda ya nanata cewa, harkokin yankin HK, harkoki ne na cikin gidan kasar Sin da bai kamata wasu su tsoma baki ciki ba.
Jawabin ya kuma bayyana cewa, kaucewa tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasashe masu cikakken ikon mulkin kai, ka’ida ce cikin tsarin mulkin MDD da huldar kasa da kasa. Ya kuma bayyana goyon bayan kasashen ga manufar “kasa daya mai tsarin mulki biyu” da Sin ke aiwatar a yankin Hongkong. A ganin kasashen, bayan zartas da dokar tsaron kasa ta Hongkong da kasar Sin ta yi, an kawar da rikice-rikice da tabbatar da kwanciyar hankali a yankin. Kuma Hong Kong wani yanki ne da ba za a iya rabawa da kasar Sin ba. Haka kuma harkokin da suka shafi yankin, batutuwa ne na cikin gidan kasar Sin. Jawabin ya kuma kalubalanci bangarori daban-daban da su mutunta ikon mulkin kasar Sin da kauracewa shisshigi cikin harkokin HongKong da sauran harkokin cikin gidan kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)